God
Ayoyin da suka ambaci God
Ubangiji Mai Iko Duka ya ba ni harshen umarni, don in san maganar da za tă ƙarfafa gajiyayye. Ya farkar da ni da safe, ya farkar da kunnena don in saurara kamar wanda ake koya masa.
Ubangiji Mai Iko Duka ya buɗe kunnuwana, kuma ban yi tayarwa ba; ban ja da baya ba.
Gama Ubangiji Mai Iko Duka zai taimake ni, ba zan sha kunya ba. Saboda haka na kafa fuskata kamar dutsen ƙanƙara, na kuma sani ba zan sha kunya ba.
Ubangiji Mai Iko Duka ne zai taimake ni. Wane ne zai iya tabbatar da ni mai laifi? Duk za su koɗe kamar riga; asu za su cinye su.
Wane ne a cikinku yake tsoron Ubangiji yana kuma yin biyayya ga maganar bawansa? Bari wanda yake tafiya cikin duhu, wanda ba shi da haske, ya dogara a sunan Ubangiji ya kuma dogara ga Allahnsa.
“Ku kasa kunne gare ni, ku da kuna neman adalci kuke kuma neman Ubangiji. Dubi dutse daga inda aka yanke ku da kuma mahaƙar duwatsu inda aka fafe ku;
dubi Ibrahim, mahaifinku, da Saratu, wadda ta haife ku. Sa’ad da na kira shi kaɗai ne, na kuma albarkace shi na kuma mai da shi da yawa.
Tabbatacce Ubangiji zai ta’azantar da Sihiyona zai kuma duba da tausayi a kan dukan kufanta; zai sa hamadanta ta zama kamar Eden, ƙeƙasasshiyar ƙasarta kamar lambun Ubangiji. Za a sami farin ciki da murna a cikinta, godiya da ƙarar rerawa.
“Ku kasa kunne gare ni, mutanena; ku ji ni, al’ummata. Doka za tă fito daga gare ni; shari’ata za tă zama haske ga al’ummai.
Adalcina na zuwa da sauri, cetona yana a kan hanya, hannuna kuma zai kawo adalci ga al’ummai. Tsibirai za su dube ni su kuma jira da sa zuciya don hannuna.
Ku daga idanunku zuwa sammai ku dubi duniya a ƙasa; sammai za su ɓace kamar hayaƙi, duniya za tă shuɗe kamar riga mazaunanta kuma su mutu kamar ƙudaje. Amma cetona zai dawwama har abada, adalcina ba zai taɓa kāsa ba.
“Ku ji ni, ku da kuka san abin da yake daidai, ku mutanen da kuke da dokata a zukatanku. Kada ku ji tsoron ba’ar da mutane suke yi ko ku firgita saboda zargin da suke yi.
Gama asu za su cinye su kamar riga; tsutsotsi za su cinye su kamar ulu. Amma adalcina zai dawwama har abada, cetona har dukan zamanai.”
Ka tashi, ka tashi! Ka yafa wa kanka ƙarfi, Ya hannun Ubangiji; ka farka, kamar a kwanakin da suka wuce, kamar a zamanai na dā. Ba kai ba ne wanda ya yayyanka Rahab gunduwa-gunduwa, wanda ya soki dodon ruwan nan?
Waɗanda Ubangiji ya fansar za su dawo. Za su shiga Sihiyona da waƙoƙi; madawwamin farin ciki zai rufe kansu da rawani. Murna da farin ciki zai cika su, baƙin ciki da nishi zai ɓace.
“Ni kaɗai ne na ta’azantar da ku. Wane ne ku da kuke tsoron mutane masu mutuwa, ’ya’yan mutane waɗanda suke ciyawa ne kawai,
har da kuka manta da Ubangiji Mahaliccinku, wanda ya shimfiɗa sammai ya kuma kafa harsashen duniya, har kuna zama da tsoro kowace rana saboda fushin masu zalunci, waɗanda sun ƙudura sai sun hallaka? Gama ina fushin mai zalunci?
Gama ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya dama teku domin raƙumansa su yi ruri, Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa.
Na sa maganata a bakinka na kuma rufe ka da inuwar hannuna, Na shimfiɗa sammai, na kafa harsashen duniya, na kuma ce wa Sihiyona, ‘Ku mutanena ne.’ ”
Ki farka, ki farka! Ki tashi, ya Urushalima, ke da kika sha daga hannun Ubangiji kwaf na fushinsa, ke da kika shanye har ƙasar kwaf kwaf da ya sa mutane suna tangaɗi.
’Ya’yanki sun sume; sun kwanta kusurwar kowane titi, kamar barewar da aka kama da tarko. Sun cika da fushin Ubangiji da kuma tsawatawar Allahnki.
Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, Allahnki, wanda ya kāre mutanensa, “Duba, na ƙwace daga hannunki kwaf da ya sa ki tangaɗi; daga wannan kwaf, kwaf na fushina, ba za ki ƙara sha ba.
Zan sa shi a hannuwan masu gwada miki azaba, waɗanda suke ce miki, ‘Fāɗi rubda ciki don mu iya taka a kanki.’ Kika kuma mai da bayanki kamar ƙasa, kamar titin da ake takawa a kai.”
Gama ga abin Ubangiji yana cewa, “An sayar da ke ba da kuɗi ba, kuma ba da kuɗi za a fanshe ki ba.”
Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “Da farko mutanena suka gangara zuwa Masar don su zauna; a baya-bayan nan, Assuriya sun zalunce su.