Tsallake zuwa abun ciki

Creation Era

The Great Flood

Humanity's wickedness fills the earth; God preserves Noah and his family through a catastrophic flood.

97 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Ruwan ya ci gaba da janyewa har watan goma. A rana ta fari ga watan goma kuwa ƙwanƙolin duwatsun suka bayyana.

  2. Bayan kwana arba’in, sai Nuhu ya buɗe tagar jirgin da ya yi,

  3. ya saki hankaka. Hankaka ya yi ta kai da kawowa har sai da ruwa ya shanye a duniya.

  4. Sai ya saki kurciya don yă ga in ruwan ya janye daga doron ƙasa.

  5. Amma kurciyar ba tă sami inda za tă sa ƙafafunta ba gama akwai ruwa a dukan doron ƙasa, saboda haka ta komo wurin Nuhu a jirgi. Ya miƙa hannunsa ya ɗauko kurciyar ya shigar da ita wurinsa a cikin jirgi.

  6. Ya ƙara jira kwana bakwai, sai ya sāke aiken kurciyar daga jirgi.

  7. Sa’ad da kurciya ta komo wurinsa da yamma, sai ga ɗanyen ganyen zaitun da ta tsinko a bakinta! Sa’an nan Nuhu ya san cewa ruwa ya janye daga duniya.

  8. Ya ƙara jira kwana bakwai, sai ya sāke aiken kurciyar, amma a wannan ƙaro ba tă komo wurinsa ba.

  9. Farawa 8:13kusan 2347 K.H.

    A rana ta fari ga wata na fari wanda Nuhu ya cika shekaru 601, ruwa ya shanye a ƙasa. Sai Nuhu ya buɗe murfin jirgin, ya ga cewa doron ƙasa ya bushe.

  10. Farawa 8:14kusan 2347 K.H.

    A ran ashirin da bakwai ga wata na biyu, ƙasa ta bushe ƙaƙaf.

  11. Farawa 8:15kusan 2347 K.H.

    Sa’an nan Allah ya ce wa Nuhu,

  12. Farawa 8:16kusan 2347 K.H.

    “Fito daga jirgin, kai da matarka da ’ya’yanka maza da matansu.

  13. Farawa 8:17kusan 2347 K.H.

    Ka fitar da kowane iri halitta mai rai da take tare da kai waje, tsuntsaye, dabbobi, da dukan halittu masu rarrafe a ƙasa, don su yi ta haihuwa, su yi yawa, su ƙaru a duniya.”

  14. Farawa 8:18kusan 2347 K.H.

    Sai Nuhu ya fito tare da matarsa da ’ya’yansa maza da matan ’ya’yansa,

  15. Farawa 8:19kusan 2347 K.H.

    da kowace irin dabba, da kowane mai rarrafe, da kowane irin tsuntsu, da kowane irin abu da yake tafiya a bisa duniya, suka fito daga jirgi daki-daki bisa ga irinsu.

  16. Farawa 8:20kusan 2347 K.H.

    Sai Nuhu ya gina bagaden hadaya ga Ubangiji, ya ɗiba waɗansu dabbobi da tsuntsaye masu tsabta, ya yi hadaya ta ƙonawa da su a kan bagaden.

  17. Farawa 8:21kusan 2347 K.H.

    Da Ubangiji ya ji ƙanshi mai daɗi, sai ya ce a zuciyarsa, “Ba zan ƙara la’anta ƙasa saboda mutum ba, ko da yake dukan tunanin zuciyar mutum mugu ne tun yana ƙarami. Ba kuwa zan ƙara hallaka dukan halittu masu rai, kamar yadda na yi ba.

  18. Farawa 8:22kusan 2347 K.H.

    “Muddin duniya tana nan, lokacin shuki da na girbi, lokacin sanyi da na zafi, lokacin damina da na rani, dare da rana ba za su daina ba.”

  19. Sa’an nan Allah ya sa wa Nuhu da ’ya’yansa maza albarka, yana ce musu, “Ku haifi ’ya’ya, ku ƙaru, ku kuma cika duniya.

  20. Dukan namun jeji da dukan tsuntsayen sama da kowace halitta mai rarrafe a ƙasa, da dukan kifayen teku, za su riƙa jin tsoronku, suna fargaba. An sa su a cikin hannuwanku.

  21. Kome da yake da rai wanda yake tafiya, zai zama abincinku. Kamar yadda na ba ku kowane irin ganye, haka na ba ku kome da kome.

  22. “Akwai abu ɗaya da ba za ku ci ba, wato, nama wanda jininsa yake cikinsa tukuna.

  23. Game da jinin ranka kuwa lalle zan bukaci lissafi. Zan bukaci lissafi daga kowane dabba. kuma daga kowane mutum, shi ma zan bukaci lissafi game da ran ɗan’uwansa.

  24. “Duk wanda ya zub da jinin mutum, ta hannun mutum za a zub da jininsa; gama a cikin siffar Allah ne, Allah ya yi mutum.

  25. Amma ku, ku yi ta haihuwa, ku ƙaru; ku yaɗu a duniya, ku yi yawa a bisanta.”