Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 48–96

Letters to the Churches

Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.

2,767 ayoyi · 21 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Romawa 9:26kusan 60 M.

    kuma, “Zai zama cewa a daidai inda aka ce musu, ‘Ku ba mutanena ba,’ za a ce da su, ‘’ya’yan Allah mai rai.’ ”

  2. Romawa 9:27kusan 60 M.

    Ishaya ya ɗaga murya game da Isra’ila ya ce, “Ko da yake yawan Isra’ilawa yana kama da yashi a bakin teku, ragowa ce kaɗai za su sami ceto.

  3. Romawa 9:28kusan 60 M.

    Gama Ubangiji zai zartar da hukuncinsa a bisan duniya da sauri kuma ba da ɓata lokaci ba.”

  4. Romawa 9:29kusan 60 M.

    Yana nan kamar yadda Ishaya ya riga ya faɗa. “Da ba don Ubangiji Maɗaukaki ya bar mana zuriya ba, da mun zama kamar Sodom, da mun kuma zama kamar Gomorra.”

  5. Romawa 9:30kusan 60 M.

    Me za mu ce ke nan? Ai, Al’ummai da ba su nemi adalci ba, sun same shi, adalcin da yake ta wurin bangaskiya;

  6. Romawa 9:31kusan 60 M.

    amma Isra’ila da suka yi ƙwazo wajen bin Dokar adalci, ba su same shi ba.

  7. Romawa 9:32kusan 60 M.

    Don me? Domin sun yi ƙwazo wajen binta ba ta wurin bangaskiya ba sai dai ta wurin ayyuka. Sun yi tuntuɓe a kan “dutsen sa tuntuɓe.”

  8. Romawa 9:33kusan 60 M.

    Kamar yadda yake a rubuce, “Ga shi, na sa dutse a Sihiyona da yake sa mutane yin tuntuɓe da kuma dutsen da yake sa su fāɗi wanda kuwa ya dogara gare shi ba zai taɓa shan kunya ba.”

  9. Romawa 10:1kusan 60 M.

    ’Yan’uwa, abin da zuciyata take so da kuma addu’ata ga Allah saboda Isra’ilawa shi ne su sami ceto.

  10. Romawa 10:2kusan 60 M.

    Gama na shaida su a kan suna da kishi bin Allah, sai dai kishinsu ba a bisa sani ba.

  11. Romawa 10:3kusan 60 M.

    Da yake ba su san adalcin da yake fitowa daga Allah ba suka kuma nemi su kafa nasu, sai suka ƙi miƙa kai ga adalcin Allah.

  12. Romawa 10:4kusan 60 M.

    Kiristi shi ne ƙarshen doka domin a sami adalci wa kowane mai bangaskiya.

  13. Romawa 10:5kusan 60 M.

    Musa ya bayyana adalcin da yake ga Doka cewa, “Mutumin da ya aikata waɗannan abubuwa zai rayu ta wurinsu.”

  14. Romawa 10:6kusan 60 M.

    Amma adalcin da yake ga bangaskiya yana cewa, “Kada ka faɗa a zuciyarka, ‘Wa zai hau sama?’ ” (wato, don yă sauko da Kiristi),

  15. Romawa 10:7kusan 60 M.

    “ko kuwa ‘Wa zai gangara can zurfin ƙasa?’ ” (wato, don yă hauro da Kiristi daga matattu).

  16. Romawa 10:8kusan 60 M.

    Amma mene ne aka ce? “Maganar tana kusa da kai; tana cikin bakinka da kuma cikin zuciyarka,” wato, maganar bangaskiyan nan da muke shela.

  17. Romawa 10:9kusan 60 M.

    Cewa in ka furta da bakinka, “Yesu Ubangiji ne,” ka kuma gaskata a zuciyarka cewa Allah ya tā da shi daga matattu, za ka sami ceto.

  18. Romawa 10:10kusan 60 M.

    Gama da zuciyarka ce kakan gaskata a kuma kuɓutar da kai, da bakinka ne kuma kake furta a kuma cece ka.

  19. Romawa 10:11kusan 60 M.

    Kamar yadda Nassi ya ce, “Duk wanda ya gaskata da shi ba zai taɓa shan kunya ba.”

  20. Romawa 10:12kusan 60 M.

    Gama ba bambanci tsakanin mutumin Yahuda da mutumin Al’ummai, Ubangijin nan ɗaya shi ne Ubangijin kowa yana kuma ba da albarka a yalwace ga duk masu kira gare shi,

  21. Romawa 10:13kusan 60 M.

    gama, “Duk wanda ya kira bisa sunan Ubangiji zai sami ceto.”

  22. Romawa 10:14kusan 60 M.

    To, ta yaya za su kira ga wanda ba su gaskata ba? Ta yaya kuma za su gaskata wanda ba su taɓa ji ba? Ta yaya kuma za su ji ba tare da wani ya yi musu wa’azi ba?

  23. Romawa 10:15kusan 60 M.

    Kuma ta yaya za su yi wa’azi in ba an aike su ba? Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Isowar masu kawo labari mai daɗi abu mai kyau ne ƙwarai!”

  24. Romawa 10:16kusan 60 M.

    Amma ba dukan Isra’ilawa ne suka karɓi labari mai daɗin nan ba. Gama Ishaya ya ce, “Ubangiji, wa ya gaskata saƙonmu?”

  25. Romawa 10:17kusan 60 M.

    Saboda haka, bangaskiya takan zo ne ta wurin jin saƙo, akan ji saƙon kuma ta wurin maganar Kiristi.