Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Aliens: Religious privileges of

5 ayoyi · 13 fannoni

Ayoyi game da Religious privileges of

  1. “Baƙon da yake zama tare da ku da yake so yă yi Bikin Ƙetarewar Ubangiji, dole yă yi wa dukan mazan da suke cikin gidansa kaciya; sa’an nan ne zai iya yin abubuwa kamar haifaffen ɗan ƙasa.

  2. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ta shafi ɗan ƙasa da kuma baƙon da yake zama a tsakaninku.”

  3. “ ‘Baƙon da yake zaune a cikinku wanda yake so yă yi Bikin Ƙetarewar Ubangiji, dole yă yi shi bisa ga dokokinsa da ƙa’idodinsa. Dole ku kasance da ƙa’ida ɗaya ga baƙo da kuma ɗan ƙasa.’ ”

  4. Idan baƙon da yake baƙunci a cikinku, ko kowane ne da yake tare da ku a dukan zamananku, yana so yă ba da hadayar da akan yi da wuta don a yi ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji, dole yă yi kamar yadda kuke yi.

  5. Ƙa’ida ɗaya ce ga jama’a da kuma baƙin da suke zama a cikinku, wannan za tă zama dawwammamiyar farilla a dukan tsararraki masu zuwa. Da ku, da baƙi, za ku zama ɗaya a gaban Ubangiji.