Jesus
An kuma san shi da: Jesus Christ, Immanuel, Emmanuel, Christ
Ayoyin da suka ambaci Jesus
Yesu ya yi tambaya, “Wa ya taɓa ni?” Bayan kowa ya yi musu, sai Bitrus ya ce, “Ubangiji, ai, mutane da yawa suna matsinka ta kowane gefe.”
Amma Yesu ya ce, “Wani ya taɓa ni, na san cewa iko ya fita daga wurina.”
Sai macen, da ta ga ba halin ɓoyewa, sai ta fita, jikinta na rawa, ta fāɗi a gabansa. A gaban dukan mutanen, ta faɗi dalilin da ya sa ta taɓa shi, da yadda ta warke nan take.
Sai Yesu ya ce mata, “Diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya.”
Yayinda Yesu na cikin magana har yanzu, sai ga wani daga gidan Yayirus, mai mulkin majami’ar ya ce, “Kada ka ƙara damun malam, diyarka ta rasu.”
Da Yesu ya ji wannan, sai ya ce wa Yayirus, “Kada ka ji tsoro, ka gaskata, za a kuma warkar da ita.”
Da ya iso gidan Yayirus, sai ya hana kowa yă bi shi cikin ɗakin, sai dai Bitrus, da Yohanna, da Yaƙub, da kuma mahaifin da mahaifiyar.
Ana cikin haka, dukan mutanen kuma sai kuka da makoki suke ta yi, domin yarinyar. Sai Yesu ya ce, “Ka daina yin kuka, ba tă mutu ba, tana barci ne.”
Sai suka yi masa dariya, da yake sun san cewa, ta mutu.
Amma Yesu ya kama ta a hannu ya ce, “Diyata, tashi.”
Ruhunta ya dawo, kuma ta tashi, nan take. Yesu ya ce musu, su ba ta wani abu tă ci.
Iyayenta suka yi mamaki, amma ya ba su umarni kada su faɗa wa kowa abin da ya faru.
Bayan da Yesu ya tara Sha Biyun wuri ɗaya, sai ya ba su iko da izini na fitar da dukan aljanu, da na warkar da cututtuka.
Ya kuma aike su, su yi wa’azin mulkin Allah, su kuma warkar da marasa lafiya.
Ya ce musu, “Kada ku ɗauki kome don tafiyar, wato, ba sanda, ba jaka, ba burodi, ba kuɗi, ba riga na biyu.
Yanzu fa, Hiridus mai sarauta ya ji labarin dukan abubuwan da suke faruwa. Sai ya rikice, don waɗansu mutane suna cewa, Yohanna Mai Baftisma ne ya tashi daga matattu,
Amma Hiridus ya ce, “Yohanna dai na yanke kansa, amma wanne mutum ne nake jin labarin abubuwan nan a kansa?” Sai ya yi ƙoƙari ya ga Yesu.
Da manzannin suka dawo, sai suka faɗa wa Yesu abin da suka yi. Sai ya ɗauke su, suka keɓe kansu su kaɗai, zuwa wani gari da ake kira Betsaida.
Amma taron mutane suka ji labari, sai suka bi shi. Ya marabce su, kuma ya yi musu magana a kan mulkin Allah, ya kuma warkar da masu bukatar warkarwa.
Da rana ta kusa fāɗuwa, sai Sha Biyun suka zo wurinsa, suka ce, “Ka sallami taron domin su shiga ƙauyuka na kewaye, su nemi abin da za su ci, da wurin kwana, don inda muke, ba kowa.”
Yesu ya ce, “Ku, ku ba su wani abu su ci.” Sai suka ce masa, “Muna da burodi biyar da kifi biyu kaɗai. Sai dai, in mun je mu sayi abinci domin dukan wannan taron.”
Maza kaɗai sun kai kusan dubu biyar. Amma ya ce wa almajiransa, “Ku sa su su zauna a ƙungiya hamsin-hamsin.”
Sai Yesu ya ɗauki burodin biyar da kifin biyun, ya ɗaga kansa sama, ya yi godiya, ya kuma kakkarya su. Ya ba wa almajiransa, domin su rarraba wa mutanen.
Wata rana sa’ad da Yesu yana addu’a a ɓoye, almajiransa kuma suna tare da shi, sai ya tambaye, su ya ce, “Wa, taron mutane ke ce da ni?”
“Amma ku fa, wa, kuke ce da ni?” Bitrus ya amsa ya ce, “Kiristi na Allah.”