Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446 BC

Sinai & The Law

God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.

1,657 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Firistoci 26:24kusan 1491 K.H.

    zan yi adawa da ku, zan kuma aukar muku saboda zunubanku har sau bakwai.

  2. Firistoci 26:25kusan 1491 K.H.

    Zan kawo takobi a kanku don in yi ramuwa saboda karya alkawarin da kuka yi. Sa’ad da kuka janye zuwa cikin biranenku, zan aika da annoba a cikinku, za a kuwa ba da ku ga hannun abokan gāba.

  3. Firistoci 26:26kusan 1491 K.H.

    Sa’ad da na yanke abincinku, mata goma za su dafa abinci a murhu ɗaya, za su kuma rarraba abincin a ma’auni. Za ku ci amma ba za ku ƙoshi ba.

  4. Firistoci 26:27kusan 1491 K.H.

    “ ‘In duk da haka kuka ci gaba da ƙin saurare ni, kuka ci gaba da yin adawa da ni,

  5. Firistoci 26:28kusan 1491 K.H.

    cikin fushina, sai in yi adawa da ku, in kuma hukunta ku saboda zunubanku har sau bakwai.

  6. Firistoci 26:29kusan 1491 K.H.

    Za ku ci naman ’ya’yanku maza da na ’ya’yanku mata.

  7. Firistoci 26:30kusan 1491 K.H.

    Zan rurrushe dukan masujadanku, in yanke bagadanku na turare, in yi tarin gawawwakinku a kan gumakanku, zan kuma yi ƙyamarku.

  8. Firistoci 26:31kusan 1491 K.H.

    Zan mai da biranenku kango, in lalace wuraren tsarkinku, ba zan kuma shaƙi ƙanshi hadayunku ba.

  9. Firistoci 26:32kusan 1491 K.H.

    Zan mai da ƙasarku kango har abokan gābanku da suke zama a wurin su yi mamaki.

  10. Firistoci 26:33kusan 1491 K.H.

    Zan watsar da ku cikin al’ummai, in kuma ja takobina in kore ku. Ƙasarku za tă zama kufai, biranenku kuma su zama kango.

  11. Firistoci 26:34kusan 1491 K.H.

    Sa’an nan ƙasar za tă ji daɗin hutun shekarun Asabbacinta, a dukan lokutan da take kango, ku kuwa kuna a ƙasar abokan gābanku, sa’an nan ƙasar za tă huta ta ji daɗin asabbatanta.

  12. Firistoci 26:35kusan 1491 K.H.

    A dukan lokutan da take kango, ƙasar za tă sami hutun da ba tă samu a lokutan asabbatan da kuke zama a cikinta ba.

  13. Firistoci 26:36kusan 1491 K.H.

    “ ‘Ga waɗanda za su ragu kuwa, zan cika zukatansu da tsoro a ƙasashen abokan gābansu har motsin ganyen da iska ta hura zai sa su ruga da gudu. Za su yi gudu kamar suna gudu daga takobi ne, za su kuma fāɗi, ko da yake babu wanda yake korinsu.

  14. Firistoci 26:37kusan 1491 K.H.

    Za su yi karo da juna kamar waɗanda suke tsere wa takobi, ko da yake babu wanda yake korinsu. Ta haka ba za ku iya tsaya a gaban abokan gābanku ba.

  15. Firistoci 26:38kusan 1491 K.H.

    Za ku mutu a cikin al’ummai, ƙasar abokan gābanku za tă cinye ku.

  16. Firistoci 26:39kusan 1491 K.H.

    Sauranku da suka ragu za su lalace a ƙasashen abokan gābansu saboda zunubansu; da kuma saboda zunuban kakanninsu.

  17. Firistoci 26:40kusan 1491 K.H.

    “ ‘Amma in suka tuba daga zunubansu da zunuban kakanninsu, da cin amanar da suka yi mini, da kuma adawar da suka yi da ni,

  18. Firistoci 26:41kusan 1491 K.H.

    waɗanda suka sa na yi adawa da su har da na aika da su ƙasar abokan gābansu, sa’ad da suka ƙasƙantar da zukatansu marasa kaciya, suka kuma biya hukuncin zunubansu,

  19. Firistoci 26:42kusan 1491 K.H.

    zan tuna da alkawarina da Yaƙub, da alkawarina da Ishaku, da kuma alkawarina da Ibrahim, zan tuna da ƙasar.

  20. Firistoci 26:43kusan 1491 K.H.

    Gama za su gudu su bar ƙasar, ƙasar kuwa ta ji daɗin asabbatanta yayinda take kango muddin ba su ciki. Za su biya hukuncin zunubansu domin sun ƙi dokokina, suka kuma yi ƙyamar farillaina.

  21. Firistoci 26:44kusan 1491 K.H.

    Duk da haka, sa’ad da suke a ƙasar abokan gābansu, ba zan ƙi su, ko in yi ƙyamarsu, in hallaka su ƙaƙaf, har in karya alkawarina da su ba. Ni ne Ubangiji Allahnsu.

  22. Firistoci 26:45kusan 1491 K.H.

    Amma saboda su, zan tuna da alkawarin da na yi da kakanninsu, waɗanda na fitar da su daga Masar a idon al’ummai, don in zama Allahnsu. Ni ne Ubangiji.’ ”

  23. Firistoci 26:46kusan 1491 K.H.

    Waɗannan su ne farillai, da dokoki, da kuma ƙa’idodin da Ubangiji ya kafa a Dutsen Sinai, tsakaninsa da Isra’ilawa ta wurin Musa.

  24. Firistoci 27:1kusan 1491 K.H.

    Ubangiji ya ce wa Musa,

  25. Firistoci 27:2kusan 1491 K.H.

    “Ka yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Duk sa’ad da mutum ya yi rantsuwa ta musamman zai keɓe wani ga Ubangiji, ta wurin biyan kuɗaɗen fansa,