Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Ancient Samaria: The residence of the kings of Israel
Ayoyi game da The residence of the kings of Israel
A shekara ta talatin da takwas ta Asa sarkin Yahuda, Ahab ɗan Omri ya zama sarkin Isra’ila, ya kuma yi mulki a Samariya a kan Isra’ila, shekara ashirin da biyu.
Ahaziya fa ya fāɗo daga tagar ɗakin samansa a Samariya ya ji rauni. Saboda haka ya aiki masinjoji, yana cewa, “Ku je ku tuntuɓi Ba’al-Zebub, allahn Ekron, ku ga ko zan warke daga wannan rauni.”
Yoram, ɗan Ahab ya zama sarki Isra’ila, a Samariya, a shekara ta goma sha takwas ta mulkin Yehoshafat, sarkin Yahuda, ya kuma yi mulki shekara goma sha biyu.
To, a lokacin, Sarki Yoram ya tashi daga Samariya, ya tattara sojoji daga dukan Isra’ila.