God
Ayoyin da suka ambaci God
Har yaushe, ya Ubangiji za ka ɓoye? Za ka ɓoye har abada ne? Har yaushe fushinka zai yi ta ci kamar wuta?
Ka tuna yadda raina mai wucewa ne. Gama ka halicce dukan mutane ba amfani!
Ya Ubangiji, ina ƙaunar mai girma ta dā, wadda cikin amincinka ka rantse wa Dawuda?
Ka tuna, Ubangiji, yadda aka yi wa bawanka ba’a, yadda na jimre a zuciyata da zage-zagen dukan al’ummai,
zage-zagen da abokan gābanka suka yi mini, ya Ubangiji, da suka yi wa kowane matakin da shafaffenka ya ɗauka.
Yabo ya tabbata ga Ubangiji har abada!
Addu’ar Musa Mutumin Allah. Ubangiji kai ne mazauninmu cikin dukan zamanai.
Kafin a haifi duwatsu ko a fid da ƙasa da duniya, daga madawwami zuwa madawwami kai Allah ne.
Gama shekaru dubu a gabanka kamar kwana ɗaya ne da ya wuce, ko sa’a guda na dare.
An cinye mu ta wurin fushinka mun kuma razana ta wurin hasalarka.
Ka ajiye laifinmu a gabanka, asirin zunubanmu a hasken kasancewarka.
Dukan kwanakinmu sun wuce ƙarƙashin fushinka; mun gama shekarunmu da nishi.
Wa ya san ƙarfin fushinka? Gama hasalarka tana da girma kamar tsoron da ya dace da kai.
Ka ji mu, ya Ubangiji! Har yaushe zai ci gaba? Ka ji tausayin bayinka.
Ka ƙosar da mu da safe da ƙaunarka marar ƙarewa, don mu rera don yabo, mu kuma yi murna dukan kwanakinmu.
Faranta mana zuciya kamar yawan kwanakin da muka sha azaba, kamar yawan shekarun da muka ga wahala.
Bari a nuna ayyukanka ga bayinka, darajarka ga ’ya’yansu.
Bari alherin shugabanmu Allah yă kasance a kanmu; ka albarkaci mana aikin hannuwanmu, I, ka albarkaci aikin hannuwanmu.
Shi wanda yake zama a wurin Mafi Ɗaukaka zai huta a cikin inuwar Maɗaukaki.
Zan ce game da Ubangiji, “Shi ne mafakata da kagarata, Allahna, wanda nake dogara.”
Tabbatacce zai cece ka daga tarkon mai farauta da kuma daga cututtuka masu kisa.
Zai rufe ka da fikafikansa, a ƙarƙashin fikafikansa kuwa za ka sami mafaka; amincinsa zai zama maka garkuwa da katanga.
In ka mai da Mafi Ɗaukaka wurin zamanka, har ma Ubangiji wanda yake mafakata,
Gama zai umarci mala’ikunsa game da kai don su tsare ka a dukan hanyoyinka;
Ubangiji ya ce, “Domin ya ƙaunace ni, zan kuɓutar da shi; zan kiyaye shi, gama ya yarda da sunana.