God
Ayoyin da suka ambaci God
“Yanzu kuma me nake da shi a nan?” In ji Ubangiji. “Gama an kwashe mutanena ba a bakin kome ba kuma waɗanda suka mallake su sun yi musu ba’a, Kullum ana cin gaba da yin wa sunana saɓo.
Saboda haka mutanena za su san sunana; saboda haka a wannan rana za su san cewa ni ne wanda ya faɗa wannan. I, ni ne.”
Me ya fi wannan kyau a kan duwatsu a ga ƙafafu na masu kawo labari mai daɗi waɗanda suke shelar salama, waɗanda suke kawo labari mai daɗi, waɗanda suke shelar ceto, waɗanda suke ce wa Sihiyona, “Allahnki yana mulki!”
Ki kasa kunne! Masu tsaronki sun tā da muryoyinsu; tare sun yi sowa ta farin ciki. Sa’ad da Ubangiji ya komo Sihiyona, za su gan shi da idanunsu.
Ku ɓarke cikin waƙoƙin farin ciki gaba ɗaya, kangonki na Urushalima, gama Ubangiji ya ta’azantar da mutanensa, ya fanshi Urushalima.
Ubangiji zai nuna hannunsa mai tsarki a fili a idanun dukan al’ummai, da kuma dukan iyakokin duniya za su gani ceton Allahnmu.
Ku fita, ku fita daga can! Kada ku taɓa wani abu marar tsarki! Ku fita daga cikinta ku zama da tsarki, ku da kuke ɗaukan kayan aikin Ubangiji.
Amma ba za ku fita a gaggauce ba ko ku tafi da gudu; gama Ubangiji zai ja gabanku, Allah na Isra’ila zai kasance mai tsaron bayanku.
Duba, bawana zai aikata abubuwa da hikima; za a tā da shi a kuma ɗaga shi da ɗaukaka ƙwarai.
Kamar dai yadda aka kasance da mutane masu yawa waɗanda suka giggice sa’ad da suka gan shi, kamanninsa ya lalace ƙwarai fiye da na kowane mutum siffarsa kuma ta yi muni fiye da yadda ta mutum take,
Wa ya gaskata saƙonmu kuma ga wa hannun Ubangiji ya bayyana?
Ya yi girma kamar dashe marar ƙarfi, kamar saiwa kuma daga ƙeƙasasshiyar ƙasa. Ba shi da kyan gani ko wani makamin da zai ja hankalinmu, babu wani abin da yake da shi da zai sa mu yi sha’awarsa.
Tabbatacce ya ɗauki cututtukanmu ya kuma daure da baƙin cikinmu duk da haka muka ɗauka Allah ya hukunta shi ne, ya buge shi ya kuma sa ya sha azaba.
Dukanmu, muna kama da tumakin da suka ɓata, kowannenmu ya kama hanyarsa; Ubangiji kuwa ya sa hukunci ya auko a kansa hukuncin da ya wajaba a kanmu.
Da wulaƙanci da kuma hukunci aka ɗauke shi aka tafi. Wa kuwa zai yi maganar zuriyarsa? Gama an kawar da shi daga ƙasar masu rai; saboda laifin mutanena aka kashe shi.
Duk da haka nufin Ubangiji ne a ƙuje shi yă kuma sa yă sha wahala, kuma ko da yake Ubangiji ya sa ransa ya zama hadaya don zunubi, zai ga zuriyarsa zai kuma kawo masa tsawon rai, nufin Ubangiji kuma zai yi nasara a hannunsa.
Bayan wahalar ransa, zai ga hasken rai, ya kuma gamsu; ta wurin saninsa bawana mai adalci zai ’yantar da mutane masu yawa, zai kuma ɗauki laifofinsu.
Saboda haka zan ba shi rabo tare da manya, zai kuma raba ganima tare da masu ƙarfi, domin ya ba da ransa har mutuwa, aka kuma lissafta shi tare da masu laifofi. Gama ya ɗauki zunubin mutane masu yawa, ya kuma yi roƙo saboda laifofinsu.
“Ki rera, ya ke bakararriya, ke da ba ki taɓa haihuwa ba; ki ɓarke da waƙa, ki yi sowa don farin ciki, ke da ba ki taɓa naƙuda ba; domin ’ya’yan mace mai kaɗaici sun fi na mai miji yawa,” in ji Ubangiji.
Gama Mahaliccinki shi ne mijinki, Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa, Mai Tsarkin nan na Isra’ila ne Mai Fansarki; ana ce da shi Allahn dukan duniya.
Ubangiji zai kira sai ka ce ke mace ce da aka yashe ta tana kuma damuwa a ranta, macen da ta yi aure a ƙuruciya, sai kawai aka ƙi ta,” in ji Allahnki.
“Gama a ɗan ƙanƙanen lokaci na rabu da ke, amma da ƙauna mai zurfi zan sāke dawo da ke.
Cikin fushi mai zafi na ɓoye fuskata daga gare ki na ɗan lokaci, amma da madawwamin alheri zan ji tausayinki,” in ji Ubangiji Mai Fansarki.
“A gare ni wannan ya yi kamar kwanakin Nuhu, sa’ad da na rantse cewa ruwan Nuhu ba za su ƙara rufe duniya ba. Yanzu fa na rantse ba zan yi fushi da ke ba, ba zan ƙara tsawata miki kuma ba.
Ko da duwatsu za su girgiza a kuma tumɓuke tuddai, duk da haka madawwamiyar ƙaunata da nake yi miki ba za tă jijjigu ba ba kuwa za a kawar da alkawarin salamata ba,” in ji Ubangiji, wanda ya ji tausayinki.