Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Ubangiji ya ɗauke hukuncinki, ya mai da abokan gābanki baya. Ubangiji, Sarkin Isra’ila, yana tare da ke; ba kuma za ki ƙara jin tsoron wani lahani ba.

  2. Ubangiji Allahnki yana tare da ke, mai iko ne don ceto. Zai yi matuƙar farin ciki da ke, zai rufe ki da ƙaunarsa, zai yi farin ciki da ke ta wurin rerawa.”

  3. “Zan cire taƙaici daga gare ki a ƙayyadaddun bukukkuwa; su kaya ne da kuma zargi a gare ki.

  4. A wannan lokaci zan jijji wa waɗanda suka danne ku; zan kuɓutar da guragu in kuma tattara waɗanda suke a warwatse. Zan sa a yabe su a kuma girmama su a kowace ƙasar da aka kunyatar da su.

  5. A wannan lokaci zan tattara ku; a wannan lokaci zan kawo ku gida, zan sa a yabe ku a kuma girmama ku a cikin dukan mutanen duniya a sa’ad da na maido da arzikinku a idanunku,” in ji Ubangiji.

  6. A shekara ta biyu ta mulkin Sarki Dariyus, a rana ta fari ga watan shida, maganar Ubangiji ta zo ta wurin annabi Haggai zuwa ga Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel, gwamnan Yahuda, da kuma Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist.

  7. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Waɗannan mutane sun ce, ‘Lokaci bai yi ba tukuna da za a gina gidan Ubangiji.’ ”

  8. Sa’an nan maganar Ubangiji ta zo ta wurin annabi Haggai cewa,

  9. To, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Ku lura da al’amuranku.

  10. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Ku lura da al’amuranku.

  11. Ku haura zuwa kan duwatsu ku sauko da katakai don ku gina gidan, don ni ma in ji daɗinsa, in kuma sami ɗaukaka,” in ji Ubangiji.

  12. “Ga shi, kukan sa rai za ku sami da yawa, amma sai ku ga kun sami kaɗan. Ɗan kaɗan ɗin ma da kukan kawo gida, nakan hura shi yă tafi. Me ya sa yake faruwa haka?” In ji Ubangiji Maɗaukaki. “Saboda gidana da yake zaman kango, yayinda kowannenku yana faman gina gidansa.

  13. Na kawo fări a ƙasar, da a kan duwatsu, da a kan hatsi, da a kan dukan abin da yake tsirowa daga ƙasa, da a kan mutane, da a kan dabbobi da kuma a kan wahalar hannuwanku.”

  14. Sa’an nan sai Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel, da Yoshuwa ɗan Yehozadak, wanda yake babban firist, da kuma dukan raguwar jama’ar suka yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnsu da kuma saƙon annabi Haggai, domin Ubangiji Allahnsu ne ya aiko shi. Mutane kuwa suka ji tsoron Ubangiji.

  15. Sai Haggai, ɗan saƙon Ubangiji, ya ba da wannan saƙo na Ubangiji ga mutane cewa, “Ina tare da ku” in ji Ubangiji.

  16. Saboda haka Ubangiji ya motsa zuciyar Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel, wanda yake gwamna a Yahuda, da kuma zuciyar Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da kuma zukatan dukan raguwar jama’ar. Suka zo suka fara aiki a gidan Ubangiji Maɗaukaki, Allahnsu,

  17. a ranar ashirin da ɗaya ga watan bakwai, maganar Ubangiji ta zo ta wurin annabi Haggai cewa,

  18. Amma yanzu ka ƙarfafa, ya Zerubbabel,’ in ji Ubangiji. ‘Ka ƙarfafa, ya Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist. Ku ƙarfafa, dukanku mutanen ƙasar,’ in ji Ubangiji, ‘ku yi aiki. Gama ina tare da ku,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.

  19. ‘Wannan shi ne alkawarin da na yi da ku a lokacin da kuka fito daga Masar. Ruhuna kuwa yana tare da ku. Kada ku ji tsoro.’

  20. “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ba da jimawa ba zan sāke girgiza sammai da kuma ƙasa, teku da busasshiyar ƙasa.

  21. Zan girgiza dukan al’ummai, marmarin kowace al’umma kuma zai taso, sa’an nan zan cika gidan nan da ɗaukaka,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.

  22. ‘Da zinariya da azurfa duka nawa ne,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.

  23. ‘Ɗaukakar gidan nan na yanzu za tă fi ɗaukakar gidan nan na dā,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki. ‘A wannan wuri kuma zan ba da salama,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.”

  24. A ranar ashirin da huɗu ga watan tara, a shekara ta biyu ta mulkin Dariyus, maganar Ubangiji ta zo wa annabi Haggai cewa,

  25. “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ku tambayi firist abin da doka ta ce.