- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1446–1406 BC
The Wilderness Years
Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Maimaitawar Shari’a 28:44kusan 1451 K.H.
Za su ba ku bashi, amma ba za ku ba su bashi ba. Za su zama kai, ku kuwa za ku zama wutsiya.
- Maimaitawar Shari’a 28:45kusan 1451 K.H.
Dukan waɗannan la’anoni za su sauko a kanku. Za su bi ku, su same ku, sai an hallaka ku, domin ba ku yi biyayya ga Ubangiji Allahnku, kuka kuma kiyaye umarnai da ƙa’idodin da ya ba ku ba.
- Maimaitawar Shari’a 28:46kusan 1451 K.H.
Za su zama alamu da al’ajabi gare ku da kuma zuriyarku har abada.
- Maimaitawar Shari’a 28:47kusan 1451 K.H.
Gama ba ku bauta wa Ubangiji Allahnku da farin ciki da kuma murna a lokacin wadata ba,
- Maimaitawar Shari’a 28:48kusan 1451 K.H.
saboda haka a cikin yunwa da ƙishirwa, cikin tsiraici da mugun talauci, za ku bauta wa abokan gāban da Ubangiji ya aiko muku. Zai sa karkiyar ƙarfe a wuyanku har sai ya hallaka ku ƙaf.
- Maimaitawar Shari’a 28:49kusan 1451 K.H.
Ubangiji zai kawo al’umma daga nesa, daga iyakar duniya, ta sauko a kanku kamar gaggafa, al’ummar da ba ku san yarenta ba,
- Maimaitawar Shari’a 28:50kusan 1451 K.H.
al’umma mai zafin hali wadda ba ta ba wa tsofaffi girma, kuma ba ta tausayin yara.
- Maimaitawar Shari’a 28:51kusan 1451 K.H.
Za su cinye ’ya’yan dabbobinku da hatsin gonarku sai an hallaka ku. Ba za su rage ko ƙwayar hatsi, ko sabon ruwan inabi, ko mai ba, ba kuwa za a bar ’yan tumakinku ba, sai an lalatar da ku.
- Maimaitawar Shari’a 28:52kusan 1451 K.H.
Za su kuwa kewaye ku a dukan garuruwanku, har sai katangarku masu tsayi wadda kuke dogara gare su, sun fāɗi ko’ina a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku.
- Maimaitawar Shari’a 28:53kusan 1451 K.H.
Saboda wahalar da abokan gābanku za su gasa muku a lokacin kwanto, za ku ci ’ya’yan cikinku, naman ’ya’yanku maza da mata waɗanda Ubangiji Allahnku ya ba ku.
- Maimaitawar Shari’a 28:54kusan 1451 K.H.
Kai, har da mutumin da ya fi hankali da kuma kirki a cikinku, ba zai ji tausayi ɗan’uwansa, ko matar da yake ƙauna, ko ’ya’yansa da suka ragu ba,
- Maimaitawar Shari’a 28:55kusan 1451 K.H.
ba kuwa zai ba waninsu wani naman ’ya’yansa da yake ci ba. Gama dukan abin da ya rage masa ke nan saboda wahalar da abokan gābanku za su gasa muku a lokacin da ake kwanton wa dukan biranenku.
- Maimaitawar Shari’a 28:56kusan 1451 K.H.
Mace mafi hankali da kuma kirki a cikinku, kai, mafi hankali da kirki da ba ta ma karambanin taɓa ƙasa da tafin ƙafarta, za tă hana wa mijinta da take ƙauna, da kuma ɗanta, ko ’yarta abinci.
- Maimaitawar Shari’a 28:57kusan 1451 K.H.
A ɓoye za tă ci mahaifar da take biyo bayan ta haihu, da ’ya’yan da za tă haifa, saboda ba ta da wani abinci lokacin da abokan gābanku za su kewaye garuruwanku da yaƙi mai tsanani.
- Maimaitawar Shari’a 28:58kusan 1451 K.H.
In ba ku lura kuka bi dukan kalmomi wannan doka, waɗanda an rubuta a wannan littafi ba, ba ku kuma girmama wannan suna mai ɗaukaka da kuma mai banrazana na Ubangiji Allahnku ba,
- Maimaitawar Shari’a 28:59kusan 1451 K.H.
Ubangiji zai aika da annoba masu zafi a kanku da zuriyarku, masifu masu zafi waɗanda za su daɗe, da mugayen cututtuka waɗanda ba sa kawuwa.
- Maimaitawar Shari’a 28:60kusan 1451 K.H.
Zai kawo muku dukan cututtukan Masar da kuke tsoro, za su kuwa manne muku.
- Maimaitawar Shari’a 28:61kusan 1451 K.H.
Ubangiji kuma zai kawo muku kowane irin ciwo da masifar da ba a rubuta a cikin wannan Littafin Doka ba, har sai an hallaka ku.
- Maimaitawar Shari’a 28:62kusan 1451 K.H.
Ku da kuke da yawa kamar taurari a sarari za ku ragu ku zama kaɗan, domin ba ku yi biyayya ga Ubangiji Allahnku ba.
- Maimaitawar Shari’a 28:63kusan 1451 K.H.
Kamar yadda ya gamshi Ubangiji ya sa kuka yi arziki kuka kuma ƙaru, haka zai gamshe shi yă lalatar yă kuma hallaka ku. Za a tumɓuke ku daga ƙasar da kuke shiga ku mallaka.
- Maimaitawar Shari’a 28:64kusan 1451 K.H.
Sa’an nan Ubangiji zai watsar da ku cikin dukan al’ummai, daga wannan bangon duniya zuwa wancan. A can za ku bauta waɗansu alloli, allolin itace da na dutse, waɗanda ko ku, ko kakanninku, ba ku sani ba.
- Maimaitawar Shari’a 28:65kusan 1451 K.H.
A cikin waɗancan al’ummai ba za ku sami hutu ba, ba wurin hutu wa tafin ƙafanku. A can Ubangiji zai sa fargaba a zuciyarku, yă sa idanunku su lalace, ranku zai yi suwu.
- Maimaitawar Shari’a 28:66kusan 1451 K.H.
Za ku yi zama cikin damuwa kullum, cike da tsoro, dare da rana, ba tabbacin abin da zai faru da ranku.
- Maimaitawar Shari’a 28:67kusan 1451 K.H.
Da safe za ku ce, “Da ma yamma ne!” Da yamma kuma ku ce, “Da ma safiya ce!” Saboda tsoron da ya cika zukatanku da kuma abubuwan da idanunku za su gani.
- Maimaitawar Shari’a 28:68kusan 1451 K.H.
Ubangiji zai komar da ku cikin jiragen ruwa zuwa Masar, tafiyar da na ce kada ku ƙara yi. A can za ku ba da kanku don sayarwa ga abokan gābanku a matsayin bayi maza da mata, amma ba wanda zai saye ku.