Tsallake zuwa abun ciki

Holy Spirit

251 ayoyi

An kuma san shi da: Spirit

Ayoyin da suka ambaci Holy Spirit

Tace bisa littafi
  1. Yanzu da kuka tsarkake kanku ta wurin yin biyayya ga gaskiyan nan, don ku kasance da ƙauna mai gaskiya wa ’yan’uwanku, sai ku ƙaunaci juna ƙwarai, daga zuciya.

  2. Gama Kiristi ya mutu domin zunubi sau ɗaya tak, mai adalci saboda marasa adalci, don yă kawo ku ga Allah. An kashe shi a cikin jiki, amma an rayar da shi a Ruhu,

  3. Gama annabci bai taɓa samo tushensa daga nufin mutum ba, sai dai mutane sun yi magana daga Allah yayinda Ruhu Mai Tsarki ya bishe su.

  4. Waɗanda suke biyayya da umarnansa kuwa suna rayuwa a cikinsa, shi kuma a cikinsu. Ta haka muka san cewa yana raye a cikinmu. Mun san haka ta wurin Ruhun da ya ba mu.

  5. Ga yadda za ku gane Ruhun Allah, duk ruhun da ya yarda cewa Yesu Kiristi ya zo cikin jiki, to, daga Allah yake.

  6. Mun san cewa muna rayuwa a cikinsa shi kuma a cikinmu, domin ya ba mu Ruhunsa.

  7. Ga wanda ya zo ta wurin ruwa da jini, wato, Yesu Kiristi. Bai zo ta wurin ruwa kaɗai ba, sai dai ta wurin ruwa da kuma jini. Ruhu ne kuwa yake ba da shaida, gama Ruhu shi ne gaskiya.

  8. Akwai shaidu uku, wato,

  9. Ruhu, da ruwa, da kuma jini; waɗannan uku kuwa manufarsu ɗaya ce.

  10. Waɗannan mutanen ne, suke kawo rabe-rabe, masu bin abin da jiki yake so, marasa Ruhu.

  11. Amma ku, abokaina ƙaunatattu, ku gina kanku cikin bangaskiyarku mafi tsarki, ku kuma yi addu’a cikin Ruhu Mai Tsarki.

  12. Daga Yohanna, Zuwa ga ikkilisiyoyi bakwai da suke a lardin Asiya. Alheri da salama gare ku daga shi wanda yake a yanzu, wanda yake a dā, da kuma wanda zai zo, da kuma daga ruhohi bakwai da suke a gaban kursiyinsa,

  13. A Ranar Ubangiji ina cikin Ruhu, sai na ji a bayana wata babbar murya kamar ƙaho,

  14. Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ikon ci daga itacen rai, da yake cikin aljannar Allah.

  15. Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara mutuwa ta biyu ba za tă cuce shi ba ko kaɗan.

  16. Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara zan ba shi kaɗan daga cikin ɓoyayyiyar Manna. Zan kuma ba shi farin dutse tare da sabon suna a rubuce a bisansa, sananne kawai ga mai karɓan dutsen.

  17. Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi.

  18. “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Sardis, ka rubuta, Waɗannan su ne kalmomi, na wanda yake riƙe da ruhohi bakwai na Allah da kuma taurari bakwai. Na san ayyukanka; ana ganinka kamar rayayye, amma kai matacce ne.

  19. Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi.

  20. Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi.

  21. Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi.”

  22. Daga kursiyin hasken walƙiya yana ta fitowa, da ƙararraki da kuma tsawa. A gaban kursiyin, fitilu bakwai suna ci. Waɗannan ne ruhohi bakwai na Allah.

  23. Sa’an nan na ga Ɗan Rago, yana kamar an yanka, tsaye a tsakiyar kursiyin, halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan an sun kewaye shi. Yana da ƙahoni bakwai da idanu bakwai, waɗanda suke ruhohi bakwai na Allah da aka aika cikin dukan duniya.

  24. Amma bayan kwana uku da rabi ɗin numfashin rai daga Allah ya shige su, suka kuwa tashi tsaye, tsoro kuma ya kama waɗanda suka gan su.

  25. Sai na ji murya daga sama ta ce, “Rubuta, Masu albarka ne matattun da suka mutu cikin Ubangiji daga yanzu zuwa gaba.” “I, za su huta daga faman aikinsu, gama ayyukansu za su bi su,” in ji Ruhu.