God
Ayoyin da suka ambaci God
Zai kira bisa sunana, zan kuma amsa masa; zan kasance tare da shi a lokacin wahala, zan kuɓutar da shi in kuma girmama shi.
Da tsawon rai zan ƙosar da shi in kuma nuna masa cetona.”
Zabura ce. Waƙa ce. Domin ranar Asabbaci. Yana da kyau a yabi Ubangiji a kuma yi kiɗi ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka,
don a yi shelar ƙaunarka da safe amincinka kuma da dare,
Gama ka sa na yi murna ta wurin ayyukanka, ya Ubangiji; na rera don farin ciki saboda ayyukan hannuwanka.
Ina misalin ayyukanka, ya Ubangiji, tunaninka da zurfi suke ƙwarai!
Amma kai, ya Ubangiji, za a ɗaukaka har abada.
Gama tabbatacce abokan gābanka, ya Ubangiji, tabbatacce abokan gābanka za su hallaka; za a watsar da dukan masu aikata mugunta.
Ka ɗaukaka ƙahona kamar na ɓauna; an zubo mai masu kyau a kaina.
da aka daddasa a gidan Ubangiji, za su haɓaka a filayen gidan Allahnmu.
suna shela cewa, “Ubangiji adali ne; shi ne Dutsena, kuma babu mugunta a cikinsa.”
Ubangiji yana mulki, yana sanye da ɗaukaka; Ubangiji yana sanye da ɗaukaka yana kuma sanye da ƙarfi. An kafa duniya daram; ba za a iya matsar da ita ba.
An kafa kursiyin tun da daɗewa; kana nan tun fil azal.
Tekuna sun taso, ya Ubangiji, tekuna sun ta da muryarsu; tekuna sun tā da ta raƙumansu masu tumbatsa.
Mafi ƙarfi fiye da tsawan manyan ruwaye, mafi ƙarfi fiye da ikon raƙuman ruwan teku, Ubangiji mai zama a bisa mai girma ne.
Ƙa’idodinka suna nan daram; tsarki ya yi wa gidanka ado har kwanaki marar ƙarewa, ya Ubangiji.
Ya Ubangiji, Allahn da yake ramuwa, Ya Allah wanda yake ramuwa, ka haskaka.
Ka tashi, ya Alƙalin duniya; ka sāka wa masu girman kai abin da ya dace da su.
Har yaushe mugaye, ya Ubangiji har yaushe mugaye za su yi ta murna?
Suna murƙushe mutanenka, ya Ubangiji; suna danne gādonka.
Suna ce, “Ubangiji ba ya gani; Allah na Yaƙub bai kula ba.”
Shi da ya sa kunne ba don a ji ba ne? Shi da ya yi ido ba don yă gani ba ne?
Shi da yake yi wa al’ummai horo ba ya hukunci ne? Shi da yake koya wa mutum ba shi da sani ne?
Ubangiji ya san tunanin mutum; ya san cewa tunaninsu banza ne.
Mai albarka ne mutumin da ka yi masa horo, ya Ubangiji, mutumin da ka koyar daga dokarka;