- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1446–1406 BC
The Wilderness Years
Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Maimaitawar Shari’a 27:20kusan 1451 K.H.
“La’ananne ne mutumin da ya kwana da matar mahaifinsa, gama ya ƙasƙantar da gadon mahaifinsa ke nan.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
- Maimaitawar Shari’a 27:21kusan 1451 K.H.
“La’ananne ne mutumin da ya yi jima’i da dabba.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
- Maimaitawar Shari’a 27:22kusan 1451 K.H.
“La’ananne ne mutumin da ya kwana da ’yar’uwarsa, ’yar mahaifinsa ko ’yar mahaifiyarsa.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
- Maimaitawar Shari’a 27:23kusan 1451 K.H.
“La’ananne ne mutumin da ya kwana da mahaifiyar matarsa.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
- Maimaitawar Shari’a 27:24kusan 1451 K.H.
“La’ananne ne mutumin da ya kashe maƙwabcinsa a ɓoye.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
- Maimaitawar Shari’a 27:25kusan 1451 K.H.
“La’ananne ne mutumin da ya karɓi cin hanci don yă kashe marar laifi.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
- Maimaitawar Shari’a 27:26kusan 1451 K.H.
“La’ananne ne mutumin da bai yi na’am da kalmomin wannan doka ta wurin aikata su ba.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
- Maimaitawar Shari’a 28:1kusan 1451 K.H.
In kun yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, kuka kuma lura, kuka bi dukan umarnan da na ba ku a yau, Ubangiji Allahnku zai sa ku bisa dukan al’ummai a duniya.
- Maimaitawar Shari’a 28:2kusan 1451 K.H.
Dukan waɗannan albarku za su sauko muku, su zama naku, in kuka yi biyayya ga Ubangiji Allahnku.
- Maimaitawar Shari’a 28:3kusan 1451 K.H.
Za ku zama masu albarka a cikin birni, za ku kuma zama masu albarka har a ƙauye.
- Maimaitawar Shari’a 28:4kusan 1451 K.H.
’Ya’yanku za su zama masu albarka, haka ma hatsin gonakinku da kuma ’ya’yan dabbobinku, wato, ’ya’yan shanu da ’yan tumakinku.
- Maimaitawar Shari’a 28:5kusan 1451 K.H.
Za a albarkaci kwandonku da kwanon kwaɓan kullunku.
- Maimaitawar Shari’a 28:6kusan 1451 K.H.
Za ku zama masu albarka sa’ad da kuka shiga, za ku kuma zama masu albarka sa’ad da kuka fita.
- Maimaitawar Shari’a 28:7kusan 1451 K.H.
A gabanku, Ubangiji zai sa ku fatattaki abokan gāban da za su taso suna gāba da ku. Ta hanya guda za su auka muku, amma ta hanyoyi bakwai za su gudu daga gabanku.
- Maimaitawar Shari’a 28:8kusan 1451 K.H.
Ubangiji zai aika da albarka a rumbunanku da kuma a bisa kome da kuka sa hannunku a kai. Ubangiji Allahnku zai albarkace ku a ƙasar da yake ba ku.
- Maimaitawar Shari’a 28:9kusan 1451 K.H.
Ubangiji zai kafa ku kamar mutanensa masu tsarki, kamar yadda ya yi alkawari da rantsuwa, in kun kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, kuka kuma yi tafiya a hanyoyinsa.
- Maimaitawar Shari’a 28:10kusan 1451 K.H.
Sa’an nan dukan mutane a duniya za su ga cewa ana kiranku da sunan Ubangiji, za su kuwa ji tsoronku.
- Maimaitawar Shari’a 28:11kusan 1451 K.H.
Ubangiji zai azurta ku sosai, a ’ya’yan cikinku, a ’ya’yan dabbobinku da kuma a hatsin gonarku, a cikin ƙasar da ya rantse wa kakanninku zai ba ku.
- Maimaitawar Shari’a 28:12kusan 1451 K.H.
Ubangiji zai buɗe sammai, wurin ajiyarsa mai yalwa, don yă aika da ruwan sama a gonarku a lokacinsa, yă kuma albarkaci dukan aikin hannuwanku. Za ku ba wa al’ummai masu yawa rance, amma ba za ku karɓa bashi daga wurin wani ba.
- Maimaitawar Shari’a 28:13kusan 1451 K.H.
Ubangiji zai sa ku zama kai, ba wutsiya ba. In kun mai da hankali ga umarnan Ubangiji Allahnku da nake ba ku a wannan rana, kuka kuma lura, kuka bi su, kullum za ku kasance a bisa, ba a ƙasa ba.
- Maimaitawar Shari’a 28:14kusan 1451 K.H.
Kada ku kauce zuwa dama ko zuwa hagu daga umarnan da na ba ku a yau, har ku bi waɗansu alloli kuna yin musu sujada.
- Maimaitawar Shari’a 28:15kusan 1451 K.H.
Amma fa, in ba ku yi biyayya ga Ubangiji Allahnku ba, ba ku kuma lura kun bi dukan umarnansa da ƙa’idodin da nake ba ku a yau ba, dukan la’anan nan za su zo a bisanku, su kuma same ku.
- Maimaitawar Shari’a 28:16kusan 1451 K.H.
Za ku zama la’anannu a birni da kuma a ƙauye.
- Maimaitawar Shari’a 28:17kusan 1451 K.H.
Za a la’anta kwandonku da kwanon kwaɓan kullunku.
- Maimaitawar Shari’a 28:18kusan 1451 K.H.
Za a la’anta ’ya’yan cikinku, haka ma hatsin gonarku, da ’ya’yan shanunku da ’yan tumakinku.