God
Ayoyin da suka ambaci God
Amma in mutumin da yake da tsarki bai kuma yi tafiya ba, ya kuwa ƙi yă yi Bikin Ƙetarewar, dole a ware wannan mutum daga mutanensa, domin bai miƙa hadaya ga Ubangiji a ƙayyadadden lokaci ba. Wannan mutum zai ɗauki alhakin zunubinsa.
“ ‘Baƙon da yake zaune a cikinku wanda yake so yă yi Bikin Ƙetarewar Ubangiji, dole yă yi shi bisa ga dokokinsa da ƙa’idodinsa. Dole ku kasance da ƙa’ida ɗaya ga baƙo da kuma ɗan ƙasa.’ ”
Da umarnin Ubangiji, Isra’ilawa suke tashi. Da umarninsa kuma suke sauka. Muddin girgijen yana tsaye a bisa tabanakul, sukan yi ta zamansu a sansanoni.
Sa’ad da girgijen ya ci gaba da kasancewa a bisan tabanakul na dogon lokaci, Isra’ilawa sukan bi umarnin Ubangiji, ba kuwa za su tashi ba.
Wani lokaci girgijen yakan yi ’yan kwanaki ne kawai a bisa tabanakul; da umarnin Ubangiji sukan kafa sansani da umarninsa kuma su tashi.
Da umarnin Ubangiji sukan kafa sansani, da umarninsa kuma sukan tashi. Sukan bi umarnin Ubangiji, bisa ga umarninsa ta wurin Musa.
Ubangiji ya ce wa Musa,
Duk lokacin da za ku tafi yaƙi a ƙasarku, in akwai waɗansu da suke matsa muku, za ku yi amfani da waɗannan kakaki ta wurin hura su, alama ce, cewa za a je yaƙi. Sa’an nan Ubangiji Allahnku zai tuna da ku, yă cece ku daga maƙiyanku.
Haka ma in kuna cikin jin daɗinku, musamman lokacin da kuke bukukkuwanku, kamar Bikin Sabon Wata da dai kowane Bikinku, za ku hura waɗannan kakaki lokacin da kuke miƙa hadayunku na ƙonawa, da hadayunku na salama, za su kuma zama muku abin tunawa a gaban Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku.”
Suka kama hanya, a wannan lokaci, bisa umarnin Ubangiji, ta wurin Musa.
Sai Musa ya ce wa Hobab ɗan Reyuwel Bamidiyane surukinsa, “Yanzu fa, muna shirin tashi ne daga nan, domin mu tafi inda Ubangiji ya ce, ‘Zan ba ku.’ Ka zo tare da mu, za mu kuwa yi maka alheri, gama Ubangiji ya yi wa Isra’ilawa alkawari abubuwa masu kyau.”
In ka zo tare da mu, za mu raba duk abin alherin Ubangiji ya ba mu tare da kai.”
Saboda haka suka kama hanya daga dutsen Ubangiji, suka yi tafiya kwana uku. Akwatin alkawarin Ubangiji ya ja gabansu a waɗannan kwanaki uku, don yă samo musu masauƙi.
A duk lokacin da suka tashi daga sansani, girgijen Ubangiji ya inuwantar da su da rana.
Duk kuma sa’ad da akwatin ya kama hanya, sai Musa ya ce, “Ka tashi, ya Ubangiji! Ka sa maƙiyanka su warwatse; masu ƙinka kuma su gudu a gabanka.”
Duk sa’ad da akwatin ya sauka kuma, sai Musa ya ce, “Ka komo, ya Ubangiji, a wurin dubban da ba a iya ƙidayawa na iyalan Isra’ila.”
Da Ubangiji ya ji gunagunin da mutanen suke yi saboda wahalarsu, sai ya husata ƙwarai. Sai wuta daga Ubangiji ta yi ta ci a cikinsu har ta ƙone waɗansu wurare na sansanin.
Da jama’ar suka yi wa Musa kuka, sai ya yi addu’a ga Ubangiji, wutar kuwa ta mutu.
Saboda haka aka kira wannan wuri Tabera, gama a wurin ne wuta daga Ubangiji ta ƙuna a cikinsu.
Musa ya ji mutanen suna ta gunaguni ko’ina a cikin iyalansu, kowane mutum a ƙofar tentinsa. Ubangiji kuwa ya husata ƙwarai, sai Musa ya damu.
Sai ya ce wa Ubangiji, “Me ya sa ka kawo wannan damuwar a kan bawanka? Me na yi da ya ɓata maka rai har ka ɗora dukan nauyin mutanen nan a kaina?
Ni ne na yi cikin dukan mutanen nan? Ni ne na haife su? To, me ya sa ka ce in ɗauke su a ƙirjina kamar yadda mai reno yake rungume jariri, zuwa ƙasa wadda ka yi alkawari da rantsuwa za ka ba wa kakanninsu?
In haka za ka yi da ni, ka kashe ni yanzu, in na sami tagomashi daga gare ka, kada ka bar ni in rayu in ga wannan baƙin ciki.”
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka tattaro mini dattawa saba’in daga cikin mutanen Isra’ila, waɗanda aka sani su ne dattawa da kuma shugabanni a cikin jama’a. Ka sa su zo Tentin Sujada, su tsaya a can tare da kai.
Zan sauko in yi magana da kai a can, zan kuma ɗauki Ruhun da yake kanka in mai da shi wajensu. Za su taimake ka ɗaukan nauyin mutane, don yă zama ba kai kaɗai ba ne mai ɗaukan kaya.