Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446 BC

Sinai & The Law

God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.

1,657 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Firistoci 23:21kusan 1490 K.H.

    A wannan rana za ku yi taro mai tsarki, ba kuwa za ku yi aiki na kullum ba. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla wa tsararraki masu zuwa, a ko’ina kuke da zama.

  2. Firistoci 23:22kusan 1490 K.H.

    “ ‘Sa’ad da kuka yi girbin gonarku, kada ku girbe har ƙarshen gefen gonar, ko ku yi kalar girbinku. Ku bar su wa matalauta da baƙi. Ni ne Ubangiji Allahnku.’ ”

  3. Firistoci 23:23kusan 1490 K.H.

    Ubangiji ya ce wa Musa,

  4. Firistoci 23:24kusan 1490 K.H.

    “Faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘A ranar farko ga wata na bakwai, za tă zama ranar hutu, rana ce ta tuni da yin taro mai tsarki na sujada da za a fara busar ƙaho.

  5. Firistoci 23:25kusan 1490 K.H.

    Kada ku yi aiki na kullum, amma ku miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji.’ ”

  6. Firistoci 23:26kusan 1490 K.H.

    Ubangiji ya ce wa Musa,

  7. Firistoci 23:27kusan 1490 K.H.

    “Rana ta goma ta wata bakwai, za tă zama Ranar Kafara. Sai ku yi taro mai tsarki don ku yi mūsun kanku ku kuma miƙa hadayar da aka yi da wuta ga Ubangiji.

  8. Firistoci 23:28kusan 1490 K.H.

    Kada ku yi aiki a ranar, gama Ranar Kafara ce, sa’ad da za a yi kafara saboda ku a gaban Ubangiji Allahnku.

  9. Firistoci 23:29kusan 1490 K.H.

    Duk wanda bai yi mūsun kansa a wannan rana ba, dole a raba shi daga mutanensa.

  10. Firistoci 23:30kusan 1490 K.H.

    Zan hallaka duk wani da ya yi aiki a wannan rana daga mutanensa.

  11. Firistoci 23:31kusan 1490 K.H.

    Sam ba za ku yi wani aiki ba. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ce, wa tsararraki masu zuwa, a ko’ina kuke da zama.

  12. Firistoci 23:32kusan 1490 K.H.

    Asabbaci ne na hutu dominku, kuma dole ku yi mūsun kanku. Daga yamman rana ta tara ga wata, har zuwa yamma na biye, za ku kiyaye Asabbacinku.”

  13. Firistoci 23:33kusan 1490 K.H.

    Ubangiji ya ce wa Musa,

  14. Firistoci 23:34kusan 1490 K.H.

    “Faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘A ranar goma sha biyar ga wata na bakwai, za a fara Bikin Tabanakul na Ubangiji, zai kuma ɗauki kwana bakwai.

  15. Firistoci 23:35kusan 1490 K.H.

    A ranar farko za tă zama ta taro mai tsarki, kada ku yi aiki na kullum.

  16. Firistoci 23:36kusan 1490 K.H.

    Kwana bakwai za ku miƙa hadayun da aka yi da wuta ga Ubangiji, a rana ta takwas, ku yi taro mai tsarki, ku kuma miƙa hadayar da aka yi da wuta ga Ubangiji. Wannan ranar rufewar taro ce; kada ku yi aiki na kullum.

  17. Firistoci 23:37kusan 1490 K.H.

    (“ ‘Waɗannan su ne bukukkuwan da Ubangiji ya kafa, waɗanda za ku yi a matsayin tsarkakakkun taro, don kawo hadayun da aka yi da wuta ga Ubangiji, hadayu na ƙonawa da hadayu na hatsi, sadaka da kuma hadayu na sha, da ake bukata kowace rana.

  18. Firistoci 23:38kusan 1490 K.H.

    Waɗannan hadayu, ƙari ne a kan waɗannan na Asabbatan Ubangiji, haɗe kuma da kyautanku, da kome da kuka yi alkawari, da kuma hadayu yardar ran da za ku ba wa Ubangiji.)

  19. Firistoci 23:39kusan 1490 K.H.

    “ ‘Saboda haka, farawa daga ranar goma sha biyar ga watan bakwai, bayan kun tara hatsin gona, ku yi bikin Ubangiji kwana bakwai; rana ta fari, rana hutu ce, rana ta takwas kuma rana hutu ce.

  20. Firistoci 23:40kusan 1490 K.H.

    A rana ta fari, za ku ɗebi zaɓaɓɓun ’ya’yan itatuwa daga itatuwa, da rassan dabino, rassa masu ganye, da kuma ganyayen itacen wardi na rafi, ku yi farin ciki a gaban Ubangiji Allahnku, kwana bakwai.

  21. Firistoci 23:41kusan 1490 K.H.

    Za ku kiyaye bikin nan har kwana bakwai a kowace shekara ga Ubangiji. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla wa tsarraraki masu zuwa, ku kiyaye ta a wata na bakwai.

  22. Firistoci 23:42kusan 1490 K.H.

    Ku zauna a bukkoki kwana bakwai. Dukan ’yan ƙasa haifaffun Isra’ilawa, za su zauna a bukkoki

  23. Firistoci 23:43kusan 1490 K.H.

    don zuriyarku tă san cewa na sa Isra’ilawa suka zauna a bukkoki sa’ad da na fitar da su daga Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.’ ”

  24. Firistoci 23:44kusan 1490 K.H.

    Saboda haka Musa ya sanar wa Isra’ilawa ƙayyadaddun bukukkuwan Ubangiji.

  25. Firistoci 24:1kusan 1490 K.H.

    Ubangiji ya ce wa Musa,