Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446 BC

Sinai & The Law

God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.

1,657 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Firistoci 18:22kusan 1490 K.H.

    “ ‘Kada ka kwana da namiji kamar yadda namiji yakan kwana da ta mace, wannan abin ƙyama ne.

  2. Firistoci 18:23kusan 1490 K.H.

    “ ‘Kada ka yi jima’i da dabba ka ƙazantar da kanka. Mace ba za tă ba da kanta ga dabba don yă yi jima’i da ita ba; wannan abin ƙyama ne.

  3. Firistoci 18:24kusan 1490 K.H.

    “ ‘Kada ku ƙazantar da kanku da wani daga cikin waɗannan, domin haka al’umman da zan kora a gabanku suka ƙazantu.

  4. Firistoci 18:25kusan 1490 K.H.

    Har ƙasar ma ta ƙazantu, saboda haka na hukunta ta saboda zunubinta, ƙasar kuwa ta amayar da mazaunanta.

  5. Firistoci 18:26kusan 1490 K.H.

    Amma dole ku kiyaye farillaina da kuma dokokina. Kada haifaffe ɗan ƙasa da baƙin da suke zama a cikinku yă yi wani daga cikin waɗannan abubuwa banƙyama,

  6. Firistoci 18:27kusan 1490 K.H.

    gama mutanen da suka zauna a wannan ƙasa kafin ku sun aikata dukan waɗannan abubuwa, suka kuma ƙazantu.

  7. Firistoci 18:28kusan 1490 K.H.

    Kuma in kuka ƙazantar da ƙasar, za tă amayar da ku kamar yadda ta amayar da al’umman da suka riga ku.

  8. Firistoci 18:29kusan 1490 K.H.

    “ ‘Duk wanda ya yi wani daga cikin waɗannan abubuwa banƙyama, dole a fid da mutumin daga cikin mutanensa.

  9. Firistoci 18:30kusan 1490 K.H.

    Ku kiyaye umarnaina kuma kada yi ku wata al’ada mai banƙyamar da aka yi kafin ku zo kuma kada ku ƙazantar da kanku da su. Ni ne Ubangiji Allahnku.’ ”

  10. Firistoci 19:1kusan 1490 K.H.

    Ubangiji ya ce wa Musa,

  11. Firistoci 19:2kusan 1490 K.H.

    “Yi wa taron jama’ar Isra’ila gaba ɗaya magana, ka ce musu, ‘Ku zama masu tsarki, domin Ni, Ubangiji Allahnku, mai tsarki ne.

  12. Firistoci 19:3kusan 1490 K.H.

    “ ‘Dole kowannenku yă girmama mahaifiyarsa da mahaifinsa, dole kuma ku kiyaye Asabbacina. Ni ne Ubangiji Allahnku.

  13. Firistoci 19:4kusan 1490 K.H.

    “ ‘Kada ku juyo ga gumaka, ko ku yi wa kanku allolin da aka yi zubi da ƙarfe. Ni ne Ubangiji Allahnku.

  14. Firistoci 19:5kusan 1490 K.H.

    “ ‘Sa’ad da kuka miƙa hadaya ta salama ga Ubangiji, ku miƙa ta yadda za tă karɓu a madadinku.

  15. Firistoci 19:6kusan 1490 K.H.

    Za a ci ta a ranar da kuka miƙa ta, ko kuwa a kashegarin; duk abin da ya rage har kwana ta uku dole a ƙone shi.

  16. Firistoci 19:7kusan 1490 K.H.

    In aka ci ta a rana ta uku, marar tsabta ce, ba kuma za a karɓe ta ba.

  17. Firistoci 19:8kusan 1490 K.H.

    Duk wanda ya ci ta zai zama da laifi domin ya ƙazantar da abin da yake da tsarki ga Ubangiji, dole a raba mutumin nan da mutanensa.

  18. Firistoci 19:9kusan 1490 K.H.

    “ ‘Sa’ad da kuka yi girbin amfanin gonarku, kada ku girbe har zuwa gefen gonar, ko ku yi kalan girbinku.

  19. Firistoci 19:10kusan 1490 K.H.

    Kada ku koma gonar inabinku kuna kala, ko ku tattara ’ya’yan inabin da suka fāffāɗi. Ku bar su domin matalauta da kuma baƙi. Ni ne Ubangiji Allahnku.

  20. Firistoci 19:11kusan 1490 K.H.

    “ ‘Kada ku yi sata. “ ‘Kada ku yi ƙarya. “ ‘Kada ku ruɗe juna.

  21. Firistoci 19:12kusan 1490 K.H.

    “ ‘Kada ku rantse bisa ƙarya da sunana, ta haka har ku ƙasƙantar da sunan Allahnku. Ni ne Ubangiji.

  22. Firistoci 19:13kusan 1490 K.H.

    “ ‘Kada ku zalunci maƙwabcinku, ko ku yi masa ƙwace. “ ‘Kada ku riƙe albashin ma’aikaci yă kwana.

  23. Firistoci 19:14kusan 1490 K.H.

    “ ‘Kada ku zagi kurma, ko ku sa abin tuntuɓe a gaban makaho, amma ku ji tsoron Allahnku. Ni ne Ubangiji.

  24. Firistoci 19:15kusan 1490 K.H.

    “ ‘Kada ku yi rashin adalci cikin shari’a; kada ku nuna sonkai ga matalauci, ko ku goyi bayan mai arziki, amma ku shari’anta maƙwabci cikin gaskiya.

  25. Firistoci 19:16kusan 1490 K.H.

    “ ‘Kada ku yi ta yawo kuna yaɗa ƙarya a cikin mutanenku. “ ‘Kada ku yi wani abin da zai sa ran maƙwabcinku cikin hatsari. Ni ne Ubangiji.