Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Aaron

145 ayoyi · 27 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,

  2. Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,

  3. Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,

  4. Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,

  5. Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Haruna, shafaffun firistocin da aka naɗa domin su yi aiki firist.

  6. Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,

  7. Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,

  8. “Gaya wa Haruna da ’ya’yansa, ‘Ga yadda za ku albarkaci Isra’ilawa. Za ku ce musu,

  9. Miriyam da Haruna suka fara zargin Musa saboda matarsa ’yar ƙasar Kush da ya aura.

  10. sai Haruna ya ce wa Musa, “Ranka yă daɗe, ina roƙonka kada ka hukunta mu, gama zunubin da muka yi, mun yi ne cikin wauta.

  11. Kada ka sa ta zama kamar haifaffen mataccen jariri daga cikin mahaifiya wanda rabin jikin ruɓaɓɓe ne.”

  12. Dukan Isra’ilawa suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna, dukan taron kuwa suka ce musu, “Da ma mun mutu a Masar! Ko kuma a wannan hamada ma!

  13. Don me Ubangiji yana kawo mu wannan ƙasa yă bar mu kawai mu mutu da takobi? A kuma kwashe matanmu da ’ya’yanmu ganima. Ashe, bai fi mana mu koma Masar ba?”

  14. Sai suka ce wa junansu, “Mu naɗa wa kanmu shugaba, mu koma Masar.”

  15. Sai Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki a gaban jama’ar Isra’ilawa da suka taru a can.

  16. Amma taron jama’a suka ce za su jajjefe su da duwatsu. Sai ɗaukakar Ubangiji ta bayyana a Tentin Sujada ga dukan Isra’ilawa.

  17. tare kuwa suka zo wurin Musa da Haruna, suka ce musu, “Kun wuce gona da iri! Dukan jama’an nan masu tsarki ne, kowannensu, Ubangiji kuma yana tare da su. Me ya sa kuke ɗaukan kanku fiye da taron jama’ar Ubangiji?”

  18. Da Musa ya ji haka, sai ya fāɗi rubda ciki ya yi addu’a

  19. Sai ya ce wa Kora da dukan waɗannan da suke tare shi, “Da safe, Ubangiji zai nuna wane ne yake nasa, da kuma wane ne yake da tsarki. Zai kuma sa mutumin yă zo kusa da shi. Mutumin da ya zaɓa kuwa zai sa yă zo kusa da shi.

  20. Kai Kora da ƙungiyarka, gobe, za ku ɗauki farantai,

  21. ku zuba wuta a ciki, ku kuma zuba musu turaren wuta a gaban Ubangiji. Sa’an nan wanda Ubangiji ya zaɓa a tsakaninmu sh ne mai tsarki. Ku Lawiyawa ku ne kuka wuce gona da iri!”

  22. Musa ya kuma ce wa Kora, “Yanzu ku saurara, ku Lawiyawa!

  23. Ashe, bai ishe ku ba, cewa Allah na Isra’ila, ya keɓe ku daga sauran jama’ar Isra’ilawa, ya kuma kawo ku kusa da shi don ku yi aiki a tabanakul na Ubangiji, ku kuma tsaya a gaba jama’a don ku yi musu aiki?

  24. Ya kawo ku da kuma dukan ’yan’uwanku Lawiyawa kusa da shi, amma yanzu kuna ƙoƙari ku karɓi aikin firist.

  25. Kai da ƙungiyarka kun haɗa kai kuna yi wa Haruna gunaguni, amma wane ne Haruna? A zahiri tawaye ne kuke wa Ubangiji.”