Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446 BC

Sinai & The Law

God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.

1,657 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Firistoci 21:3kusan 1490 K.H.

    ko ’yar’uwarsa da ba tă riga ta yi aure ba, wadda take dogara gare shi, da yake ba ta da miji, saboda ita zai iya ƙazantar da kansa.

  2. Firistoci 21:4kusan 1490 K.H.

    Kada yă ƙazantar da kansa saboda mutanen da suke da dangantakar da shi ta wurin aure, ta yin haka zai ƙazantar da kansa.

  3. Firistoci 21:5kusan 1490 K.H.

    “ ‘Kada firistoci su aske kansu ƙwal ko su kwakkwafe gemunsu, ko su tsattsage jikunansu.

  4. Firistoci 21:6kusan 1490 K.H.

    Dole su kasance masu tsarki ga Allahnsu, kada kuma su ɓata sunan Allahnsu. Domin sukan miƙa hadayun da aka kawo wa Ubangiji da wuta, abincin Allahnsu, saboda haka sai su kasance da tsarki.

  5. Firistoci 21:7kusan 1490 K.H.

    “ ‘Ba za su auri matan da karuwanci ya ɓata su, ko waɗanda mazansu suka sake su ba, gama firistoci masu tsarki ne ga Allahnsu.

  6. Firistoci 21:8kusan 1490 K.H.

    An ɗauke su da tsarki, domin suna miƙa abincin Allahnku. An ɗauka su masu tsarki gama Ni Ubangiji, mai tsarki ne, Ni wanda ya mai da ku masu tsarki.

  7. Firistoci 21:9kusan 1490 K.H.

    “ ‘In ’yar firist ta ɓata kanta ta wurin zama karuwa, ta kunyatar da mahaifinta ke nan; dole a ƙone ta da wuta.

  8. Firistoci 21:10kusan 1490 K.H.

    “ ‘Babban firist, wanda yake ɗaya cikin ’yan’uwansa wanda aka shafe da mai a kansa, wanda kuma aka naɗa don yă sa rigunan firistoci, kada yă bar gashin kansa buzu-buzu, ko ya kyakketa rigunansa.

  9. Firistoci 21:11kusan 1490 K.H.

    Ba zai shiga inda akwai gawa ba. Kada yă ƙazantar da kansa, ko ma ta mahaifinsa ce ko ta mahaifiyarsa.

  10. Firistoci 21:12kusan 1490 K.H.

    An keɓe shi domina, kada yă ƙazantar da kansa, kada kuwa yă ɓata Tentin Sujada ta wurin shiga gidan da gawa take, ko ta mahaifinsa, ko ta mahaifiyarsa ce. Ni ne Ubangiji.

  11. Firistoci 21:13kusan 1490 K.H.

    “ ‘Dole macen da zai aura ta kasance budurwa.

  12. Firistoci 21:14kusan 1490 K.H.

    Ba zai auri matan da mijinta ya mutu, ko macen da mijinta ya rabu da ita, ko macen da ta ɓata kanta ta wurin karuwanci ba, sai dai yă auri budurwa daga cikin mutanensa,

  13. Firistoci 21:15kusan 1490 K.H.

    don kada yă ƙazantar da ’ya’yansa a cikin mutanensa. Ni ne Ubangiji, wanda ya mai da shi mai tsarki.’ ”

  14. Firistoci 21:16kusan 1490 K.H.

    Ubangiji ya ce wa Musa,

  15. Firistoci 21:17kusan 1490 K.H.

    “Faɗa wa Haruna cewa, ‘Don tsararraki masu zuwa, kada ko ɗaya daga cikin zuriyarka, da yake da lahani yă zo kusa domin yă miƙa hadaya ta ci gare ni.

  16. Firistoci 21:18kusan 1490 K.H.

    Duk mai lahani, ko makaho, ko gurgu, ko mai naƙasa, ko mai wani lahani a jiki;

  17. Firistoci 21:19kusan 1490 K.H.

    ko mai karyayyen ƙafa, ko mai karyayyen hannu,

  18. Firistoci 21:20kusan 1490 K.H.

    ko mai ƙusumbi, ko wada, ko wanda yake da lahani a ido, ko mai cuta mai sa ƙaiƙayi, ko mai kirci, ko wanda aka daƙe, ba zai yi kusa domin yă miƙa hadaya ba.

  19. Firistoci 21:21kusan 1490 K.H.

    Ba zuriyar Haruna firist, mai lahanin da zai zo kusa don yă miƙa hadayun da aka yi ga Ubangiji da wuta. Da yake yana da lahani, ba zai zo kusa don yă miƙa abincin Allahnsa ba.

  20. Firistoci 21:22kusan 1490 K.H.

    Zai iya cin abinci mafi tsarki na Allahnsa, haka ma abinci mai tsarki;

  21. Firistoci 21:23kusan 1490 K.H.

    duk da haka saboda lahaninsa, ba zai yi kusa da labule, ko yă yi kusa da bagade don kada yă ƙazantar da wuri mai tsarkina. Ni ne Ubangiji wanda yake mai da su masu tsarki.’ ”

  22. Firistoci 21:24kusan 1490 K.H.

    Sai Musa ya faɗa wannan wa Haruna da ’ya’yansa maza da kuma dukan Isra’ilawa.

  23. Firistoci 22:1kusan 1490 K.H.

    Ubangiji ya ce wa Musa,

  24. Firistoci 22:2kusan 1490 K.H.

    “Faɗa wa Haruna da ’ya’yansa maza, su lura da tsarkakakkun abubuwan da Isra’ilawa suka keɓe gare ni da bangirma, saboda ba za su ƙazantar da sunana mai tsarki ba. Ni ne Ubangiji.

  25. Firistoci 22:3kusan 1490 K.H.

    “Faɗa musu cewa, ‘Don tsararraki masu zuwa, in wani zuriyarku ya ƙazantu, duk da haka ya kusaci tsarkakakku hadayun da Isra’ilawa suka keɓe ga Ubangiji, dole a raba wannan mutum daga gabana. Ni ne Ubangiji.