Tsallake zuwa abun ciki

circa 605–538 BC

The Babylonian Exile

Jerusalem falls and the temple burns; Ezekiel and Daniel minister among the exiles as Lamentations mourns the city's ruin.

1,784 ayoyi · 3 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ezekiyel 24:5kusan 590 K.H.

    ka kama mafi kyau daga cikin garken. Ka tara itace a ƙarƙashinta saboda ƙasusuwan; ka sa ta tafasa ka kuma dafa ƙasusuwan a cikinta.

  2. Ezekiyel 24:6kusan 590 K.H.

    “ ‘Gama wannan shi ne abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Kaito birnin nan mai zubar da jini, ga tukunya wadda take da tsatsa, wadda tsatsarta ba za tă fita ba! Ka fitar da shi gunduwa-gunduwa ba tare da jefa ƙuri’a a kansu ba.

  3. Ezekiyel 24:7kusan 590 K.H.

    “ ‘Gama zubar da jini yana a tsakiyarta, ta zubar da shi a dutsen da yake a fili; ba tă zubar da shi a ƙasa ba, inda ƙura za tă rufe shi.

  4. Ezekiyel 24:8kusan 590 K.H.

    Don a zuga hasala a kuma yi sakayya na sa jininta a dutsen da ba a rufe ba, saboda kada a rufe.

  5. Ezekiyel 24:9kusan 590 K.H.

    “ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Kaito birnin nan mai zubar da jini! Ni ma zan jibge itace da yawa.

  6. Ezekiyel 24:10kusan 590 K.H.

    Ka tula gumagumai ka kuma ƙuna wuta. Ka dafa naman da kyau, kana haɗawa da yaji; ka kuma bar ƙasusuwan su ƙone.

  7. Ezekiyel 24:11kusan 590 K.H.

    Sa’an nan ka sa tukunyan nan da babu kome a kan garwashi sai ta yi zafi har darmarta ta yi ja wur domin dattinta ya narke tsatsarta kuma ta ƙone.

  8. Ezekiyel 24:12kusan 590 K.H.

    Ta gajiyar da dukan ƙoƙari; ba a fid da tsatsarta nan mai yawa ba, kai, ko a wuta ma.

  9. Ezekiyel 24:13kusan 590 K.H.

    “ ‘Yanzu ƙazantarki ita ce lalaci. Domin na yi ƙoƙari in tsabtacce ke amma ba ki tsabtattu daga ƙazantarki ba, ba za ki ƙara yin tsabta ba sai hasalata a kanki ya kwanta.

  10. Ezekiyel 24:14kusan 590 K.H.

    “ ‘Ni Ubangiji na faɗa. Lokaci ya zo da zan aikata. Ba zan janye ba; ba zan ji tausayi ba, ba kuwa zan bari ba. Za a hukunta ki bisa ga hali da ayyukanki, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”

  11. Ezekiyel 24:15kusan 590 K.H.

    Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,

  12. Ezekiyel 24:16kusan 590 K.H.

    “Ɗan mutum, da farat ɗaya ina gab da ɗauke abin da idanunka suke jin daɗin gani. Duk da haka kada ka yi makoki ko ka yi kuka ko ka zub da hawaye.

  13. Ezekiyel 24:17kusan 590 K.H.

    Ka yi nishi shiru; kada ka yi makoki saboda matacciyar. Ka naɗa rawaninka ka kuma sa takalmanka a ƙafa; kada ka rufe sashen fuskarka daga ƙasa ko ka ci abincin da masu kuka sukan ci.”

  14. Ezekiyel 24:18kusan 590 K.H.

    Da gari ya waye, sai na yi magana da mutane, da yamma kuwa matata ta rasu. Kashegari na yi yadda aka umarce ni.

  15. Ezekiyel 24:19kusan 590 K.H.

    Sai mutane suka tambaye ni suka ce, “Ba za ka faɗa mana abin da waɗannan abubuwa suke nufi a gare mu ba?”

  16. Ezekiyel 24:20kusan 590 K.H.

    Sai na ce musu, “Maganar Ubangiji ta zo mini cewa

  17. Ezekiyel 24:21kusan 590 K.H.

    faɗa wa gidan Isra’ila, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gab da ƙazantar da wuri mai tsarkina, kagarar da kuke taƙama, abin da idanunku suke jin daɗin gani, abin faranta zuciyarku. ’Ya’yanku maza da mata waɗanda kun bari a baya za su mutu ta wurin takobi.

  18. Ezekiyel 24:22kusan 590 K.H.

    Za ku kuma yi yadda na yi. Ba za ku rufe sashe ƙasa na fuskarku ko ku ci abinci da masu kuka sukan ci ba.

  19. Ezekiyel 24:23kusan 590 K.H.

    Za ku naɗa rawunanku a kai ku sa takalmanku a ƙafafunku. Ba za ku yi kuka ko makoki ba amma za ku lalace saboda zunubanku ku kuma yi ta yin nishi.

  20. Ezekiyel 24:24kusan 590 K.H.

    Ezekiyel zai zama alama gare ku; za ku yi daidai yadda ya yi. Sa’ad da wannan ya faru, za ku san cewa ni ne Ubangiji Mai Iko Duka.’

  21. Ezekiyel 24:25kusan 590 K.H.

    “Kai kuma ɗan mutum, a ranar da zan ɗauke musu kagararsu, farin cikinsu da darajarsu, abin da idanunsu ke jin daɗin gani, abin da yake faranta musu zuciya, da kuka ’ya’yansu maza da mata,

  22. Ezekiyel 24:26kusan 590 K.H.

    a ranan nan wanda ya tsere zai zo don yă ba ka labari.

  23. Ezekiyel 24:27kusan 590 K.H.

    A lokacin bakinka zai buɗe, za ka yi magana da shi ba kuwa za ka ƙara yin shiru ba. Ta haka za ka zama alama gare su, za su kuwa san cewa ni ne Ubangiji.”

  24. Ezekiyel 25:1kusan 590 K.H.

    Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,

  25. Ezekiyel 25:2kusan 590 K.H.

    “Ɗan mutum, ka fuskanci wajen Ammonawa ka kuma yi annabci a kansu.