Jesus
An kuma san shi da: Jesus Christ, Immanuel, Emmanuel, Christ
Ayoyin da suka ambaci Jesus
Sai Yahudawa suka ce masa, “Kai, shekarunka har yanzu ba su kai hamsin tukuna ba fa, har ka ga Ibrahim!”
Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, tun ba a haifi Ibrahim ba, ni ne!”
Da jin haka sai suka ɗebo duwatsu don su jajjefe shi, amma Yesu ya ɓuya, ya fita daga filin haikali.
Da Yesu yana tafiya, sai ya ga wani mutum wanda aka haifa makaho.
Sai almajiransa suka tambaye shi suka ce, “Rabbi, wane ne ya yi zunubi, mutumin ne, ko iyayensa, da ya sa aka haife shi makaho?”
Sai Yesu ya ce, “Ba don mutumin ko iyayensa sun yi zunubi ne ba, sai dai don a bayyana aikin Allah ne a rayuwarsa.
Muddin da sauran rana, dole mu yi aikin wanda ya aiko ni. Dare yana zuwa, sa’ad da ba wanda zai iya yin aiki.
Yayinda ina a cikin duniya, ni ne hasken duniya.”
Bayan ya faɗi haka, sai ya tofa miyau a ƙasa, ya kwaɓa laka da miyau ɗin, ya kuma shafa a idanun mutumin.
Ya ce masa, “Je ka, ka wanke a Tafkin Silowam” (kalman nan tana nufin “Aikakke”). Saboda haka mutumin ya tafi ya wanke, ya kuma dawo gida yana gani.
Waɗansu suka ce shi mana. Waɗansu kuwa suka ce, “A’a, ya dai yi kama da shi.” Amma shi ɗin ya ce, “Ƙwarai kuwa ni ne.”
Ya amsa ya ce, “Mutumin da ake kira Yesu ne ya kwaɓa laka ya shafa mini a idanu. Ya ce mini in je Silowam in wanke. Na kuwa tafi, na wanke, sai na sami ganin gari.”
Suka tambaye shi suka ce, “Ina mutumin yake?” Ya ce, “Ban sani ba.”
To, a ranar da Yesu ya kwaɓa laka ya buɗe idanun mutumin ranar Asabbaci ce.
Sai waɗansu daga cikin Farisiyawa suka ce, “Mutumin nan ba daga Allah yake ba, don ba ya kiyaye ranar Asabbaci.” Amma waɗansu suka yi tambaya suka ce, “Yaya mutum mai zunubi zai yi irin abubuwan banmamaki haka?” Sai ra’ayinsu ya sha bamban.
A ƙarshe suka sāke koma ga makahon suka ce, “Kai fa, me ka gani game da shi? Idanunka ne fa ya buɗe.” Sai mutumin ya ce, “Tab, ai, shi annabi ne.”
Iyayensa sun faɗa haka ne saboda suna tsoron Yahudawa, gama Yahudawa sun riga sun yanke shawara cewa duk wanda ya yarda cewa Yesu shi ne Kiristi, za a kore shi daga majami’a.
Sai suka sāke kiran mutumin nan da yake makaho a dā, suka ce masa, “Ka ɗaukaka Allah, mu kam, mun san mutumin nan mai zunubi ne.”
Sai ya amsa ya ce, “Ko shi mai zunubi ne ko babu, ni dai ban sani ba. Abu ɗaya fa na sani, dā ni makaho ne, amma yanzu ina gani!”
Sai suka tambaye suka ce, “Shin, me ya yi maka? Ta yaya ya buɗe idanunka?”
Ya amsa ya ce, “Na riga na gaya muku ba ku kuwa saurara ba. Don me kuke so ku sāke ji? Ko ku ma kuna so ku zama almajiransa ne?”
Sai suka hau shi da zagi suna cewa, “Kai ne dai almajirin mutumin! Mu almajiran Musa ne!
Mun dai san cewa Allah ya yi magana da Musa, amma wannan mutum ba mu san inda ya fito ba.”
Sai mutumin ya ce, “Cabɗi, yau ga abin mamaki! Ba ku san inda ya fito ba, ga shi kuwa ya buɗe idanuna.
Da mutumin nan ba daga Allah ba ne, da ba abin da zai iya yi.”