- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1446 BC
Sinai & The Law
God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Firistoci 25:54kusan 1491 K.H.
“ ‘Ko ma ba a fanshe shi a ɗaya daga cikin waɗannan hanyoyi ba, sai a sake shi da ’ya’yansa a Shekara ta Murna,
- Firistoci 25:55kusan 1491 K.H.
gama Isra’ilawa nawa ne a matsayin bayi. Su bayina ne waɗanda na saya daga Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.
- Firistoci 26:1kusan 1491 K.H.
“ ‘Kada ku yi gumaka, ko ku kafa siffa, ko al’amudi wa kanku, kada kuma ku sa sassaƙaƙƙun duwatsu a ƙasarku don ku rusuna musu. Ni ne Ubangiji Allahnku.
- Firistoci 26:2kusan 1491 K.H.
“ ‘Ku kiyaye Asabbataina, ku kuma ba wa wuri mai tsarkina girma. Ni ne Ubangiji.
- Firistoci 26:3kusan 1491 K.H.
“ ‘In kuka kiyaye farillaina, kuka yi biyayya da umarnaina,
- Firistoci 26:4kusan 1491 K.H.
zan aika da ruwan sama a lokacinsa, ƙasa kuma za tă ba da hatsi, itatuwa kuma za su haihu ’ya’yansu.
- Firistoci 26:5kusan 1491 K.H.
Masussukanku za su ci gaba har lokacin girbin inabi, girbin inabi kuma zai ci gaba har lokacin shuki, za ku kuma ci duk abincin da kuke so cikin salama a ƙasarku.
- Firistoci 26:6kusan 1491 K.H.
“ ‘Zan ba ku salama a ƙasar, za ku kuwa kwanta, kuma babu wani da zai tsorata ku. Zan kori mugayen namun jeji daga ƙasar, takobi kuma ba zai ratsa cikin ƙasarku ba.
- Firistoci 26:7kusan 1491 K.H.
Za ku kori abokan gābanku, za su kuwa fāɗi a kaifin takobi a gabanku.
- Firistoci 26:8kusan 1491 K.H.
Mutanenku biyar za su kori mutum ɗari, mutanenku ɗari kuma za su kori mutane dubu goma, abokan gābanku kuma za su fāɗi a kaifin takobi a gabanku.
- Firistoci 26:9kusan 1491 K.H.
“ ‘Zan dube ku da idon rahama, in kuma sa ku riɓaɓɓanya ku kuma ƙaru, zan kiyaye alkawarina da ku.
- Firistoci 26:10kusan 1491 K.H.
Za ku ci gaba da cin girbin bara, har ku fitar da shi don ku sami wurin saboda sabo.
- Firistoci 26:11kusan 1491 K.H.
Zan kafa wurin zamana a cikinku, ba zan kuma yi ƙyamarku ba.
- Firistoci 26:12kusan 1491 K.H.
Zan yi tafiya a cikinki in kuma zama Allahnku, za ku kuwa zama mutanena.
- Firistoci 26:13kusan 1491 K.H.
Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar don kada ku ƙara zama bayi ga Masarawa; na karya sandunan wahalarku, na kuma bar ku ku yi tafiya a sake.
- Firistoci 26:14kusan 1491 K.H.
“ ‘Amma in za ku kasa kunne gare ni, ku kuma aikata dukan waɗannan umarnai,
- Firistoci 26:15kusan 1491 K.H.
in kuka kuma ƙi farillaina, kuka yi ƙyamar dokokina, kuka kuma kāsa kiyaye umarnaina, har kuka karya alkawarina,
- Firistoci 26:16kusan 1491 K.H.
to, zan yi muku wannan. Zan kawo muku abin bantsoro, cututtuka da zazzaɓin da zai lalatar da idonku, yă kuma sa ranku a wahala. Za ku shuka iri a banza, domin abokan gābanku ne za su ci.
- Firistoci 26:17kusan 1491 K.H.
Zan yi gāba da ku har abokan gābanku su ci ku a yaƙi, su waɗanda suke ƙinku za su yi mulki a kanku, za ku gudu ba tare da wani yana korinku ba.
- Firistoci 26:18kusan 1491 K.H.
“ ‘In bayan dukan wannan, ba ku saurare ni ba, zan hukunta ku saboda zunubanku har sau bakwai.
- Firistoci 26:19kusan 1491 K.H.
Zan karya ikonku wanda kuke fariya da shi, in hana ruwan sama, ƙasa kuma tă zama kamar tagulla.
- Firistoci 26:20kusan 1491 K.H.
Ƙarfinku zai ƙare a banza domin ƙasarku ba za tă ba da hatsi ba, balle itatuwan ƙasar su ba da ’ya’ya.
- Firistoci 26:21kusan 1491 K.H.
“ ‘In kuka ci gaba da tayar mini, kuka ƙi ku saurare ni, zan ninka wahalolinku sau bakwai, yadda ya dace da zunubanku.
- Firistoci 26:22kusan 1491 K.H.
Zan aika da mugayen namun jeji a kanku, za su kuwa kashe ’ya’yanku, su hallaka shanunku, su rage yawanku, ku zama kaɗan. Wannan zai sa a rasa mutane a kan hanyoyinku.
- Firistoci 26:23kusan 1491 K.H.
“ ‘In duk da waɗannan abubuwa, ba ku yarda da gyaran da nake yi muku ba, kuka ci gaba da yin adawa da ni,