Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Ancient Samaria

87 ayoyi · 29 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Haka kuwa ya kasance kamar yadda mutumin Allah ya ce wa sarki, “Gobe war haka, za a sayar da mudun gari shekel guda, mudun sha’ir biyu ma a shekel guda, a ƙofar Samariya.”

  2. Hafsan ya riga ya ce wa mutumin Allah, “Kai, ko da Ubangiji zai buɗe tagogin sama, wannan abu ba zai yiwu ba!” Mutumin Allah kuwa ya faɗa masa, “Za ka gani da idanunka sai dai ba za ka ci ba!”

  3. Haka kuwa ya kasance, gama mutane sun tattake shi a hanyar shiga, har ya mutu.

  4. “Da zarar wasiƙan nan ta sadu da ku, da yake ’ya’yan maigidanku suna tare da ku, kuna kuma da kekunan yaƙi da dawakai, da birni mai katanga da makamai,

  5. Yowash ya huta da kakanninsa, Yerobowam kuwa ya gāje shi. Aka binne Yehowash a Samariya tare da sarakunan Isra’ila.

  6. Sarkin Assuriya ya kai wa ƙasar Hosheya gaba ɗaya farmaki, ya kewaye Samariya na tsawon shekara uku.

  7. A shekara ta tara ta sarautar Hosheya, sarkin Assuriya ya ci Samariya da yaƙi ya kuma kwashe Isra’ilawa zuwa Assuriya. Ya tsugunar da su a Hala, da a Gozan a bakin Kogin Habor da kuma a garuruwan Medes.

  8. har Ubangiji ya kawar da su daga gabansa, kamar yadda ya gargaɗe su ta bakin bayinsa annabawa. Saboda haka aka kwashi mutanen Isra’ila daga ƙasarsu zuwa bauta a Assuriya, har wa yau kuwa suna can.

  9. Sarkin Assuriya ya kawo mutane daga Babilon, Kuta, Afa, Hamat da Sefarfayim ya zaunar da su a garuruwan Samariya don su maya gurbin Isra’ilawa. Suka mallaki Samariya suka kuma zauna a garuruwansu.

  10. Sa’ad da suka fara zama a can, ba su bauta wa Ubangiji ba; saboda haka ya aika da zakoki a tsakaninsu suka karkashe waɗansu mutane.

  11. A shekara ta huɗu ta Hezekiya, wato, shekara ta bakwai ke nan ta mulkin Hosheya ɗan Ela sarkin Isra’ila; Shalmaneser Sarkin Assuriya ya tasam ma Samariya da yaƙi; ya kewaye ta.

  12. A ƙarshen shekara ta uku, Assuriyawa suka ci Samariya da yaƙi. An ci Samariya da yaƙi a shekara ta shida ta mulki Hezekiya, wanda ya zo daidai da shekara ta tara ta mulkin Hosheya sarkin Isra’ila.

  13. Sarkin Assuriya ya kwashe Isra’ila zuwa Assuriya ya zaunar da su a Hala, da Gozan a kogin Habor da kuma garuruwan Medes.

  14. Kan Efraim shi ne Samariya, kan Samariya kuma kawai shi ne ɗan Remaliya. In ba ku tsaya da ƙarfi cikin bangaskiyarku ba, ba za ku dawwama ba.’ ”

  15. Kafin yaron yă san yadda zai ce ‘Babana’ ko ‘Mamana,’ sarkin Assuriya zai kwashe arzikin Damaskus da ganimar Samariya.”

  16. Dukan mutane za su san shi, Efraim da mazaunan Samariya, waɗanda suke magana da fariya suna kuma ɗaga kai,

  17. Amma Ubangiji ya ƙarfafa maƙiyan Rezin gāba da su ya kuma ingiza abokan gāba.

  18. Arameyawa daga gabas da Filistiyawa daga yamma sun cinye Isra’ila da buɗaɗɗen baki. Duk da haka, fushinsa bai huce ba, hannunsa har yanzu yana a miƙe.

  19. Kaito ga wannan rawani, girman kai na mashayan Efraim, ga fure mai yanƙwanewa, darajar kyansa, da aka sa a kan kwari mai ba da amfani, ga birnin nan, wadda take girman kan waɗanda aka ƙasƙantar da ruwan inabinsu!

  20. Za ki sāke dasa gonakin inabi a kan tussan Samariya; manoma za su yi shuka a kansu su kuma ji daɗin amfaninsu.

  21. Babbar ’yar’uwarki mutuniyar Samariya ce, wadda take zaune da ’ya’yanta mata wajen arewa da ke; ƙanuwarki ita ce Sodom wadda take zaune kudu da ke tare da ’ya’yanta mata.

  22. Ba ki bi hanyoyinsu da abubuwansu na banƙyama kaɗai ba, sai ka ce wannan ya yi miki kaɗan, amma kin lalace fiye da su.

  23. Samariya ba tă aikata ko rabin zunubanki ba. Kin aikata abubuwa masu banƙyama fiye da su, suka kuma sa ’yan’uwanki mata suka zama kamar masu adalci ta wurin dukan waɗannan abubuwa da kika aikata.

  24. “Ohola ta shiga karuwanci yayinda take zamana; ta kuwa yi ta kai da kawowa da kwartayenta, Assuriyawa, mayaƙa

  25. a duka sa’ad da zan warkar da Isra’ila, zunuban Efraim za su tonu za a kuma bayyana laifofin Samariya. Suna ruɗu, ɓarayi sukan fasa su shiga gidaje, ’yan fashi sukan yi fashi a tituna;