Tsallake zuwa abun ciki

circa 800–400 BC

The Hebrew Prophets

God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.

3,706 ayoyi · 14 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ishaya 41:4kusan 712 K.H.

    Wane ne ya taɓa yin haka ya kuma sa ya faru, yana kira ga tsararraki daga farko? Ni, Ubangiji ina can tun farkonsu ni kuma ina can har ƙarshe, Ni ne shi.”

  2. Ishaya 41:5kusan 712 K.H.

    Tsibirai sun gan shi suka kuma ji tsoro; iyakokin duniya sun yi rawar jiki. Suka kusato suka kuma zo gaba;

  3. Ishaya 41:6kusan 712 K.H.

    kowa na taimakon wani yana ce wa ɗan’uwansa, “Ka ƙarfafa!”

  4. Ishaya 41:7kusan 712 K.H.

    Masassaƙi yakan ƙarfafa maƙerin zinariya, kuma shi mai gyara da guduma ya yi sumul yakan ƙarfafa mai harhaɗawa. Ya ce game da haɗin, “Ya yi kyau.” Yakan buga ƙusoshi su riƙe gunkin don kada yă fāɗi.

  5. Ishaya 41:8kusan 712 K.H.

    “Amma kai, ya Isra’ila, bawana, Yaƙub, wanda na zaɓa, zuriyar Ibrahim abokina,

  6. Ishaya 41:9kusan 712 K.H.

    na ɗauke ka daga iyakar duniya, daga kusurwoyi masu nesa na kira ka. Na ce, ‘Kai bawana ne’; na zaɓe ka ban kuwa ƙi ka ba.

  7. Ishaya 41:10kusan 712 K.H.

    Saboda haka kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai; kada ka karai, gama ni ne Allahnka. Zan ƙarfafa ka in kuma taimake ka; zan riƙe ka da hannun damana mai adalci.

  8. Ishaya 41:11kusan 712 K.H.

    “Duk wanda ya yi fushi da kai tabbatacce zai sha kunya da ƙasƙanci; waɗanda suka yi hamayya da kai za su zama kamar ba kome ba su kuma hallaka.

  9. Ishaya 41:12kusan 712 K.H.

    Ko ka nemi abokan gābanka, ba za ka same su ba. Waɗanda suke yaƙi da kai za su zama kamar ba kome ba.

  10. Ishaya 41:13kusan 712 K.H.

    Gama ni ne Ubangiji Allahnka, wanda ya riƙe ka da hannun damana ya kuma ce maka, Kada ka ji tsoro; zan taimake ka.

  11. Ishaya 41:14kusan 712 K.H.

    Kada ka ji tsoro, ya Yaƙub marar ƙarfi, ya ƙaramin Isra’ila, gama ni kaina zan taimake ka,” in ji Ubangiji, Mai Fansarka, Mai Tsarkin nan na Isra’ila.

  12. Ishaya 41:15kusan 712 K.H.

    “Duba, zan sa ka cikin abin sussuka, saboda kuma mai kaifi mai haƙora da yawa. Za ka yi sussukar duwatsu ka ragargaza su, ka kuma farfashe tuddai su zama kamar yayi.

  13. Ishaya 41:16kusan 712 K.H.

    Za ka tankaɗe su, iska kuma ta kwashe su, guguwa kuma za tă warwatsa su. Amma za ka yi farin ciki a cikin Ubangiji ka kuma ɗaukaka a cikin Mai Tsarkin nan na Isra’ila.

  14. Ishaya 41:17kusan 712 K.H.

    “Matalauta da mabukata suna neman ruwa, amma babu kome; harsunansu sun bushe saboda ƙishi. Amma Ni Ubangiji zan amsa musu; Ni, Allah na Isra’ila, ba zan yashe su ba.

  15. Ishaya 41:18kusan 712 K.H.

    Zan sa koguna su malalo a ƙeƙasassun tuddai, maɓulɓulan ruwa kuma a kwaruruka. Zan mai da hamada tafkunan ruwa, busasshiyar ƙasa kuma ta zama maɓulɓulan ruwa.

  16. Ishaya 41:19kusan 712 K.H.

    Zan sa a hamada ta tsiro da al’ul da itacen ƙirya, da itacen ci-zaƙi, da zaitun. Zan sa itace mai girma a ƙasashe masu sanyi ya tsiro a ƙeƙasasshiyar ƙasa, tare da fir da kuma saifires,

  17. Ishaya 41:20kusan 712 K.H.

    don mutane su gani su kuma sani, su lura su kuma fahimci, cewa hannun Ubangiji ne ya aikata haka, cewa Mai Tsarkin nan na Isra’ila ya sa abin ya faru.

  18. Ishaya 41:21kusan 712 K.H.

    “Ka gabatar da damuwarka,” in ji Ubangiji. “Ka kawo gardandaminka,” in ji Sarki na Yaƙub.

  19. Ishaya 41:22kusan 712 K.H.

    “Ka shigar da gumakanka don su faɗa mana abin da zai faru. Faɗa mana abubuwan da suka riga suka faru, domin mu lura da su mu kuma san abin da zai faru a ƙarshe. Ko kuwa ku furta mana abubuwan da za su faru,

  20. Ishaya 41:23kusan 712 K.H.

    faɗa mana abin da nan gaba ta ƙunsa, don mu san cewa ku alloli ne. Ku yi wani abu, mai kyau ko mummuna, don mu ji tsoro da fargaba.

  21. Ishaya 41:24kusan 712 K.H.

    Amma ku ba kome ba ne kuma ayyukanku banza da wofi ne; duk wanda ya zaɓe ku abin ƙyama ne.

  22. Ishaya 41:25kusan 712 K.H.

    “Na zuga wani daga arewa, ya kuwa zo, wani daga inda rana ke fitowa wanda yake kira bisa sunana. Yana takawa a kan masu mulki kamar da taɓarya, sai ka ce maginin tukwane yana taka laka.

  23. Ishaya 41:26kusan 712 K.H.

    Wa ya faɗi wannan tun daga farko, don mu sani, ko kafin ya faru, don mu ce, ‘Ya faɗi daidai’? Ba wanda ya faɗa wannan, ba wanda ya riga faɗe shi, ba wanda ya ji wata magana daga gare ku.

  24. Ishaya 41:27kusan 712 K.H.

    Ni ne na farkon da ya ce wa Sihiyona, ‘Duba, ga su nan!’ Na ba wa Urushalima saƙon labari mai daɗi.

  25. Ishaya 41:28kusan 712 K.H.

    Na duba amma ba kowa ba wani a cikinsu da zai ba da shawara, ba wani da zai ba da amsa sa’ad da na tambaye su.