Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Birds

71 ayoyi · 107 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. jimina, ƙururu, bubuƙuwa, kowane irin shaho,

  2. da mujiya, da babbar mujiya, ɗuskwi,

  3. kwasakwasa, ungulu, da babba da jaka,

  4. zalɓe, kowane irin jinjimi, katutu, da kuma jamage.

  5. Dukan ’yan ƙwari masu fikafikai masu rarrafe, haram ne a gare ku, kada ku ci su.

  6. Amma duk wata halitta mai fikafikai mai tsabta ce, za ku iya ci.

  7. In kuka ga gidan tsuntsu kusa da hanya, ko a kan itace, ko kuma a ƙasa, mahaifiyar tsuntsun kuwa tana kwance a kan ’ya’yanta, ko kuwa a kan ƙwanta, kada ku kama mahaifiyar duk da ’ya’yan.

  8. Za ku iya kwashe ’ya’yan, amma ku tabbata kun bar mahaifiyar tă tafi. Yin haka zai sa ku sami zaman lafiya da tsawon rai.

  9. “Fikafikan jimina suna bugawa cike da farin ciki amma ba za su gwada kansu da fikafikan da na shamuwa ba.

  10. Tana sa ƙwai nata a ƙasa kuma ta bar su su yi ɗumi a cikin ƙasa,

  11. ba tă damu ko za a taka su a fasa su, ko waɗansu manyan dabbobi za su tattake su.

  12. Tana tsananta wa ’ya’yanta kamar ba nata ba ba tă damu da wahalar da ta sha ba.

  13. Gama Allah bai ba ta hikima ba ko kuma iya fahimta.

  14. Duk da haka sa’ad da ta buɗe fikafikanta ta shara da gudu tana yi wa doki da mai hawansa dariya.

  15. “Ko ta wurin hikimarka ce shirwa take firiya take kuma baza fikafikanta zuwa kudu?

  16. Ko da umarninka ne shaho yake firiya ya kuma yi sheƙarsa a can sama?

  17. Yana zama a kan dutse yă zauna a wurin da dare; cikin duwatsu ne wurin zamansa.

  18. Daga can yake neman abincinsa; idanunsa suna gani daga nesa.

  19. ’Ya’yansa suna shan jini, inda akwai waɗanda aka kashe nan za a same shi.”

  20. Ka yi shi ƙasa kaɗan da Allah ka yi masa rawani da ɗaukaka da girma.

  21. Ka mai da shi mai mulki bisa ayyukan hannuwanka; ka sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa,

  22. dukan shanu da tumaki, da kuma namun jeji,

  23. tsuntsayen sararin sama da kifin teku, da dukan abin da yake yawo a ƙarƙashin ruwan teku.

  24. Yabi Ubangiji, ya raina. Ya Ubangiji Allahna, kana da girma ƙwarai; kana saye da daraja da ɗaukaka.

  25. Ubangiji ya naɗe kansa da haske kamar riga ya shimfiɗa sammai kamar tenti