- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1446 BC
Sinai & The Law
God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Firistoci 22:4kusan 1490 K.H.
“ ‘In zuriyar Haruna yana da kuturu, ko mai ɗiga, ba zai ci daga cikin tsarkakakkun abubuwa ba, sai lokacin da ya tsarkaka. Duk wanda ya taɓa wani abu marar tsarki na mamaci, ko wanda maniyyinsa yake ɗiga,
- Firistoci 22:5kusan 1490 K.H.
da duk kuma wanda ya taɓa wani abu mai rarrafe wanda yake ƙazantarwa, ko kuwa wani mutum mai ƙazanta,
- Firistoci 22:6kusan 1490 K.H.
duk mutumin da ya taɓa kowane irin abu haka, zai ƙazantu har yamma, ba kuwa zai ci daga cikin tsarkakakkun abubuwan nan ba, sai ya yi wanka tukuna.
- Firistoci 22:7kusan 1490 K.H.
Sa’ad da rana ta fāɗi, zai zama tsarkakakke, bayan wannan kuwa zai iya cin tsarkakakkun hadayu, gama abincinsa ne.
- Firistoci 22:8kusan 1490 K.H.
Kada yă ci wani abin da ya mutu mushe, ko wanda namun jeji suka yayyaga, don kada yă ƙazantar da kansa. Ni ne Ubangiji.
- Firistoci 22:9kusan 1490 K.H.
“ ‘Firistoci za su kiyaye umarnaina don kada su yi laifi su mutu saboda sun rena su. Ni ne Ubangiji, wanda ya mai da su masu tsarki.
- Firistoci 22:10kusan 1490 K.H.
“ ‘Duk wanda ba daga cikin iyalin firistoci ba, ko da yake yana zama tare da su, ko kuwa an ɗauke shi yana yin musu aiki, ba zai ci daga cikin tsarkakakkun hadayun ba.
- Firistoci 22:11kusan 1490 K.H.
Amma in firist ya sayi bawa da kuɗi, ko kuwa in an haifi bawan a gidansa, wannan bawan zai iya cin tsattsarkan abincin.
- Firistoci 22:12kusan 1490 K.H.
In ’yar firist ta auri wani da ba firist ba, ba za tă ci wani tsarkakakkun sadaka ba.
- Firistoci 22:13kusan 1490 K.H.
Amma idan ’yar firist ta zama gwauruwa ko sakakkiya, ba ta da ’ya’ya, ta kuwa dawo don tă zauna a gidan mahaifinta kamar matashiya, za tă iya cin abincin.
- Firistoci 22:14kusan 1490 K.H.
“ ‘In wani ya ci tsarkakakken abinci cikin kuskure, dole yă maido wa firist hadayar, yă kuma ƙara kashi ɗaya bisa biyar na tamanin abin.
- Firistoci 22:15kusan 1490 K.H.
Firist ɗin ba zai ƙasƙantar da tsarkakakkun hadayun da Isra’ilawa suka kawo ga Ubangiji
- Firistoci 22:16kusan 1490 K.H.
ta wurin barinsu su ci tsarkakakkun hadayu, ta yin haka su jawo wa kansu laifin da zai bukaci biya ba. Ni ne Ubangiji, wanda ya mai da ku masu tsarki.’ ”
- Firistoci 22:17kusan 1490 K.H.
Ubangiji ya ce wa Musa,
- Firistoci 22:18kusan 1490 K.H.
“Yi wa Haruna da ’ya’yansa maza da kuma dukan Isra’ilawa magana ka ce musu, ‘In waninku, ko mutumin Isra’ila, ko baƙon da yake zama a Isra’ila, ya kawo kyauta don hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, ko don yă cika alkawari, ko kuwa a matsayin hadaya ta yardar rai,
- Firistoci 22:19kusan 1490 K.H.
dole ku miƙa dabba namiji marar lahani, daga shanu, tumaki, ko awaki, domin yă zama yardajje a madadinku.
- Firistoci 22:20kusan 1490 K.H.
Kada ku kawo wani abu mai lahani, domin ba zai zama yardajje ba a madadinku.
- Firistoci 22:21kusan 1490 K.H.
Sa’ad da wani ya kawo hadaya ta salama daga garken shanu, ko na tumaki, ga Ubangiji don yă cika wani alkawari na musamman, ko hadaya ta yardar rai, dole yă zama marar lahani, ko tabo, don yă zama yardajje.
- Firistoci 22:22kusan 1490 K.H.
Kada ku miƙa wa Ubangiji dabbobi makafi, ko naƙasassu, ko masu gundumi, ko masu ɗiga, ko masu susa, ko masu kirci. Kada ku sa wani daga cikin waɗannan a bisa bagade a matsayin hadaya, gama hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.
- Firistoci 22:23kusan 1490 K.H.
Za ku iya miƙa hadaya ta yardar rai da maraƙi, ko tunkiya mai naƙasa, ko marar cikakken lafiya, amma ba za tă zama yardajje don cika alkawarin da aka yi ba.
- Firistoci 22:24kusan 1490 K.H.
Ba za ku miƙa wa Ubangiji dabbar da lunsayinta yake da ƙujewa, ko dandaƙewa, ko yagewa, ko yankewa ba.
- Firistoci 22:25kusan 1490 K.H.
Ba za ku kuma karɓi irin waɗannan dabbobi daga hannun baƙi ku miƙa su a matsayin abinci ga Allahnku ba. Ba za su zama yardajje a madadinku ba, domin sun naƙasa, suna kuma da lahani.’ ”
- Firistoci 22:26kusan 1490 K.H.
Ubangiji ya ce wa Musa,
- Firistoci 22:27kusan 1490 K.H.
“Sa’ad da aka haifi ɗan maraƙi, tunkiya, ko akuya, sai yă kasance da mahaifiyarsa kwana bakwai. Daga rana ta takwas zuwa gaba, zai zama yardajje hadaya, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.
- Firistoci 22:28kusan 1490 K.H.
Kada a yanka saniya, ko tunkiya da ɗanta rana ɗaya.