Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Covenants: Presents given as tokens
Ayoyi game da Presents given as tokens
Sai Ibrahim ya kawo tumaki da shanu ya ba wa Abimelek, sai su biyun suka yi yarjejjeniya.
Ibrahim ya ware ’yan raguna bakwai daga cikin garke,
sai Abimelek ya ce wa Ibrahim, “Mene ne ma’anar ’yan raguna bakwai da ka keɓe?”
Ibrahim ya amsa ya ce, “Ka karɓi waɗannan ’yan tumaki bakwai daga hannuna a matsayin shaida cewa ni ne na haƙa wannan rijiya.”