Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Za ka cika da kunya a maimakon ɗaukaka. Yanzu lokacinka ne! Kai ma ka sha, a kuma tone asirinka! Gama kwaf na hannun daman Ubangiji yana zuwa kewaye da kai, abin kunya kuma zai rufe darajarka.

  2. Amma Ubangiji yana a cikin haikalinsa mai tsarki; bari dukan duniya tă yi shiru a gabansa.

  3. Ya Ubangiji, na ji irin shaharar da ka yi; na yi al’ajabi game da ayyukanka, ya Ubangiji. Ka maimaita su a kwanakinmu, ka sanar da su a lokacinmu; ka yi jinƙai ko a lokacin da kake fushi.

  4. Allah ya zo daga Teman, Mai Tsarkin nan daga Dutsen Faran. Sela Ɗaukakarsa ta rufe sammai yabonsa kuma ya cika duniya.

  5. Darajarsa ta yi kamar fitowar rana; ƙyalƙyali ya wulga daga hannunsa, inda ikonsa yake a ɓoye.

  6. Annoba ta sha gabansa; cuta kuma tana bin bayansa.

  7. Ya tsaya, ya kuwa girgiza duniya; ya duba, sai ya sa al’ummai suka yi rawan jiki. Tsofaffin duwatsu sun wargaje daɗaɗɗun tuddai kuma suka rurrushe. Hanyoyinsa dawwammamu ne.

  8. Ka ji haushin koguna ne, ya Ubangiji? Ko kuwa ka hasala da rafuffuka ne? Ko ka yi fushi da teku ne sa’ad da ka hau dawakanka da kuma kekunan yaƙinka masu nasara?

  9. Ka ja bakanka, ka nemi a ba ka kibiyoyi masu yawa. Sela Ka raba duniya da koguna;

  10. duwatsu sun gan ka sai suka ƙame. Ruwaye masu hauka sun yi ta fantsamawa; zurfafa suka yi ruri suka tā da raƙuman ruwansu sama.

  11. Rana da wata suka tsaya cik a sammai da ganin kibiyoyinka masu wucewa fyu, da ganin hasken māshinka mai walƙiya.

  12. Cikin hasala ka ratsa duniya cikin fushi kuma ka tattake ƙasashe.

  13. Ka fito don ka fanshi mutanenka, don ceci shafaffenka. Ka ragargaza shugaban ƙasar mugaye, ka tuɓe shi daga kai har ƙafa. Sela

  14. Ka tattake teku da dawakanka, kana kaɗa manyan ruwaye.

  15. duk da haka zan yi farin ciki da Ubangiji, zan yi murna da Allah Mai Cetona.

  16. Ubangiji Mai Iko Duka shi ne ƙarfina; yakan mai da ƙafafuna kamar na barewa, yakan sa in yi tafiya a wurare masu tsayi. Domin mai bi da kaɗe-kaɗe. A kan kayan kiɗi masu tsirkiyata.

  17. Maganar Ubangiji da ta zo wa Zefaniya ɗan Kushi, ɗan Gedaliya, ɗan Amariya, ɗan Hezekiya, a zamanin Yosiya ɗan Amon sarkin Yahuda.

  18. “Zan hallaka kome a fuskar duniya,” in ji Ubangiji.

  19. “Zan hallaka mutane da dabbobi; zan kuma hallaka tsuntsayen sama da kifayen teku, da gumakan da suke sa mugaye su yi tuntuɓe.” “Sa’ad da zan kawar da mutum daga fuskar duniya,” in ji Ubangiji.

  20. “Zan miƙa hannuna gāba da Yahuda da kuma dukan mazaunan Urushalima. Zan datse raguwar Ba’al daga wannan wuri, da sunayen firistocin gumaka da na marasa sanin Allah,

  21. waɗanda suka rusuna a kan rufin ɗaki don su yi sujada ga rundunar taurari. Waɗanda suka rusuna suka kuma yi rantsuwa da sunan Ubangiji suke kuma rantsuwa da sunan Molek.

  22. Waɗanda suka juya daga bin Ubangiji, ba sa kuma neman Ubangiji ko su nemi nufinsa.”

  23. Ku yi shiru a gaban Ubangiji Mai Iko Duka, gama ranar Ubangiji ta yi kusa. Ubangiji ya shirya hadaya; ya kuma tsarkake waɗanda ya gayyato.

  24. “A ranar hadayar Ubangiji zan hukunta sarakuna da kuma ’ya’yan sarakuna da duk waɗanda suke sanye da rigunan ƙasashen waje.

  25. A wannan rana zan hukunta dukan waɗanda suke kauce taka madogarar ƙofa, waɗanda suke cika haikalin allolinsu da rikici da ruɗu.