Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Waɗannan su ne waɗanda ba su ƙazantar da kansu da mata ba, gama sun kiyaye kansu da tsarki. Suna bin Ɗan Ragon duk inda ya tafi. Su ne aka saya daga cikin mutane aka kuwa miƙa su kamar ’ya’yan fari ga Allah da kuma Ɗan Ragon.

  2. Ba a sami ƙarya a bakunansu ba; su kuma marasa aibi ne.

  3. Ya ce da babbar murya, “Ku ji tsoron Allah ku kuma ɗaukaka shi, domin sa’ar hukuncinsa ya yi. Ku yi wa wannan da ya halicci sammai, ƙasa, teku, da maɓulɓulan ruwa sujada.”

  4. shi ma zai sha ruwan inabin fushin Allah, wanda aka zuba da duk ƙarfinsa a kwaf fushinsa. Za a ba shi azaba da farar wuta mai ci a gaban tsarkakan mala’iku da na Ɗan Ragon.

  5. Wannan yana bukata haƙuri, a gefen tsarkakan da suke biyayya da umarnan Allah suka kuma kasance da aminci ga Yesu.

  6. Mala’ikan ya wurga laujensa a duniya, ya tattara ’ya’yan inabin, ya kuma zuba su cikin babbar wurin matsewar inabin fushin Allah.

  7. Na ga wata babbar alama mai banmamaki a sama, mala’iku bakwai da annobai bakwai na ƙarshe, na ƙarshe, domin da su ne fushin Allah ya cika.

  8. Sai na ga abin da ya yi kamar tekun gilashi gauraye da wuta kuma tsaye kusa da teku, waɗanda suka ci nasara bisan dabbar da siffarta da bisan lambar sunanta. Suna riƙe da garayu waɗanda Allah ya ba su

  9. suka rera waƙar Musa bawan Allah da kuma waƙar Ɗan Ragon suna cewa, “Ayyukanka suna da girma da kuma banmamaki, ya Ubangiji Maɗaukaki. Al’amuranka suna da aminci da kuma gaskiya, ya Sarkin zamanai.

  10. Sai ɗaya daga cikin halittu huɗun nan masu rai, ya ba wa mala’iku bakwai nan kwanonin zinariya bakwai cike da fushin Allah, wanda yake raye har abada abadin.

  11. Aka kuma cika haikalin da hayaƙi daga ɗaukakar Allah da kuma daga ikonsa, kuma ba wanda ya iya shiga haikalin sai da aka cika annobai bakwai nan na mala’iku bakwai.

  12. Sai na ji wata babbar murya daga haikalin tana ce wa mala’iku bakwai nan, “Ku tafi ku zuba kwanoni bakwai nan na fushin Allah a kan duniya.”

  13. Na kuma ji bagaden ya amsa, “I, Ubangiji Allah, Maɗaukaki, hukuntanka daidai yake na adalci ne kuma.”

  14. Aka ƙone su da zafin wuta mai tsanani suka kuwa la’anci sunan Allah wanda yake da iko a kan waɗannan annoban, amma suka ƙi su tuba su kuma ɗaukaka shi.

  15. suka kuma la’anci Allah na sama saboda zafinsu, da kuma saboda gyambunansu, amma suka ƙi su tuba daga abin da suka riga suka yi.

  16. Su ruhohin aljanu ne da suke aikata abubuwan banmamaki, sukan je wurin sarakunan dukan duniya, don su tattara su don yaƙi a babbar ranar Allah Maɗaukaki.

  17. Babban birnin ya rabu kashi uku, biranen al’ummai kuma suka rurrushe. Allah ya tuna da Babilon Mai Girma ya kuma ba ta kwaf cike da ruwan inabin fushinsa.

  18. Daga sararin sama manyan ƙanƙara masu nauyin gaske suka fāɗo a kan mutane. Suka kuma la’anci Allah saboda annobar ƙanƙarar, domin annobar ta yi muni ƙwarai.

  19. Gama Allah ya sa a zukatansu su cika nufinsa ta wurin yarda su ba wa dabbar ikonsu tă yi mulki, sai lokacin da kalmomin Allah sun cika.

  20. gama zunubanta sun yi tsororuwa sun kai sama. Allah kuma ya tuna da laifofinta.

  21. Saboda haka a rana ɗaya annobarta za su cim mata, mutuwa, makoki da kuma yunwa. Wuta zai cinye ta, gama Ubangiji Allah mai girma ne, wanda yake shari’anta ta.

  22. “Ki yi murna a kanta, ya sama! Ku yi murna, ku tsarkaka! Ku yi murna, ku manzanni da annabawa! Allah ya hukunta shi saboda abin da ya yi muku.”

  23. Bayan wannan sai na ji abin da ya yi kamar ƙasaitaccen taron mutane a sama, suna cewa, “Halleluya! Ceto da ɗaukaka da iko sun tabbata ga Allahnmu,

  24. Dattawan nan ashirin da huɗu da halittu huɗun nan masu rai suka fāɗi suka yi wa Allah sujada, wannan da yake zaune a kursiyi. Suka tā da murya suka ce, “Amin, Halleluya!”

  25. Sa’an nan wata murya ta fito daga kursiyin, tana cewa, “Ku yabi Allahnmu, dukanku da kuke bayinsa, ku da kuke tsoronsa, babba da yaro!”