Tsallake zuwa abun ciki

circa 800–400 BC

The Hebrew Prophets

God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.

3,706 ayoyi · 14 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Irmiya 52:4kusan 590 K.H.

    A kan rana ta goma ga watan goma, a shekara ta tara ta mulkin Zedekiya, Sarkin Yahuda, sai Nebukadnezzar, Sarkin Babilon, ya zo yaƙi da Urushalima tare da dukan sojojinsa. Suka kewaye ta da yaƙi, suka gina katanga kewaye da ita.

  2. Irmiya 52:5kusan 590 K.H.

    An kewaye birnin da yaƙi har shekara ta goma sha ɗaya ta mulkin Zedekiya.

  3. Irmiya 52:6kusan 588 K.H.

    A kan rana ta tara a watan huɗu na wannan shekara, yunwa ta tsananta ƙwarai a birnin. Mutane suka rasa abin da za su ci.

  4. Irmiya 52:7kusan 588 K.H.

    Sai aka huda katangan birnin, sojojin kuwa suka gudu, suka fita daga cikin birnin da dare ta hanyar ƙofar da take tsakanin bango biyu, kusa da gonar sarki, sa’ad da Babiloniyawa suke kewaye da birnin. Sojojin suka nufi wajen Araba.

  5. Irmiya 52:8kusan 588 K.H.

    Amma sojojin Babiloniyawa suka runtumi sarki Zedekiya, suka ci masa a filayen Yeriko. Dukan sojoji suka yashe shi.

  6. Irmiya 52:9kusan 588 K.H.

    Da aka kama Zedekiya, sai aka kai shi wurin Sarkin Babilon a Ribla a ƙasar Hamat, a nan ne Sarkin Babilon ya yanke masa shari’a.

  7. Irmiya 52:10kusan 588 K.H.

    Sarkin Babilon ya kashe ’ya’yan Zedekiya a idonsa. Ya kuma kashe dukan shugabannin Yahuda a Ribla.

  8. Irmiya 52:11kusan 588 K.H.

    Sa’an nan ya ƙwaƙule idanun Zedekiya, ya kuma sa masa ƙuƙumi, aka kai shi Babilon inda aka sa shi a kurkuku har ran da ya mutu.

  9. Irmiya 52:12kusan 588 K.H.

    A kan rana ta goma ga watan biyar a shekara ta goma sha tara ta sarautar Nebukadnezzar, Sarkin Babilon, sai Nebuzaradan shugaban matsara da kuma ɗan majalisar sarki, ya zo Urushalima.

  10. Irmiya 52:13kusan 588 K.H.

    Sai ya ƙone haikalin Ubangiji, da gidan sarki, da dukan gine-gine masu alfarman da suke Urushalima.

  11. Irmiya 52:14kusan 588 K.H.

    Sojojin Babiloniyawa da suke tare da shugaban matsara, suka rushe dukan katangan Urushalima.

  12. Irmiya 52:15kusan 588 K.H.

    Sa’an nan Nebuzaradan shugaban matsara ya kwashe waɗansu matalauta, da sauran mutane da aka bari a birnin, da waɗanda suka gudu zuwa wurin Sarkin Babilon, da sauran masu sana’a, ya kai su bautar talala a Babilon.

  13. Irmiya 52:16kusan 588 K.H.

    Amma ya bar waɗansu matalauta na gaske a ƙasar don su yi aiki a gonakin inabi, da sauran gonaki.

  14. Irmiya 52:17kusan 588 K.H.

    Babiloniyawa kuwa suka farfasa ginshiƙan tagulla, da dakalai, da babbar kwatarniya, waɗanda suke a haikalin Ubangiji. Suka kwashe tagulla duka suka kai Babilon.

  15. Irmiya 52:18kusan 588 K.H.

    Suka kwashe tukwanen ƙarfe, da manyan cokula, da hantsuka, da daruna, da tasoshin ƙona turare, da kayayyakin tagulla waɗanda ake amfani da su domin hidimar haikali.

  16. Irmiya 52:19kusan 588 K.H.

    Suka kuma kwashe ƙananan kwanonin sha, da farantan wuta, da daruna, da tukwane, da alkukai, da tasoshin ƙona turare, da kwanonin miƙa hadayar sha. Duk abin da yake na zinariya da azurfa, shugaban matsara ya kwashe.

  17. Irmiya 52:20kusan 588 K.H.

    Tagullar da sarki Solomon ya yi wa haikalin Ubangiji da ita, wato, ginshiƙai biyu, da ƙaton kwano mai suna Teku na tagulla, da bijimai goma sha biyu, waɗanda suke ɗauke da kwatarniya, da dakalai, ta fi ƙarfin a auna.

  18. Irmiya 52:21kusan 588 K.H.

    Tsawon kowane ginshiƙi kamu goma sha takwas ne, kewayensa kuwa kamu goma sha biyu ne, kaurinsa kuma huɗu ne. Kowannensu yana da rami a ciki.

  19. Irmiya 52:22kusan 588 K.H.

    A kan kowane ginshiƙi, an yi masa dajiyar tagulla, tsayinta kamu biyar. A bisa kan kowace dajiya akwai raga da siffofin rumman na tagulla kewaye da dajiyar. Ginshiƙi na biyu ma haka yake da siffofin rumman.

  20. Irmiya 52:23kusan 588 K.H.

    Akwai siffofin rumman tasa’in da shida da ake gani a gefen. Dukan siffofin rumman da suke a kan ragar kewaye, guda ɗari ne.

  21. Irmiya 52:24kusan 588 K.H.

    Shugaban matsara kuma ya ɗauki Serahiya babban firist, da Zefaniya wanda yake biye da babban firist, da mutum uku masu tsaron ƙofar, ya tafi da su.

  22. Irmiya 52:25kusan 588 K.H.

    Daga cikin birnin kuma ya ɗauki shugaban sojojin, da mutum bakwai ’yan majalisar sarki, da magatakardan shugaban sojojin wanda yakan tara sojojin ƙasar, da mutane sittin na ƙasar, waɗanda aka same su a birnin, ya tafi da su.

  23. Irmiya 52:26kusan 588 K.H.

    Nebuzaradan shugaban matsara ya tafi da waɗannan mutane wurin Sarkin Babilon a Ribla,

  24. Irmiya 52:27kusan 588 K.H.

    Sarkin Babilon kuwa ya kashe su a Ribla a ƙasar Hamat. Haka aka tafi da mutanen Yahuda bautar talala, daga ƙasarta.

  25. Irmiya 52:28kusan 600 K.H.

    Wannan shi ne yawan mutanen da Nebukadnezzar ya kai su bauta. A shekara ta bakwai ta sarautarsa, ya tafi da Yahudawa 3,023;