Jesus
An kuma san shi da: Jesus Christ, Immanuel, Emmanuel, Christ
Ayoyin da suka ambaci Jesus
Yesu ya ji labari cewa sun kore shi, da ya same shi kuwa, sai ya ce, “Ka gaskata da Ɗan Mutum?”
Sai mutumin ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, wane ne shi? Gaya mini, don in gaskata da shi.”
Yesu ya ce, “Yanzu ka gan shi; tabbatacce ma, shi ne yake magana da kai.”
Sai mutumin ya ce, “Ubangiji, na gaskata,” ya kuma yi masa sujada.
Yesu ya ce, “Saboda shari’a ce na zo duniya nan, saboda makafi su sami ganin gari, waɗanda suke gani kuma su makance.”
Da Farisiyawan da suke tare da shi suka ji ya faɗi haka sai suka yi tambaya suka ce, “Mene? Mu ma makafi ne?”
Yesu ya ce, “Ai, da ku makafi ne ma, da ba ku da zunubi, amma da yake kun ce, kuna gani, zunubanku suna nan daram.
“Gaskiya nake gaya muku, mutumin da bai shiga inda ake ajiye garken tumaki ta ƙofa ba, amma ya hau ta katanga, ɓarawo ne, ɗan fashi kuma.
Yesu ya yi musu wannan misali, amma ba su fahimci abin da yake faɗa musu ba.
Saboda haka Yesu ya sāke cewa, “Gaskiya nake gaya muku, ni ne ƙofar tumakin.
Duk waɗanda suka riga ni zuwa ɓarayi ne, ’yan fashi kuma, amma tumakin ba su saurare su ba.
Ni ne ƙofar; duk wanda ya shiga ta wurina zai sami ceto. Zai riƙa shiga yă fita yă kuwa sami wurin kiwo.
Ɓarawo yakan zo don yă yi sata ne kawai da kisa da kuma ɓarna. Ni kuwa na zo ne don su sami rai, su kuma same shi a yalwace.
“Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau yakan ba da ransa domin tumakin.
“Ni ne makiyayi mai kyau; na san tumakina, tumakina kuma sun san ni,
kamar yadda Uba ya san ni, ni kuma na san Uba, ina kuwa ba da raina domin tumakin.
Ina da waɗansu tumaki da ba na wannan garken ba ne. Dole ne in kawo su su ma. Za su saurari muryata, za su kasance garke guda ɗaya, makiyayi guda kuma.
Abin da ya sa Ubana yake ƙaunata ke nan, domin ina ba da raina, in ɗauko shi kuma.
Ba mai karɓe mini rai, ina dai ba da shi. Ina da iko in ba da shi, ina da iko in ɗauko shi kuma. Wannan umarni kuwa daga wurin Ubana na karɓo shi.”
Da yawa daga cikinsu suka ce, “Yana da aljani, yana kuma hauka. Don me za ku saurare shi?”
Sai ga Yesu a filin haikali yana zagawa a Shirayin Solomon,
sai Yahudawa suka taru kewaye da shi, suka ce masa, “Har yaushe za ka bar mu da shakka? In kai ne Kiristin, ka faɗa mana a fili mana.”
Yesu ya amsa ya ce, “Na faɗa muku, amma ba ku gaskata ba. Ayyukan da nake yi cikin sunan Ubana su suke nuna ko wane ne ni.
Amma ba ku gaskata ba domin ku ba tumakina ba ne.
Tumakina sukan saurari muryata; na sansu, suna kuma bi na.