Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446–1406 BC

The Wilderness Years

Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.

2,247 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Sai dattawan garinsa su kira shi, su kuma yi masa magana. In ya nace yana cewa, “Ba na so in aure ta,”

  2. sai gwauruwan nan, matar ɗan’uwansa tă haura wurinsa a gaban dattawa, tă tuɓe takalminsa guda, ta tofa masa miyau a fuska, tă ce, “Haka za a yi ga mutumin da zai ƙi kafa gidan ɗan’uwansa.”

  3. Za a kira zuriyarsa a Isra’ila Iyalin da aka tuɓe masa takalmi.

  4. In mutane biyu suna faɗa, sai matar mutum ɗaya daga cikinsu ta zo don tă kuɓutar da mijinta daga abokin faɗarsa, ta kuma miƙa hannu ta kama marainan wancan,

  5. sai ku yanke hannunta. Kada ku ji tausayinta.

  6. Kada ku kasance da ma’auni iri biyu a jakarku, ɗaya babba, ɗaya ƙarami.

  7. Kada ku kasance da mudu iri biyu a jakarku, ɗaya babba, ɗaya ƙarami.

  8. Dole ku kasance da ma’aunin da kuma mudun da yake daidai, kuma na gaskiya, saboda ku yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku.

  9. Gama Ubangiji Allahnku yana ƙyamar duk mai yi waɗannan abubuwa, da kuma mai rashin gaskiya.

  10. Ku tuna da abin da Amalekawa suka yi muku a hanya, sa’ad da kuka fito Masar.

  11. Yadda suka yi muku kwanto a hanya, suka fāɗa muku ta baya, suka karkashe waɗanda suka gaji tiɓis. Ba su ko ji tsoron Allah ba.

  12. Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya ba ku hutu daga dukan abokan gābanku kewaye da ku, a ƙasar da yake ba ku ku mallaka a matsayin gādo, sai ku shafe Amalekawa daga duniya, don kada a ƙara tunawa da su. Kada fa ku manta!

  13. Sa’ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo, kuka mallake ta, kuka kuma zauna a cikinta,

  14. sai ku ɗauki ’ya’yan fari na dukan amfanin gonar ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, ku zuba a kwando. Sa’an nan ku je wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa yă zama mazauni don Sunansa,

  15. ku faɗa wa firist da yake aiki a lokacin, “Na sakankance yau ga Ubangiji Allahnka, cewa na zo ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba wa kakanninmu.”

  16. Firist ɗin zai karɓi kwandon daga hannuwanku yă sa shi a ƙasa a gaban bagaden Ubangiji Allahnku.

  17. Sa’an nan za ku furta a gaban Ubangiji Allahnku cewa, “Mahaifina mutumin Aram ne mai yawo, ya gangara zuwa Masar da mutane kaɗan, ya zauna a can, ya kuma zama babban al’umma, mai iko da kuma mai yawa.

  18. Amma Masarawa suka wulaƙanta mu suka sa muka sha wahala, suna sa mu aikin dole.

  19. Sai muka yi kuka ga Ubangiji Allahn kakanninmu, Ubangiji kuwa ya ji kukanmu, ya kuma azabar da muke sha, da wahalar da muke sha, da danniyar da suke yin mana.

  20. Sai Ubangiji ya fitar da mu daga Masar da hannu mai ƙarfi da kuma iko, da razana mai girma da kuma alamu banmamaki da al’ajabai.

  21. Ya kawo mu wannan wuri, ya kuma ba mu wannan ƙasa, ƙasa mai zub da madara da kuma zuma;

  22. yanzu kuwa na kawo ’ya’yan fari na gonar da kai, ya Ubangiji ka ba ni.” Sai ku sa kwandon a gaban Ubangiji Allahnku, sa’an nan ku rusuna a gabansa.

  23. Ku da Lawiyawa da baƙin da suke a cikinku, za ku yi murna cikin dukan abubuwa masu kyau da Ubangiji Allahnku ya ba ku tare da gidanku.

  24. Sa’ad da kuka gama fitar da kashi ɗaya bisa goma na dukan amfanin gona a shekara ta uku, shekarar zakka, za ku ba da su ga Balawe, baƙo, maraya da kuma gwauruwa, don su ci a cikin garuruwanku su ƙoshi.

  25. Sa’an nan ku faɗa wa Ubangiji Allahnku, “Na cire tsattsarkan rabo daga gidana na kuma ba wa Balawe, baƙo, maraya da gwauruwa, bisa ga dukan abin da ka umarta. Ban ja gefe daga umarnanka ko in manta da wani a cikinsu ba.