Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446 BC

Sinai & The Law

God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.

1,657 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Firistoci 17:13kusan 1490 K.H.

    “ ‘Duk wani mutumin Isra’ila ko baƙon da yake zama a cikinku wanda ya ji wa wani dabba ko tsuntsu wanda ake ci ciwo, dole yă tsiyaye jinin yă rufe shi da ƙasa,

  2. Firistoci 17:14kusan 1490 K.H.

    domin ran kowace halitta yana cikin jini. Shi ya sa na ce wa Isra’ilawa, “Kada ku ci jinin wani halitta, domin ran kowace halitta yana cikin jinin; duk wanda ya ci shi dole a fid da shi.”

  3. Firistoci 17:15kusan 1490 K.H.

    “ ‘Kowa, ko haifaffe ɗan ƙasa ko baƙo, da ya ci wani abin da aka sami a mace, ko naman jeji ya yayyage, dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma; sa’an nan zai tsarkake.

  4. Firistoci 17:16kusan 1490 K.H.

    Amma in bai wanke rigunansa ya kuma yi wanka ba, alhaki zai kasance a kansa.’ ”

  5. Firistoci 18:1kusan 1490 K.H.

    Ubangiji ya ce wa Musa,

  6. Firistoci 18:2kusan 1490 K.H.

    “Yi wa Isra’ilawa magana ka kuma faɗa musu cewa, ‘Ni ne Ubangiji Allahnku.

  7. Firistoci 18:3kusan 1490 K.H.

    Kada ku yi yadda suke yi a Masar inda da kuke zama, kuma ba a ku yi kamar yadda suke yi a ƙasar Kan’ana inda nake kawo ku ba. Kada ku yi yadda suke yin abubuwa.

  8. Firistoci 18:4kusan 1490 K.H.

    Dole ku kiyaye dokokina kuma ku lura ku bi farillaina. Ni ne Ubangiji Allahnku.

  9. Firistoci 18:5kusan 1490 K.H.

    Ku kiyaye farillaina da dokokina, gama mutumin da ya aikata waɗannan abubuwa zai rayu ta wurinsu. Ni ne Ubangiji.

  10. Firistoci 18:6kusan 1490 K.H.

    “ ‘Kada wani ya kusaci wani dangi na kusa don yă yi jima’i. Ni ne Ubangiji.

  11. Firistoci 18:7kusan 1490 K.H.

    “ ‘Kada ka ƙasƙantar da mahaifinka ta wurin kwana da mahaifiyarka. Ita mahaifiyarka ce; kada ka yi jima’i da ita.

  12. Firistoci 18:8kusan 1490 K.H.

    “ ‘Kada ka yi jima’i da matar mahaifinka, wannan zai ƙasƙantar da mahaifinka.

  13. Firistoci 18:9kusan 1490 K.H.

    “ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar’uwarka, ko ’yar mahaifinka ko ’yar mahaifiyarka, ko an haife ta a gida ɗaya da kai ko kuwa a wani wuri dabam.

  14. Firistoci 18:10kusan 1490 K.H.

    “ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar ɗanka ko ’yar ’yarka, wannan zai ƙasƙantar da kai.

  15. Firistoci 18:11kusan 1490 K.H.

    “ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar matar mahaifinka wadda aka haifa wa mahaifinka; ita ’yar’uwarka ce.

  16. Firistoci 18:12kusan 1490 K.H.

    “ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar’uwar mahaifinka, ita dangin mahaifinka ne na kusa.

  17. Firistoci 18:13kusan 1490 K.H.

    “ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar’uwar mahaifiyarka, domin ita dangin mahaifiyarka ce na kusa.

  18. Firistoci 18:14kusan 1490 K.H.

    “ ‘Kada ka ƙasƙantar da ɗan’uwan mahaifinka ta wurin kusaci matarsa don ka yi jima’i da ita, ita bābarka ce.

  19. Firistoci 18:15kusan 1490 K.H.

    “ ‘Kada ka yi jima’i da matar ɗanka. Ita matar ɗanka ne; kada ka yi jima’i da ita.

  20. Firistoci 18:16kusan 1490 K.H.

    “ ‘Kada ka yi jima’i da matar ɗan’uwanka; wannan zai ƙasƙanta ɗan’uwanka.

  21. Firistoci 18:17kusan 1490 K.H.

    “ ‘Kada ka yi jima’i da mace da kuma ’yarta. Kada ka yi jima’i da ’yar ɗanta ko ’yar ’yarta; su danginta ne na kusa. Wannan mugun abu ne.

  22. Firistoci 18:18kusan 1490 K.H.

    “ ‘Kada ka auri ’yar’uwar matarka ta zama kishiyar matarka ka kuma yi jima’i da ita yayinda matarka tana da rai.

  23. Firistoci 18:19kusan 1490 K.H.

    “ ‘Kada ka kusaci mace don ka yi jima’i da ita a lokacin ƙazantar al’adarta.

  24. Firistoci 18:20kusan 1490 K.H.

    “ ‘Kada ka yi jima’i da matar maƙwabcinka ka ƙazantar da kanka tare da ita.

  25. Firistoci 18:21kusan 1490 K.H.

    “ ‘Kada ku ba da wani daga cikin ’ya’yanku don a yi hadaya wa Molek, gama ba za ku ƙasƙantar da sunan Allahnku ba. Ni ne Ubangiji.