Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. kana ba shi sauƙi a lokacin wahala, sai har an haƙa rami wa mugaye.

  2. Gama Ubangiji ba zai ƙi mutanensa ba; ba zai taɓa yashe gādonsa ba.

  3. Da ba don Ubangiji ya yi mini taimako ba, da tuni na zauna shiru a wurin mutuwa.

  4. Sa’ad da na ce, “Ƙafata na santsi,” ƙaunarka, ya Ubangiji, ta riƙe ni.

  5. Sa’ad da alhini ya yi yawa a cikina, ta’aziyyarka ta kawo farin ciki wa raina.

  6. Zai yiwu kursiyin da ya cika da lalaci yă haɗa kai da kai, wanda yake kawo azaba ta wurin abin da ya zartar?

  7. Amma Ubangiji ya zama kagarata, Allahna kuma dutsen da nake samun mafaka.

  8. Zai sāka musu saboda zunubansu yă kuma hallaka su saboda muguntarsu; Ubangiji Allahnmu zai hallaka su.

  9. Ku zo, bari mu rera don farin ciki ga Ubangiji; bari mu yi sowa da ƙarfi ga Dutsen cetonmu.

  10. Bari mu zo gabansa da godiya mu rera gare shi da kiɗi da waƙa.

  11. Gama Ubangiji Allah mai girma ne, babban Sarki a bisa dukan alloli.

  12. A hannunsa ne zurfafan duniya suke, ƙwanƙolin dutse kuma nasa ne.

  13. Teku nasa ne, gama shi ne ya yi shi, da hannuwansa kuma ya yi busasshiyar ƙasa.

  14. Ku zo, bari mu rusuna mu yi sujada, bari mu durƙusa a gaban Ubangiji Mahaliccinmu;

  15. gama shi ne Allahnmu mu mutanen makiyayansa ne, garke kuwa a ƙarƙashin kulawarsa. Yau, in kuka ji muryarsa,

  16. inda kakanninku suka gwada suka kuma jarraba ni, ko da yake sun ga abin da na yi.

  17. Shekara arba’in na yi fushi da wancan tsara; na ce, ‘Su mutane ne waɗanda zukatansu suka kauce, kuma ba su san hanyoyina ba.’

  18. Saboda haka na yi rantsuwa cikin fushina, ‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’ ”

  19. Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji; ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka.

  20. Ku rera ga Ubangiji, ku yabe sunansa; ku yi shelar cetonsa kowace rana.

  21. Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai, manyan ayyukansa a cikin dukan mutane.

  22. Gama da girma Ubangiji yake, ya kuma cancanci yabo; tilas a ji tsoronsa fiye da dukan alloli.

  23. Gama dukan allolin al’ummai gumaka ne, amma Ubangiji ne ya yi sammai.

  24. Daraja da ɗaukaka suna a gabansa; ƙarfi da ɗaukaka suna a cikin tsarkakar wurinsa.

  25. Ku ba wa Ubangiji, ya iyalan al’ummai ku ba wa Ubangiji ɗaukaka da kuma ƙarfi.