Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Ka ɗauke abokaina na kurkusa daga gare ni ka sa na zama abin ƙyama a gare su. An kange ni, ba yadda zan kuɓuta

  2. idanuna ba sa gani sosai saboda baƙin ciki. Ina kira gare ka, ya Ubangiji, kowace rana; na tā da hannuwana zuwa gare ka.

  3. Kakan nuna wa matattu ayyukanka na banmamaki ne? Waɗanda suka mutu sukan tashi su yabe ka ne? Sela

  4. Ana furta ƙaunar a cikin kabari ne, ana zancen amincinka a cikin Hallaka ne?

  5. An san ayyukanka masu banmamaki a wurin duhu ne, ko ayyukan adalcinka a lahira?

  6. Amma ina kuka gare ka neman taimako, ya Ubangiji; da safe addu’ata kan zo gabanka.

  7. Don me, ya Ubangiji, ka ƙi ni ka kuma ɓoye fuskarka daga gare ni?

  8. Tun ina ƙarami na sha wahala na kuma yi kusa in mutu; na sha wahalar razanarka kuma na kuma fid da zuciya.

  9. Hasalarka ta sha kaina; razanarka ta hallaka ni.

  10. Ka ɗauke abokaina da ƙaunatattuna daga gare ni; duhu ne abokina na kurkusa.

  11. Maskil na Etan dangin Ezra. Zan rera game da ƙauna mai girma ta Ubangiji har abada; da bakina zan sanar da amincinka a dukan zamanai.

  12. Zan furta cewa ƙaunarka tana nan daram har abada, cewa ka kafa amincinka a sama kanta.

  13. Ka ce, “Na yi alkawari da zaɓaɓɓena, na rantse wa Dawuda bawana,

  14. cewa ‘Zan kafa zuriyarka har abada in kuma sa kursiyinka yă tsaya daram dukan zamanai.’ ” Sela

  15. Sammai na yabon abubuwan banmamakinka, ya Ubangiji, amincinka shi ma, a cikin taron tsarkakanka.

  16. Gama wane ne a sarari za a iya kwatanta da Ubangiji? Wane ne yake kamar Ubangiji a cikin talikan samaniya?

  17. Cikin taron tsarkaka Allah ne aka fi tsoro; shi ne mafi bantsoro fiye da dukan waɗanda suka kewaye shi.

  18. Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, wane ne kamar ka? Kai mai iko ne, ya Ubangiji, kuma amincinka ya kewaye ka.

  19. Kana mulkin teku mai tumbatsa; sa’ad da raƙuma sun tashi, kakan kwantar da su.

  20. Ka ragargaza Rahab kamar waɗanda aka kashe; da hannunka mai ƙarfi ka watsar da abokan gābanka.

  21. Sammai naka ne, haka kuma duniya; ka kafa duniya da dukan abin da yake cikinta.

  22. Ka halicce arewa da kudu; Tabor da Hermon suna rera don farin ciki ga sunanka.

  23. Hannunka mai iko ne; hannunka yana da ƙarfi, hannunka na dama ya sami ɗaukaka.

  24. Adalci da gaskiya su ne tushen kursiyinka; ƙauna da aminci suna tafiya a gabanka.

  25. Masu albarka ne waɗanda suka koyi yin maka kirari waɗanda suke tafiya cikin hasken da yake gabanka, Ubangiji.