Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. “Ya ke birni mai shan azaba, wadda hadari ya bulale ki ba a kuma ta’azantar da ke ba, zan gina ke da duwatsu turkuwoyis, zan kafa harsashenki da duwatsun saffaya.

  2. Zan gina hasumiyarki da jan yakutu, ƙofofinki kuma da duwatsu masu haske, dukan katangarki kuma da duwatsu masu daraja.

  3. Ubangiji zai koya wa dukan ’ya’yanki maza, da girma kuma salamar ’ya’yanki zai zama.

  4. In wani ya far miki, ba daga wurina ba ne; duk wanda ya far miki zai miƙa wuya gare ki.

  5. “Duba, ni ne wanda na halicci maƙeri wanda yake zuga garwashi ya zama harshen wuta ya kuma ƙera makamin da ya dace da aikinsa. Ni ne kuma na halicci mai hallakarwa ya yi ɓarna;

  6. ba makamin da aka ƙera don yă cuce ki da zai yi nasara, za ki kuma mayar da magana ga duk wanda ya zarge ki. Wannan ne gādon bayin Ubangiji, kuma wannan ita ce nasararsu daga gare ni,” in ji Ubangiji.

  7. Don me za ku kashe kuɗi a kan abin da ba abinci ba, ku kuma yi wahala a kan abin da ba za ku ƙoshi ba? Ku saurara, ku saurare ni, ku kuma ci abin da yake da kyau, ranku kuma zai ji daɗin abinci mafi kyau.

  8. Ku kasa kunne ku kuma zo gare ni; ku saurare ni, don ranku ya rayu. Zan yi madawwamin alkawari da ku, zan nuna muku ƙaunata marar ƙarewa da na yi wa Dawuda alkawari.

  9. Duba, na mai da shi shaida ga mutane, shugaba da kuma jagorar mutane.

  10. Tabbatacce za ku kira al’umman da ba ku sani ba, kuma al’umman da ba ku sani ba za su sheƙo a guje zuwa wurinku, saboda Ubangiji Allahnku, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, gama ya darjanta ku.”

  11. Ku nemi Ubangiji tun yana samuwa; ku yi kira gare shi tun yana kusa.

  12. Bari mugu ya bar irin halinsa mugu kuma ya sāke irin tunaninsa. Bari yă juyo ga Ubangiji, zai kuwa ji tausayinsa, ya juyo ga Allahnmu kuma, gama shi mai gafartawa ne a sauƙaƙe.

  13. “Gama tunanina ba tunaninku ba ne, yadda kuke yin abubuwa ba yadda nake yin abubuwa ba ne,” in ji Ubangiji.

  14. “Kamar yadda sammai suke can nesa da ƙasa, haka yadda nake yin abubuwa suke dabam da yadda kuke yin abubuwa tunanina kuma dabam da naku.

  15. haka maganata da take fitowa daga bakina. Ba za tă koma gare ni wofi ba, amma za tă cika abin da nake so ta kuma cika abin da na aike ta tă yi.

  16. A maimakon sarƙaƙƙiya, itacen fir ne zai tsiro, a maimakon ƙayayyuwa kuma, itacen ci-zaƙi ne zai tsiro. Wannan zai zama matuni na abin da Ni Ubangiji na yi, madawwamiyar alama ce, wadda ba za a datse ba.”

  17. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ku riƙe gaskiya ku yi abin da yake daidai, gama cetona yana kusa za a kuma bayyana adalcina nan da nan.

  18. Kada baƙon da ya miƙa kansa ga Ubangiji ya ce, “Ai Ubangiji zai ware ni daga mutanensa.” Kada kuma wani bābā ya yi gunaguni cewa, “Ni busasshen itace ne kawai.”

  19. Gama ga abin da Ubangiji ya faɗa, “Wa bābānnin da suna kiyaye Asabbatai, waɗanda suka zaɓi yin abin da ya gamshe ni suna kuma riƙe da alkawarina kankan,

  20. a gare su cikin haikalina da kuma bangayensa zan ba da matuni da kuma suna mafi kyau fiye da ’ya’ya maza da kuma ’ya’ya mata; zan ba su madawwamin sunan da ba za a raba su da shi ba.

  21. Baƙin da suka miƙa kansu ga Ubangiji don su bauta masa, su kuma ƙaunaci sunan Ubangiji, waɗanda kuma suke yin masa sujada, duk waɗanda suka kiyaye Asabbaci ba tare da ƙazantar da shi ba suka kuma riƙe alkawarina kankan,

  22. waɗannan ne zan kai tsattsarkan dutsena in sa su yi farin ciki a gidana na addu’a. Hadayunsu na ƙonawa da sadakokinsu za su zama abin karɓa a bagadena; gama za a ce da gidana gidan addu’a domin dukan al’ummai.”

  23. Ubangiji Mai Iko Duka ya furta cewa, zai tattara korarru na Isra’ila, “Zan ƙara tattaro waɗansu bayan waɗanda na riga na tattara.”

  24. Kowanne yakan ce, “Zo, bari in samo ruwan inabi! Bari mu cika cikinmu da barasa! Gobe ma zai zama kamar yau, ko ma fiye da haka.”

  25. Gumakan da suke cikin duwatsu masu sulɓi su ne rabonku; su ɗin, su ne rabonku. I, gare su kuka kwarara hadayu na sha kuka kuma miƙa hadayu na gari. Saboda waɗannan abubuwa, zan yi haƙuri?