Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Sa’an nan Ruhun Ubangiji ya sauko wa Yefta. Sai ya haye Gileyad da Manasse, ya ratsa ta Mizfa zuwa Gileyad, daga can kuma ya kai wa Ammonawa hari.

  2. Yefta kuwa ya yi wa’adi da Ubangiji ya ce, “In ka ba da Ammonawa a hannuwana,

  3. duk abin da ya fara fitowa daga ƙofar gidana don yă tarye ni, sa’ad da na komo daga yaƙi da Ammonawa, zai zama na Ubangiji, zan miƙa shi hadaya ta ƙonawa.”

  4. Sa’an nan Yefta ya haye zuwa wajen Ammonawa don yaƙi da su. Ubangiji kuwa ya ba da su a hannuwansa.

  5. Da ya gan ta, sai ya yayyage tufafinsa ya yi kuka ya ce, “Kaito! ’Yata! Kin karya mini gwiwa, kuma na lalace, domin na yi wa’adi ga Ubangiji da ba zan iya in karya ba.”

  6. Ta ce, “Mahaifina, idan ka riga ka yi wa Ubangiji magana, sai ka yi da ni yadda ka yi alkawari, da yake Ubangiji ya ɗau maka fansa a kan Ammonawa.”

  7. Da na ga ba za ku taimake ni ba, sai na yi kasai da raina na kuwa haye don in yaƙi Ammonawa, Ubangiji kuwa ya ba ni nasara a kansu. To, don me kuka zo yau don ku yaƙe ni?”

  8. Isra’ilawa suka sāke yin mugayen ayyuka a gaban Ubangiji, saboda haka ya ba da su a hannun Filistiyawa shekara arba’in.

  9. Mala’ikan Ubangiji ya bayyana gare ta ya ce, “Ga shi ke bakararriya ce ba kya haihuwa, amma za ki yi ciki ki kuma haifi ɗa.

  10. gama za ki yi ciki, ki haifi ɗa. Aska ba za tă taɓa kansa ba, domin yaron zai zama Banazare, keɓaɓɓe ga Allah tun daga haihuwa, shi ne kuwa zai soma ceton Isra’ilawa daga hannuwan Filistiyawa.”

  11. Sa’an nan matar ta tafi wajen mijinta ta faɗa masa cewa, “Wani mutumin Allah ya zo wurina. Ya yi kama da mala’ikan Allah, yana da bantsoro ƙwarai. Ban tambaye shi inda ya fito ba, kuma bai gaya mini sunansa ba.

  12. Sai dai ya ce mini, ‘Za ki yi ciki, ki kuma haifi ɗa. To, fa, kada ki sha ruwan inabi ko abu mai sa maye kada kuma ki ci abin da yake marar tsarki, gama ɗan zai zama Banazare na Allah tun daga haihuwa har ranar mutuwarsa.’ ”

  13. Sai Manowa ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji, ina roƙonka, bari mutumin Allahn da ka aiko mana yă sāke zuwa don yă koya mana yadda za mu goyi yaron da za a haifa.”

  14. Allah ya ji Manowa, sai mala’ikan Allah ya sāke zuwa wurin matar yayinda take gona; amma Manowa mijinta ba ya tare da ita.

  15. Mala’ikan Ubangiji ya ce, “Dole matarka ta kiyaye duk abin da na riga na gaya mata.

  16. Manowa ya ce wa mala’ikan Ubangiji, “Muna roƙonka ka jira mu yanka maka ɗan akuya.”

  17. Mala’ikan Ubangiji ya ce, “Ko kun sa na tsaya, ba zan ci abincinku ba. Amma in kun shirya hadaya ta ƙonawa, ku miƙa wa Ubangiji.” (Manowa bai gane cewa mala’ikan Ubangiji ne ba.)

  18. Sa’an nan Manowa ya sāke tambayi mala’ikan Ubangiji ya ce, “Mene ne sunanka, don mu girmama ka sa’ad da maganarka ta tabbata.”

  19. Ya ce, “Me ya sa kake tambaya sunana? Ai, ya wuce fahimta.”

  20. Sa’an nan Manowa ya ɗauki ɗan akuya, tare da hadaya ta hatsi ya miƙa wa Ubangiji a kan dutse. Ubangiji kuwa ya yi abin mamaki yayinda Manowa da matarsa suke kallo.

  21. Yayinda harshen wuta ya yi sama daga bagaden, sai mala’ikan Ubangiji ya haura cikin harshen wutar. Da ganin wannan Manowa da matarsa suka fāɗi da fuskokinsu har ƙasa.

  22. Da mala’ikan Ubangiji bai ƙara bayyana kansa ga Manowa da matarsa ba, sai Manowa ya gane cewa mala’ikan Ubangiji ne.

  23. Ya ce wa matar, “Ba shakka za mu mutu, gama mun ga Allah!”

  24. Amma matar ta ce, “Da Ubangiji yana nufin kashe mu ne, da ba zai karɓi hadaya ta ƙonawa da hadaya ta hatsi daga hannunmu, ko yă nuna mana dukan waɗannan abubuwa ko abin da ya gaya mana ba.”

  25. Matar kuwa ta haifi ɗa, aka sa masa suna Samson. Ya yi girma Ubangiji kuma ya albarkace shi,