Tsallake zuwa abun ciki

Sarah

48 ayoyi · 5 'yan gida

An kuma san shi da: Sarai, Sara

Ayoyin da suka ambaci Sarah

Tace bisa littafi
  1. Sai Abimelek ya kawo awaki da shanu da bayi maza da mata, ya ba wa Ibrahim, ya kuma komar da Saratu matarsa gare shi.

  2. Ga Saratu kuwa ya ce, “Ina ba wa ɗan’uwanki shekel dubu na azurfa, shaida ce ta tabbatarwa a idanun dukan waɗanda suke tare da ke, da kuma a gaban kowa cewa ba ki da laifi.”

  3. gama Ubangiji ya rufe kowace mahaifa a gidan Abimelek saboda Saratu, matar Ibrahim.

  4. Ana nan sai Ubangiji ya nuna wa Saratu alheri kamar yadda ya ce, Ubangiji kuma ya yi wa Saratu abin da ya yi alkawari.

  5. Saratu ta yi ciki, ta kuma haifa wa Ibrahim ɗa a tsufansa; a daidai lokacin da Allah ya yi masa alkawari.

  6. Ibrahim ya sa wa ɗan da Saratu ta haifa masa suna Ishaku.

  7. Saratu ta ce, “Allah ya sa na yi dariya, kuma duk wanda ya ji game da wannan, zai yi dariya tare da ni.”

  8. Ta kuma ƙara da cewa, “Dā, wa zai iya ce wa Ibrahim, Saratu za tă yi renon yara? Duk da haka na haifar masa ɗa cikin tsufansa.”

  9. Amma Saratu ta ga cewa yaron da Hagar, mutuniyar Masar ta haifa wa Ibrahim yana wa ɗanta Ishaku gori,

  10. Amma Allah ya ce wa Ibrahim, “Kada hankalinka yă tashi game da yaron nan da kuma baiwarka. Ka saurari duk abin da Saratu ta faɗa maka, saboda ta wurin Ishaku ne za a lissafta zuriyarka.

  11. Saratu ta yi shekara ɗari da ashirin da bakwai a duniya.

  12. Ta rasu a Kiriyat Arba (wato, Hebron) a ƙasar Kan’ana, Ibrahim kuwa ya tafi ya yi makokin Saratu, yana kuka saboda ita.

  13. Bayan wannan Ibrahim ya binne matarsa Saratu a kogon a filin Makfela kusa da Mamre (wanda yake a Hebron) a ƙasar Kan’ana.

  14. Saratu matar maigidana ta haifa masa ɗa a tsufanta, ya kuma ba shi duk mallakarsa.

  15. Ishaku ya kawo ta cikin tentin mahaifiyarsa Saratu, ya kuma auri Rebeka. Ta haka ta zama matarsa, ya kuwa ƙaunace ta; Ishaku kuma ya ta’azantu bayan rasuwar mahaifiyarsa.

  16. filin da Ibrahim ya saya daga Hittiyawa. A nan aka binne Ibrahim tare da matarsa Saratu.

  17. Waɗannan su ne zuriyar Ishmayel ɗan Ibrahim, wanda Hagar mutuniyar Masar, baranyar Saratu, ta haifa wa Ibrahim.

  18. A can aka binne Ibrahim da matarsa Saratu, a can aka binne Ishaku da matarsa Rebeka, a can kuma na binne Liyatu.

  19. dubi Ibrahim, mahaifinku, da Saratu, wadda ta haife ku. Sa’ad da na kira shi kaɗai ne, na kuma albarkace shi na kuma mai da shi da yawa.

  20. Ba tare da ya bar bangaskiyarsa ta yi rauni ba, ya fuskanci gaskiyan nan mai cewa jikinsa mai tsufa matacce ne, da yake yana da shekara wajen ɗari, mahaifar Saratu kuma matacciya ce.

  21. Ga yadda aka yi alkawarin nan, “A ƙayyadadden lokaci zan dawo, Saratu kuma za tă haifi ɗa.”

  22. Ta wurin bangaskiya Ibrahim, ko da yake shekarunsa sun wuce, Saratu kanta kuma bakararriya ce ya iya zama mahaifi domin ya amince cewa shi wanda ya yi alkawarin mai aminci ne.

  23. kamar Saratu, wadda ta yi biyayya ga Ibrahim, har ta kira shi maigidanta. Ku ’ya’yanta ne mata in kun aikata abin da yake daidai, ba ku kuma ba tsoro dama ba.