Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446 BC

Sinai & The Law

God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.

1,657 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Firistoci 27:3kusan 1491 K.H.

    ga yadda ma’aunin biyan zai kasance, mutum mai shekara tsakanin ashirin da sittin, za a biya azurfa hamsin.

  2. Firistoci 27:4kusan 1491 K.H.

    Mace kuma za a biya azurfa talatin.

  3. Firistoci 27:5kusan 1491 K.H.

    Saurayi mai shekara tsakanin biyar da ashirin, za a biya azurfa ashirin, yarinya kuma azurfa goma.

  4. Firistoci 27:6kusan 1491 K.H.

    Yaro mai shekara tsakanin wata ɗaya da shekara biyar, za a biya azurfa biyar, ’yar yarinya kuma azurfa uku.

  5. Firistoci 27:7kusan 1491 K.H.

    Namijin da ya fi shekara sittin, za a biya azurfa goma sha biyar, mace kuma azurfa goma.

  6. Firistoci 27:8kusan 1491 K.H.

    In mai alkawarin matalauci ne da ba zai iya biyan ƙayyadadden abin da aka tsara ba, sai yă tafi wurin firist, shi firist kuma yă duba yadda mutumin da ya yi alkawarin zai iya biya. Sa’an nan mutumin zai biya abin da firist ya faɗa.

  7. Firistoci 27:9kusan 1491 K.H.

    “ ‘In abin da ya yi alkawarin yardajje ne a matsayin hadaya ga Ubangiji, wannan dabbar da aka bayar ga Ubangiji, za tă zama mai tsarki.

  8. Firistoci 27:10kusan 1491 K.H.

    Kada yă yi musayarta ko yă yi musaya mai kyau da marar kyau, ko marar kyau da mai kyau; in lalle ne yă yi musayar dabbar da wata, to, duk wannan da kuma wanda zai yi musayar da ita za su zama masu tsarki.

  9. Firistoci 27:11kusan 1491 K.H.

    In abin da ya yi alkawari dabba ce marar tsarki, wadda ba yardajje ba ce, a matsayin hadaya ga Ubangiji, dole a kai dabbar wa firist,

  10. Firistoci 27:12kusan 1491 K.H.

    wanda zai yanke hukunci dacewarta, ko mai kyau ce, ko marar kyau. Duk darajar da firist ya kimanta, haka za tă zama.

  11. Firistoci 27:13kusan 1491 K.H.

    In mai shi yana so yă fanshi dabbar, dole yă ƙara kashi ɗaya bisa biyar na darajarta.

  12. Firistoci 27:14kusan 1491 K.H.

    “ ‘In mutum ya miƙa gidansa a matsayin wani abu mai tsarki ga Ubangiji, firist zai daidaita dacewar ko mai kyau ne, ko marar kyau. Duk darajar da firist ya kimanta, haka za tă zama.

  13. Firistoci 27:15kusan 1491 K.H.

    In mutumin da ya keɓe gidansa ya fanshe shi, dole yă ƙara kashi ɗaya bisa biyar na darajar, gidan kuma zai zama nasa.

  14. Firistoci 27:16kusan 1491 K.H.

    “ ‘In wani ya keɓe wa Ubangiji wani sashe daga cikin gonarsa ta gādo, sai yă kimanta kuɗin gonar daidai da yawan irin da za a iya shuka a gonar. Za a kimanta kuɗin a kan shekel hamsin na irin sha’ir.

  15. Firistoci 27:17kusan 1491 K.H.

    In ya keɓe gonarsa a Shekara ta Murna, darajar da aka kimanta za tă zauna.

  16. Firistoci 27:18kusan 1491 K.H.

    Amma in ya keɓe gonar bayan Shekara ta Murnan, firist zai kimanta darajar bisa ga yawan shekarun da suka rage har zuwa Shekara ta Murna mai zuwa, sai a rage darajar da aka kimanta a kanta.

  17. Firistoci 27:19kusan 1491 K.H.

    In mutumin da ya keɓe gonar, yana so yă fanshe ta, to, dole yă ƙara kashi ɗaya bisa biyar na darajarta, gonar kuwa tă zama nasa.

  18. Firistoci 27:20kusan 1491 K.H.

    In kuma bai fanshe gonar ba, ko kuwa in ya sayar wa wani dabam, ba za a taɓa fanshe ta ba.

  19. Firistoci 27:21kusan 1491 K.H.

    Sa’ad da aka saki gonar a Shekara ta Murna, za tă zama mai tsarki, a matsayin gonar da aka miƙa ga Ubangiji, za tă zama mallakar firistoci.

  20. Firistoci 27:22kusan 1491 K.H.

    “ ‘In mutum ya keɓe gonar da ya saya, wadda take ba sashe na gonar iyali ba, ga Ubangiji,

  21. Firistoci 27:23kusan 1491 K.H.

    firist zai kimanta darajarta har Shekara ta Murna, dole kuma mutumin yă biya darajarta a ranar, a matsayin wani abu mai tsarki ga Ubangiji.

  22. Firistoci 27:24kusan 1491 K.H.

    A Shekara ta Murna ɗin, gonar za tă dawo ga mutumin da aka saye ta daga wurinsa, wanda yake mai gonar.

  23. Firistoci 27:25kusan 1491 K.H.

    A kimanta kowace daraja bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, gera ashirin ga shekel.

  24. Firistoci 27:26kusan 1491 K.H.

    “ ‘Ba wani da zai iya keɓe ɗan farin dabba, da yake ɗan fari ya riga ya zama na Ubangiji, ko na saniya, ko na tunkiya, na Ubangiji ne.

  25. Firistoci 27:27kusan 1491 K.H.

    In tana cikin dabbobin da suke marasa tsarki, zai iya saye ta a darajar da aka kimanta, yă ƙara da kashi ɗaya bisa biyar na darajarta. In bai fanshe ta ba, sai a sayar da ita a darajar da aka kimanta.