Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Birds: What species were unclean

16 ayoyi · 107 fannoni

Ayoyi game da What species were unclean

  1. “ ‘Waɗannan su ne tsuntsayen da za ku yi ƙyamarsu, ba za ku ci su ba domin sun zama abin ƙyama. Tsuntsayen kuwa su ne, gaggafa, ungulu, baƙin ungulu,

  2. shirwa, da duk wani irin baƙin shirwa,

  3. kowane irin hankaka,

  4. mujiya mai ƙaho, jimina, shaho, da kowane irin shaho,

  5. ƙaramin ƙururu, babba da jaka, zalɓe,

  6. kazar ruwa, kwasakwasa, da ungulu,

  7. shamuwa, kowane irin jinjimi, katutu da kuma jamage.

  8. “ ‘Dukan ƙwarin da suke da fikafikai masu tafiya da ƙafafu huɗu abin ƙyama ne gare ku.

  9. Amma waɗannan ba za ku ci ba, gaggafa, ungulu, ungulun kwakwa,

  10. duki, buga zaɓi, kowace irin shirwa,

  11. kowane irin hankaka,

  12. jimina, ƙururu, bubuƙuwa, kowane irin shaho,

  13. da mujiya, da babbar mujiya, ɗuskwi,

  14. kwasakwasa, ungulu, da babba da jaka,

  15. zalɓe, kowane irin jinjimi, katutu, da kuma jamage.

  16. Dukan ’yan ƙwari masu fikafikai masu rarrafe, haram ne a gare ku, kada ku ci su.