Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Aliens: To be treated with justice

13 ayoyi · 13 fannoni

Ayoyi game da To be treated with justice

  1. “Kada a wulaƙanta, ko a zalunci baƙo, domin dā ku baƙi ne a ƙasar Masar.

  2. “Kada ka zalunci baƙo, ku kanku kun san halin baƙunci, gama dā ku baƙi ne a Masar.

  3. “ ‘Sa’ad da baƙo yana zama tare da ku a ƙasarku, kada ku wulaƙanta shi.

  4. Dole ku ɗauki baƙon da yake zama tare da ku kamar haifaffe ɗan ƙasa. Ku ƙaunace shi kamar kanku, gama dā ku ma baƙi ne a Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.

  5. Na kuma umarci alƙalanku a wancan lokaci, na ce, “Ku yi adalci cikin shari’a tsakanin ’yan’uwanku, ko damuwar tana tsakanin ’yan’uwa Isra’ilawa ne, ko kuwa tsakanin Isra’ilawa da baƙin da suke zaune a cikinku.

  6. Sai ku ƙaunaci baƙi, gama dā ku ma baƙi ne a ƙasar Masar.

  7. Kada ku zalunci ɗan ƙodago matalauci da mabukaci, ko da shi ɗan’uwanku ne mutumin Isra’ila, ko baƙon da yake zama a cikin garuruwanku.

  8. Ba za ku danne hakkin baƙon da yake zama a cikinku ko na marayu ba, ba za ku ɗauki rigar matar da mijinta ya mutu a matsayin jingina ba.

  9. “La’ananne ne mutumin da ya yi rashin adalci ga baƙo, maraya ko gwauruwa.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”

  10. in ba ku zalunci baƙo, maraya ko gwauruwa ba kuma in ba ku zub da jinin marar laifi a wannan wuri ba, in kuma ba ku bi waɗansu alloli da za su cuce ku ba,

  11. Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka yi abin da yake gaskiya da kuma daidai. Ka kuɓutar da wannan da aka yi masa ƙwace daga hannun mai zaluntarsa. Kada ka yi abin da ba daidai ba ko ka cuci baƙo, maraya ko gwauruwa, kuma kada ka zub da jini marar laifi a wannan wuri.

  12. Mutanen ƙasar na yin ƙwace suna yin fashi; suna cin zalin matalauta da mabukata suna wulaƙanta baƙo suna hana musu adalci.

  13. “Ta haka zan zo kusa da ku don in yi hukunci. Zan hanzarta ba da shaida a kan masu yin sihiri, da mazinata da masu shaidar zur. Zan ba da shaida a kan waɗanda suke zaluntar ma’aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye da marayu, suna kuma hana baƙi samun adalci, ba sa ma tsorona,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.