Tsallake zuwa abun ciki

circa 800–400 BC

The Hebrew Prophets

God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.

3,706 ayoyi · 14 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ishaya 1:26kusan 759 K.H.

    Zan maido da alƙalanki kamar yadda suke a dā can, mashawartanki kamar yadda suke da fari. Bayan haka za a ce da ke Birnin Masu Adalci, Amintacciyar Birni.”

  2. Ishaya 1:27kusan 759 K.H.

    Za a fanshi Sihiyona da adalci, masu tubanta kuma da aikin gaskiya.

  3. Ishaya 1:28kusan 759 K.H.

    Amma za a karye ’yan tawaye da masu zunubi, waɗanda suka rabu da Ubangiji kuma za su hallaka.

  4. Ishaya 1:29kusan 759 K.H.

    “Za ku ji kunya saboda masujadan ƙarƙashin itatuwan oak da kuka yi farin ciki; za a kunyata ku saboda lambun da kuka zaɓa.

  5. Ishaya 1:30kusan 759 K.H.

    Za ku zama kamar itacen oak mai busasshen ganyaye, kamar lambu marar ruwa.

  6. Ishaya 1:31kusan 759 K.H.

    Mutum mai ƙarfi zai zama kamar rama, aikinsa kuma kamar tartsatsin wuta; duka za su ƙone tare, ba kuwa wanda zai kashe wutar.”

  7. Ishaya 2:1kusan 759 K.H.

    Ga abin da Ishaya ɗan Amoz ya gani game da Yahuda da Urushalima.

  8. Ishaya 2:2kusan 759 K.H.

    A kwanaki masu zuwa za a kafa dutsen haikalin Ubangiji a matsayin babba cikin duwatsu; za a daga shi bisa tuddai, kuma dukan al’ummai za su bumbunto zuwa gare shi.

  9. Ishaya 2:3kusan 759 K.H.

    Mutane da yawa za su zo su ce, “Ku zo, bari mu haura zuwa dutsen Ubangiji, zuwa gidan Allah na Yaƙub. Zai koya mana hanyoyinsa, domin mu yi tafiya cikin hanyoyinsa.” Dokar za tă fito daga Sihiyona, maganar Ubangiji daga Urushalima.

  10. Ishaya 2:4kusan 759 K.H.

    Zai shari’anta tsakanin al’ummai zai kuma sulhunta faɗar mutane masu yawa. Za su mai da takubansu su zama garemani māsunsu su zama wuƙaƙen askin itatuwa. Al’umma ba za tă ƙara ɗauki takobi a kan al’umma ba, ba kuwa za su ƙara yin horarwar yaƙi.

  11. Ishaya 2:5kusan 759 K.H.

    Ki zo, ya gidan Yaƙub, bari mu yi tafiya a hasken Ubangiji.

  12. Ishaya 2:6kusan 759 K.H.

    Ka rabu da mutanenka, gidan Yaƙub. Sun cika da ayyukan sihiri da aka kawo daga Gabas; suna yin duba kamar Filistiyawa suna tafa hannuwa tare da marasa sanin Allah.

  13. Ishaya 2:7kusan 759 K.H.

    Ƙasarsu ta cika da azurfa da zinariya; dukiyarsu kuma ba iyaka. Ƙasarsu ta cika da dawakai; kekunan yaƙinsu kuma ba iyaka.

  14. Ishaya 2:8kusan 759 K.H.

    Ƙasarsu ta cika da gumaka; sukan rusuna ga aikin hannuwansu, ga abin da yatsotsinsu suka yi.

  15. Ishaya 2:9kusan 759 K.H.

    Saboda an jawo mutum ƙasa aka kuma ƙasƙantar da ɗan adam, kada ku gafarta musu.

  16. Ishaya 2:10kusan 759 K.H.

    Ku tafi cikin duwatsu, ku ɓuya cikin ƙasa daga razanar Ubangiji da kuma darajar ɗaukakarsa!

  17. Ishaya 2:11kusan 759 K.H.

    Za a ƙasƙantar da mai girman kai za a kuma lalatar da fariyar masu ɗaga kai; Ubangiji kaɗai za a ɗaukaka a wannan rana.

  18. Ishaya 2:12kusan 759 K.H.

    Ubangiji Maɗaukaki yana da rana ajiye domin dukan masu girman kai da masu fariya domin dukan waɗanda aka ɗaukaka (zai kuwa ƙasƙantar da su),

  19. Ishaya 2:13kusan 759 K.H.

    domin dukan al’ul na Lebanon, masu tsayi da masu fariya, da kuma dukan itatuwan oak na Bashan,

  20. Ishaya 2:14kusan 759 K.H.

    domin dukan dogayen duwatsu da kuma tuddai masu tsayi,

  21. Ishaya 2:15kusan 759 K.H.

    domin kowace doguwar hasumiya da kowace katanga mai ƙarfi,

  22. Ishaya 2:16kusan 759 K.H.

    domin kowane jirgin ruwan kasuwanci da kuma jirgi mafi girma mafi kyau.

  23. Ishaya 2:17kusan 759 K.H.

    Za a jawo mai girman kai ƙasa a kuma ƙasƙantar da mai ɗaga kai; Ubangiji kaɗai za a ɗaukaka a wannan rana,

  24. Ishaya 2:18kusan 759 K.H.

    za a kuma kawar da gumaka ƙaƙaf.

  25. Ishaya 2:19kusan 759 K.H.

    Mutane za su gudu zuwa kogwannin duwatsu da kuma ramummuka a ƙasa daga razanar Ubangiji da kuma darajar ɗaukakarsa, sa’ad da ya tashi don yă girgiza duniya.