Tsallake zuwa abun ciki

circa 800–400 BC

The Hebrew Prophets

God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.

3,706 ayoyi · 14 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ishaya 16:11kusan 726 K.H.

    Zuciyata tana makoki saboda Mowab kamar garaya, na yi baƙin ciki saboda Kir Hareset.

  2. Ishaya 16:12kusan 726 K.H.

    Sa’ad Mowab ta bayyana a masujadar bisa tudu, tana gajiyar da kanta ne kawai; sa’ad da ta tafi wurin tsafinta don tă yi addu’a, babu wani amfani.

  3. Ishaya 16:13kusan 726 K.H.

    Wannan ita ce maganar da Ubangiji ya riga ya yi game da Mowab.

  4. Ishaya 16:14kusan 726 K.H.

    Amma yanzu Ubangiji ya ce, “Cikin shekara uku, kamar yadda bawan da aka bautar da shi bisa ga yarjejjeniya zai lissafta, haka za a mai da daraja da kuma dukan yawan mutanen Mowab abin reni, daga ɗumbun mutanenta, ’yan kaɗan ne kaɗai za su ragu, za su kuma zama marasa ƙarfi.”

  5. Ishaya 17:1kusan 741 K.H.

    Abin da Allah ya faɗa game da Damaskus. “Duba, Damaskus ba za tă ƙara zama birni ba amma za tă zama tsibin juji.

  6. Ishaya 17:2kusan 741 K.H.

    Za a watse a bar biranen Arower a bar wa tumaki da shanu, waɗanda za su kwanta, ba tare da wani wanda zai tsorata su ba.

  7. Ishaya 17:3kusan 741 K.H.

    Birni mai katanga za tă ɓace daga Efraim, ikon sarauta kuma daga Damaskus; raguwar Aram za tă zama kamar darajar Isra’ila,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.

  8. Ishaya 17:4kusan 741 K.H.

    “A wannan rana ɗaukakar Yaƙub za tă ƙare; kitsen jikinsa zai lalace.

  9. Ishaya 17:5kusan 741 K.H.

    Zai zama kamar sa’ad da mai girbi ya tara hatsin da yake tsaye ya kuma girbe hatsin da hannunsa kamar sa’ad da mutum ya yi kala kawunan hatsi a Kwarin Refayim.

  10. Ishaya 17:6kusan 741 K.H.

    Duk da haka waɗansu kala za su ragu, sai ka ce sa’ad da an karkaɗe itace zaitun, aka bar ’ya’yan zaitun biyu ko uku a can ƙwanƙolin rassan, ko kuma aka bar huɗu ko biyar a rassa na gefe na itace mai ’ya’ya,” in ji Ubangiji, Allah na Isra’ila.

  11. Ishaya 17:7kusan 741 K.H.

    A wannan rana mutane za su nemi Mahaliccinsu su kuma juye idanunsu ga Mai Tsarkin nan na Isra’ila.

  12. Ishaya 17:8kusan 741 K.H.

    Ba za su dubi bagade ba, waɗanda suke aikin hannuwansu, ba za su kuma kula da ginshiƙan Ashera ba da kuma bagadan turaren da yatsotsinsu suka yi.

  13. Ishaya 17:9kusan 741 K.H.

    A wannan rana biranensu masu ƙarfi, waɗanda suka bari saboda Isra’ilawa, za su zama kamar wuraren da aka ƙyale suka zama kufai a jeji. Za su kuma zama kango.

  14. Ishaya 17:10kusan 741 K.H.

    Kun manta da Allah Mai Cetonku; ba ku tuna da Dutse, kagararku ba. Saboda haka, ko da yake kun fita ku shuka tsire-tsire mafi kyau kuka kuma shuka inabin da aka sayo daga waje,

  15. Ishaya 17:11kusan 741 K.H.

    ko da yake a ranar kun shuka su, kuka sa su yi girma, da safe kuma sa’ad da kuka shuka su, kuka sa suka yi toho suka yi fure, duk da haka girbin ba zai zama kome ba a ranar cuta da zafin da ba ta da magani.

  16. Ishaya 17:12kusan 741 K.H.

    Kash, ga hayaniyar al’ummai masu yawa suna hayaniya kamar rurin teku! Kash, ga fushin mutane suna ruri kamar rugugi kamar manyan ruwaye!

  17. Ishaya 17:13kusan 741 K.H.

    Ko da yake mutane suna ruri kamar sukuwar raƙuman ruwa, sa’ad da ya tsawata musu za su gudu can da nisa, aka kore su kamar yayinda iska ya hura a kan tuddai, kamar tattake kuma a cikin guguwa.

  18. Ishaya 17:14kusan 741 K.H.

    Da yamma, sai razana ba tsammani! Kafin safiya, duk sun ɓace! Wannan ne rabon waɗanda suka washe mu, rabon waɗanda suka yi mana ƙwace.

  19. Ishaya 18:1kusan 714 K.H.

    Kaiton ƙasar da ake jin ƙarar fikafikai a bakin kogunan Kush,

  20. Ishaya 18:2kusan 714 K.H.

    wadda ta aiko da jakadu ta teku cikin jiragen ruwan da aka yi da kyauro a bisa ruwa. Ku tafi, ku ’yan saƙo masu sauri, zuwa ga dogayen mutane masu sulɓin jiki, zuwa ga mutanen da ake jin tsoro a ko’ina, al’umma mai ƙarfin iko tana jawabin da ba a saba ji ba, mai ƙasar da koguna suka raba.

  21. Ishaya 18:3kusan 714 K.H.

    Ku dukan mutanen duniya, ku da kuke zama a duniya, sa’ad da aka ɗaga tutar a kan duwatsu, za ku gan shi, sa’ad da kuma aka busa ƙaho, za ku ji shi.

  22. Ishaya 18:4kusan 714 K.H.

    Ga abin da Ubangiji ya faɗa mini, “Zan yi shiru in kuma duba a hankali daga mazaunina, kamar ƙuna mai zafi a hasken rana, kamar girgijen raba a lokacin girbi.”

  23. Ishaya 18:5kusan 714 K.H.

    Gama kafin girbi, sa’ad da furanni suka karkaɗe furanni kuma suka zama ’ya’yan inabin da suka nuna, zai faffalle rassan kuringar inabi da wuƙa, ya yanke ya kuma kwashe rassan da suka bazu.

  24. Ishaya 18:6kusan 714 K.H.

    Duk za a bar su wa tsuntsayen dutse su ci da kuma namun jeji; tsuntsaye kuma za su ci rani a kansu, namun jeji kuma za su yi damina a kansu.

  25. Ishaya 18:7kusan 714 K.H.

    A wannan lokaci za a kawo kyautai wa Ubangiji Maɗaukaki daga dogayen mutane masu sulɓin jiki, daga mutanen da ake jin tsoro a ko’ina, al’umma mai ƙarfin iko na jawabin da ba a saba ji ba, mai ƙasar da koguna suka raba. Za a kawo kyautai zuwa Dutsen Sihiyona, wurin da Sunan Ubangiji Maɗaukaki yake.