- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1446 BC
Sinai & The Law
God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Firistoci 24:2kusan 1490 K.H.
“Ka umarci Isra’ilawa su kawo tsabtataccen mai na zaitun da aka matse, don ƙuna fitilun yadda harshen wutar ba zai taɓa mutuwa ba.
- Firistoci 24:3kusan 1490 K.H.
Za a ajiye su waje da labulen Wuri Mafi Tsarki a Tentin Sujada, Haruna zai riƙa kula da fitilun a gaban Ubangiji, daga yamma zuwa safiya. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla wa tsararraki masu zuwa.
- Firistoci 24:4kusan 1490 K.H.
Dole a ci gaba da shirya fitilu a kan wurin ajiye fitila na zinariya, a gaban Ubangiji.
- Firistoci 24:5kusan 1490 K.H.
“Ɗauki gari mai laushi a gasa dunƙulen burodi goma sha biyu, a yi amfani da humushi biyu na garwan gari don kowace burodi.
- Firistoci 24:6kusan 1490 K.H.
A shirya su jeri biyu, guda shida a kowane jeri a kan teburin da aka yi da zinariya zalla, a gaban Ubangiji.
- Firistoci 24:7kusan 1490 K.H.
Za a zuba turare a kowane layin dunƙulen burodin don yă kasance abin tunawa a bisa burodin. Turaren zai ƙone a madadin burodin don yă zama kamar hadayar da aka miƙa da wuta ga Ubangiji.
- Firistoci 24:8kusan 1490 K.H.
Za a shirya wannan gurasa a gaban Ubangiji kowane Asabbaci, a madadin Isra’ilawa a matsayin madawwamin alkawari.
- Firistoci 24:9kusan 1490 K.H.
Wannan burodin zai zama na Haruna da ’ya’yansa maza, waɗanda za su ci a tsattsarkan wuri, gama sashe ne mafi tsarki na rabonsu na kullum na hadayar da aka yi da wuta ga Ubangiji.”
- Firistoci 24:10kusan 1490 K.H.
To, ɗan wata mutuniyar Isra’ila wanda mahaifinsa mutumin Masar ne, ya je cikin Isra’ilawa, sai faɗa ta tashi tsakaninsa da wani mutumin Isra’ila a cikin sansani.
- Firistoci 24:11kusan 1490 K.H.
Ɗan mutuniyar Isra’ila ya saɓi Sunan Ubangiji, ya kuma la’ana shi, saboda haka aka kawo shi wa Musa. (Sunan mahaifiyarsa Shelomit ne, ’yar Dibri na kabilar Dan.)
- Firistoci 24:12kusan 1490 K.H.
Suka sa shi a gidan tsaro sai lokacin da nufin Ubangiji ya nuna musu abin da za su yi da shi.
- Firistoci 24:13kusan 1490 K.H.
Sai Ubangiji ya ce wa Musa,
- Firistoci 24:14kusan 1490 K.H.
“Ka kai mai saɓon nan waje da sansani. Duk waɗanda suka ji maganar da mai saɓon nan ya yi su ɗibiya hannuwansu a kansa, taron jama’a kuwa gaba ɗaya su jajjefe shi da duwatsu.
- Firistoci 24:15kusan 1490 K.H.
Faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘Duk wanda ya zagi Allahnsa, alhakin zai rataya a wuyansa,
- Firistoci 24:16kusan 1490 K.H.
duk wanda ya saɓi sunan Ubangiji, dole a kashe shi. Dole jama’a gaba ɗaya su jajjefe shi da duwatsu. Ko baƙo, ko haifaffen ɗan ƙasa, sa’ad da ya saɓi Sunan Ubangiji, dole a kashe shi.
- Firistoci 24:17kusan 1490 K.H.
“ ‘Duk wanda ya kashe mutum, dole a kashe shi.
- Firistoci 24:18kusan 1490 K.H.
Duk wanda ya kashe dabbar wani, dole yă biya, rai domin rai.
- Firistoci 24:19kusan 1490 K.H.
Duk wanda ya yi wa maƙwabcinsa rauni, sai a yi masa abin da ya yi;
- Firistoci 24:20kusan 1490 K.H.
karaya don karaya, ido don ido, haƙori don haƙori. Kamar yadda ya yi wa wani rauni, shi ma a yi masa.
- Firistoci 24:21kusan 1490 K.H.
Duk wanda ya kashe dabba, dole yă biya, amma duk wanda ya kashe mutum, dole a kashe shi.
- Firistoci 24:22kusan 1490 K.H.
Za ku kasance da doka iri ɗaya wa baƙo da kuma wa haifaffen ɗan ƙasa. Ni ne Ubangiji Allahnku.’ ”
- Firistoci 24:23kusan 1490 K.H.
Sai Musa ya yi wa Isra’ilawa magana, suka kuwa kai mai saɓon waje da sansani, suka jajjefi shi da duwatsu. Isra’ilawa suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa.
- Firistoci 25:1kusan 1491 K.H.
Ubangiji ya yi magana da Musa a kan Dutsen Sinai ya ce,
- Firistoci 25:2kusan 1491 K.H.
“Yi wa Isra’ilawa magana, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka shiga ƙasar da zan ba ku, dole ƙasar kanta ta kiyaye Asabbaci ga Ubangiji.
- Firistoci 25:3kusan 1491 K.H.
Shekara shida, za ku yi shuki, shekara shida kuma za ku aske gonakin inabinku, ku kuma tattara hatsinsu.