Tsallake zuwa abun ciki

Esau

159 ayoyi · 11 'yan gida

An kuma san shi da: Edom

Ayoyin da suka ambaci Esau

Tace bisa littafi
  1. Suka tashi daga Kadesh, suka yi sansani a Dutsen Hor, a iyakar Edom.

  2. “ ‘Gefenku na kudu zai haɗa da wani sashin Hamadan Zin ta iyakar Edom. A gabas, iyakarku ta kudu za tă fara daga ƙarshen Tekun Gishiri,

  3. Ka ba wa mutane waɗannan umarnai, ka ce, ‘Kuna gab da wucewa cikin yankin ’yan’uwanku, zuriyar Isuwa, wanda yake zama a Seyir. Za su ji tsoronku, amma ku yi hankali

  4. kada ku tsokane su da yaƙi, gama ba zan ba ku wata ƙasa daga cikinsu ba, ba ma wadda za tă iya isa ku sa ƙafarku a kai. Na ba wa Isuwa ƙasar tudu ta Seyir, ta zama tasa.

  5. Saboda haka muka ci gaba, muka wuce ’yan’uwanmu, zuriyar Isuwa, wanda yake zama a Seyir. Muka bar hanyar Araba, wadda ta haura daga Elat da Eziyon Geber, muka nufi wajen hamadar Mowab.

  6. Haka ma Horiyawa, a dā sun zauna a Seyir, amma zuriya Isuwa suka kore su. Suka hallaka Horiyawa da suke kafinsu, suka kuma zauna a wurinsu, kamar dai yadda Isra’ila ta yi a ƙasar da Ubangiji ya ba su a matsayin mallaka.)

  7. Ubangiji ya yi daidai yadda ya yi wa zuriyar Isuwa waɗanda suka zauna a ƙasar Seyir, sa’ad da ya hallaka Horiyawa a gabansu. Su kuma suka kore su, suka zauna a wurinsu. Har wa yau, zuriyar Isuwa ne suke zama a can.

  8. kamar yadda zuriyar Isuwa, waɗanda suke zaune a Seyir, da Mowabawa, waɗanda suke zaune a Ar, suka yardar mana, gama muna so mu ƙetare Urdun zuwa ƙasa wadda Ubangiji, Allahnmu yake ba mu.”

  9. An raba wa kabilar Yahuda gādonsu ta wurin yin ƙuri’a, bisa ga iyalansu, rabon ya kai har zuwa sashen Edom, zuwa Jejin Zin can kurewar kudu.

  10. Garuruwan kabilar Yahuda da suke kudu cikin Negeb zuwa iyakar Edom su ne. Kabzeyel, Eder, Yagur,

  11. ga Ishaku kuwa na ba shi Yaƙub da Isuwa. Na ba Isuwa ƙasar kan tudu ta Seyir, amma Yaƙub da ’ya’yansa maza suka gangara zuwa Masar.

  12. “Ya Ubangiji, sa’ad da ka bar Seyir, sa’ad da ka yi tafiya daga ƙasar Edom, ƙasa ta girgiza, sammai suka zubo, gizagizai sun zubo da ruwa.

  13. Sa’an nan Isra’ila ta aiki jakadu zuwa ga sarkin Edom cewa, ‘Ka ba mu izini mu ratsa ƙasarka,’ amma sarkin Edom bai saurara ba. Suka kuma aika wa sarkin Mowab, shi ma ya ƙi. Saboda haka Isra’ila ta zauna a Kadesh.

  14. “Daga can suka ci gaba ta hamada, suka zaga ƙasashen Edom da Mowab, suka wuce ta gabashin ƙasar Mowab, sa’an nan suka yi sansani a ɗaya gefen Arnon. Ba su shiga yankin Mowab ba, gama Arnon ce iyakarta.

  15. Bayan Shawulu ya hau karagar mulkin Isra’ila, ya yi yaƙi da abokan gābansu ta kowane gefe. Mowabawa, Ammonawa, mutanen Edom, sarakunan Zoba, da kuma Filistiyawa. Duk wurin da ya juya, ya hore su.

  16. Ya ajiye rundunar sojoji ko’ina a Edom, dukan mutanen Edom kuwa suka zama bayin Dawuda. Ubangiji ya ba wa Dawuda nasara a duk inda ya tafi.

  17. Sarki Solomon ya kuma gina jiragen ruwa a Eziyon Geber, wadda take kusa da Elot a Edom, a bakin Jan Teku.

  18. Sai Ubangiji ya tayar wa Solomon wani abokin gāba, mai suna Hadad, mutumin Edom daga gidan sarautar Edom.

  19. A shekarun baya Dawuda ya ci Edom da yaƙi. Yowab, shugaban sojojinsa ya tafi can domin yă binne Isra’ilawa waɗanda suka mutu a yaƙi. Sa’ad da suke a can, sojojin Isra’ila suka kashe kowane ɗa namiji a Edom.

  20. Yowab da dukan Isra’ilawa suka zauna a can, wata shida, sai da suka hallaka dukan mutane a Edom.

  21. Babu sarki a lokacin Edom, saboda haka sai mataimaki ya yi mulki.

  22. Ya ƙara da cewa, “Wace hanya za mu bi?” Sai Yoram ya amsa ya ce, “Ta hanyar jejin Edom.”

  23. Saboda haka sarkin Isra’ila ya fita tare da sarkin Yahuda, da kuma sarkin Edom. Da suka yi kwana bakwai suna ta zagawa, sai sojoji da dabbobi suka rasa ruwan sha.

  24. Yehoshafat ya ce, “Maganar Ubangiji tana tare da shi.” Saboda haka sarkin Isra’ila da Yehoshafat da kuma sarkin Edom suka tafi wurin Elisha.

  25. Kashegari, daidai lokacin hadaya, sai ga ruwa yana gangarowa daga gefen Edom! Ƙasar kuwa ta cika da ruwa.