Tsallake zuwa abun ciki

circa 800–400 BC

The Hebrew Prophets

God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.

3,706 ayoyi · 14 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Irmiya 51:18kusan 595 K.H.

    Su marasa amfani ne, abubuwan ba’a ne kawai; sa’ad da lokacin hukuncinsu ya kai, za su hallaka.

  2. Irmiya 51:19kusan 595 K.H.

    Wanda yake na wajen Yaƙub ba kamar waɗannan ba ne, gama shi ne Mahalicci dukan abu, har da kabilar abin gādonsa, Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa.

  3. Irmiya 51:20kusan 595 K.H.

    “Kai ne kulkin yaƙina, kayan yaƙina, da kai ne na ragargaza ƙasashe, da kai ne na hallaka mulkoki,

  4. Irmiya 51:21kusan 595 K.H.

    da kai ne na ragargaza doki da mahayi, da kai ne na ragargaza keken yaƙin da matuƙi,

  5. Irmiya 51:22kusan 595 K.H.

    da kai ne na ragargaza miji da mata, da kai ne na ragargaza tsoho da saurayi, da kai ne na ragargaza saurayi da budurwa,

  6. Irmiya 51:23kusan 595 K.H.

    da kai ne na ragargaza makiyayi da garke, da kai ne na ragargaza manoma da dawakan noma, da kai ne na ragargaza masu mulki da shugabanni.

  7. Irmiya 51:24kusan 595 K.H.

    “Zan sāka wa Babilon da dukan mazaunan Babilon a idanunku saboda dukan muguntar da suka aikata a Sihiyona,” in ji Ubangiji.

  8. Irmiya 51:25kusan 595 K.H.

    “Ga shi, ina gāba da kai, ya ke dutse mai hallakarwa, wadda ta hallaka duniya duka,” in ji Ubangiji. “Zan miƙa hannuna gāba da ke, zan mirgina ƙasa daga ƙwanƙolin dutse, zan maishe ki ƙonannen dutse.

  9. Irmiya 51:26kusan 595 K.H.

    Ba za a ɗauki dutsen yin kusurwa daga gare ki ba ko na kafa harsashen gini, gama za ki zama marar amfani har abada,” in ji Ubangiji.

  10. Irmiya 51:27kusan 595 K.H.

    “Ku tā da tuta a ƙasa! Ku busa ƙahoni a cikin ƙasashe! Ku shirya ƙasashe don yaƙi da ita, ku kira waɗannan mulkokin gāba da ita. Ararat, Minni, da Ashkenaz. A naɗa shugaba gāba da ita; ku shirya dawakai kamar fāra.

  11. Irmiya 51:28kusan 595 K.H.

    Ku shirya ƙasashe don yaƙi da ita, sarakunan Medes, gwamnoninsu da dukan masu shugabancinsu da kowace ƙasar da take ƙarƙashin mulkinsu.

  12. Irmiya 51:29kusan 595 K.H.

    Ƙasa ta girgiza tana makyarkyata saboda nufin Ubangiji na gāba da Babilon ya tabbata, nufinsa na mai da ƙasar Babilon kufai don kada kowa yă zauna a can.

  13. Irmiya 51:30kusan 595 K.H.

    Sojojin Babilon sun daina yaƙi, suna zaune a cikin kagaransu. Ƙarfinsu ya ƙare, sun zama mata. An sa wa wuraren zamanta wuta, an karya ƙyamaren ƙofofin garinta.

  14. Irmiya 51:31kusan 595 K.H.

    Maguji yana biye da maguji a guje, jakada yana biye da jakada, don su faɗa wa sarkin Babilon, cewa an ci birninsa a kowane gefe.

  15. Irmiya 51:32kusan 595 K.H.

    An ƙwace mashigai aka ƙone fadamu da wuta, sojoji kuma suka giggice.”

  16. Irmiya 51:33kusan 595 K.H.

    Ni Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila na ce, “’Yar Babilon kamar daɓen masussuka a lokacin da ake sussuka, ba da daɗewa ba lokacin girbe ta zai zo.”

  17. Irmiya 51:34kusan 595 K.H.

    “Nebukadnezzar sarkin Babilon ya cinye mu, ya sa muka rikice, ya maishe mu kamar tulun da babu kome a cikinsa. Ya cinye mu kamar yadda dodon ruwa yakan yi ya kuma cika cikinsa da kayan marmarinmu, sa’an nan kuma ya yi amanmu.

  18. Irmiya 51:35kusan 595 K.H.

    Bari abin da aka yi wa jikinmu yă kasance a bisa Babilon,” in ji mazaunan Sihiyona. “Bari jininmu yă kasance a kan waɗanda suke zama a Babilon,” in ji Urushalima.

  19. Irmiya 51:36kusan 595 K.H.

    Saboda haka ga abin da Ubangiji ya ce, “Duba, zan tsaya muku, zan ɗaukar muku fansa, zan sa tekunta kafe in kuma sa maɓulɓulanta su ƙafe.

  20. Irmiya 51:37kusan 595 K.H.

    Babilon za tă zama tarin juji, wurin zaman diloli, abin ƙyama da abar ba’a, inda ba kowa.

  21. Irmiya 51:38kusan 595 K.H.

    Mutanenta duk suna ruri kamar zakoki, suna gurnani kamar ’ya’yan zaki.

  22. Irmiya 51:39kusan 595 K.H.

    Amma sa’ad da aka farkar da su, zan yi musu biki in sa su sha su bugu, domin yi sowa da dariya, sa’an nan su shiga barcin da ba za su farka ba,” in ji Ubangiji.

  23. Irmiya 51:40kusan 595 K.H.

    “Zan sauko da su kamar tumaki zuwa mayanka, kamar raguna da bunsurai.

  24. Irmiya 51:41kusan 595 K.H.

    “Yadda za a ci Sheshak, taƙamar duniya duka za tă daina! Babilon za tă zama abar ƙyama a cikin al’ummai!

  25. Irmiya 51:42kusan 595 K.H.

    Teku zai malalo a kan Babilon, raƙumansa masu hauka za su rufe ta.