Tsallake zuwa abun ciki

Creation Era

The Great Flood

Humanity's wickedness fills the earth; God preserves Noah and his family through a catastrophic flood.

97 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Farawa 7:4kusan 2348 K.H.

    Kwana bakwai daga yanzu zan aiko da ruwa a duniya yini arba’in da dare arba’in, zan kuma kawar da kowace halitta mai rai da na yi daga doron ƙasa.”

  2. Farawa 7:5kusan 2348 K.H.

    Nuhu ya aikata duk abin da Ubangiji ya umarce shi.

  3. Farawa 7:6kusan 2348 K.H.

    Nuhu yana da shekaru 106 ne sa’ad da aka yi ambaliya ruwa a duniya.

  4. Farawa 7:7kusan 2348 K.H.

    Nuhu da matarsa da ’ya’yansa da matansu, suka shiga jirgi domin su tsira daga ruwa ambaliya.

  5. Farawa 7:8kusan 2348 K.H.

    Biyu-biyu daga dabbobi masu tsabta da marasa tsabta, da tsuntsaye da kuma dukan halittu masu rarrafe a ƙasa,

  6. Farawa 7:9kusan 2348 K.H.

    namiji da ta mace, suka zo wurin Nuhu, suka shiga jirgi, kamar yadda Allah ya umarce Nuhu.

  7. Farawa 7:10kusan 2348 K.H.

    Bayan kwana bakwai kuwa ambaliya ruwa ta sauko a bisa duniya.

  8. Farawa 7:11kusan 2348 K.H.

    A ranar sha bakwai ga wata na biyu, na shekara ta ɗari shida na rayuwar Nuhu, a ran nan sai dukan maɓuɓɓugai na manyan zurfafa suka fashe, tagogin sammai suka buɗe.

  9. Farawa 7:12kusan 2348 K.H.

    Ruwa yana ta kwararowa bisa duniya, yini arba’in da dare arba’in.

  10. Farawa 7:13kusan 2348 K.H.

    A wannan rana Nuhu tare da matarsa da ’ya’yansa maza, Shem, Ham da Yafet da matansu uku suka shiga jirgi.

  11. Farawa 7:14kusan 2348 K.H.

    Tare da su kuwa, akwai kowane naman jeji bisa ga irinsa, da dukan dabbobin gida bisa ga irinsu, da kowace halitta mai rarrafe a ƙasa bisa ga irinta, da kowane tsuntsun gida da na jeji bisa ga irinsa, da dukan abu mai fiffike.

  12. Farawa 7:15kusan 2348 K.H.

    Biyu-biyu na dukan halittu masu numfashi suka zo wurin Nuhu, suka shiga jirgi.

  13. Farawa 7:16kusan 2348 K.H.

    Dabbobi da kowane abu mai rai da suka shiga ciki, namiji ne da ta mace, yadda Allah ya umarci Nuhu. Sa’an nan Ubangiji ya kulle jirgin daga baya.

  14. Farawa 7:17kusan 2348 K.H.

    Kwana arba’in ambaliya ta yi ta saukowa a duniya, sa’ad da ruwa ya yi ta ƙaruwa sai ya yi ta ɗaga jirgin sama, ya kuwa tashi can bisa duniya.

  15. Farawa 7:18kusan 2348 K.H.

    Ruwa ya taso, ya ƙaru ƙwarai a duniya, jirgin kuma ya yi ta yawo a bisa ruwa.

  16. Farawa 7:19kusan 2348 K.H.

    Ruwa ya ƙaru ƙwarai a duniya, ya kuma rufe dukan duwatsu masu tsawo a ƙarƙashin sammai.

  17. Farawa 7:20kusan 2348 K.H.

    Ruwan ya taso ya rufe duwatsu, zurfin ruwa daga duwatsun zuwa inda jirgin yake ya fi ƙafa ashirin.

  18. Farawa 7:21kusan 2348 K.H.

    Kowane abu mai rai da yake tafiya a duniya ya hallaka, tsuntsaye, dabbobin gida, namun jeji, da dukan masu rarrafe waɗanda suke rarrafe a duniya, da kuma dukan mutane.

  19. Farawa 7:22kusan 2348 K.H.

    Kome a busasshiyar ƙasa da yake numfashi a hancinsa ya mutu.

  20. Farawa 7:23kusan 2348 K.H.

    Aka kawar da kowane abu mai rai, mutane da dabbobi da halittu masu rarrafe a ƙasa, da tsuntsayen sama a doron ƙasa, duka aka kawar da su daga duniya. Nuhu kaɗai aka bari da waɗanda suke tare da shi a cikin jirgi.

  21. Farawa 7:24kusan 2348 K.H.

    Ruwa ya mamaye duniya har kwana ɗari da hamsin.

  22. Amma Allah ya tuna da Nuhu da dukan namun jeji da dabbobin da suke tare da shi a cikin jirgi, ya kuma aika da wata iska ta hura dukan duniya, ruwan kuwa ya janye.

  23. Aka toshe maɓuɓɓugan zurfafa da ƙofofin ambaliyar sammai, ruwan sama kuma ya daina saukowa daga sarari.

  24. Ruwan ya janye a hankali daga ƙasa. A ƙarshen kwanaki ɗari da hamsin ɗin, ruwan ya ragu.

  25. A rana ta goma sha bakwai ga watan bakwai, jirgin ya sauka a duwatsun Ararat.