Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Tower

38 ayoyi · 16 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. To, a lokacin, yaren mutanen duniya ɗaya ne, maganarsu kuma ɗaya ce.

  2. Yayinda mutane suke ta yin ƙaura zuwa gabas, sai suka sami fili a Shinar, suka zauna a can.

  3. Suka ce wa juna, “Ku zo, mu yi tubula, mu gasa su sosai.” Suka yi amfani da tubula a maimakon duwatsu, kwalta kuma a maimakon laka.

  4. Sa’an nan suka ce, “Ku zo, mu gina wa kanmu birni da hasumiyar da za tă kai har sammai, domin mu yi wa kanmu suna, don kada mu warwatsu ko’ina a doron ƙasa.”

  5. Sai Ubangiji ya sauko don yă ga birni da kuma hasumiyar da mutanen suke gini.

  6. Ubangiji ya ce, “Ga su, su jama’a ɗaya ce, su duka kuwa harshensu guda ne. Wannan kuwa masomi ne kawai na abin da za su iya yi, babu kuma abin da suka yi shirya yi da ba za su iya yi ba.

  7. Zo, mu sauka, mu rikitar da harshensu don kada su fahimci juna.”

  8. Saboda haka Ubangiji ya watsar da su daga wurin zuwa ko’ina a doron ƙasa, suka kuwa daina gina birnin.

  9. Shi ya sa aka kira birnin Babel, domin a can ne Ubangiji ya rikitar da harshen dukan duniya. Daga can Ubangiji ya watsar da su ko’ina a doron ƙasa.

  10. Isra’ila ya yi gaba, ya kafa tentinsa gaba da Migdal Eder.

  11. Daga nan ya wuce zuwa Fenuwel ya yi irin roƙon nan, amma suka amsa yadda mutanen Sukkot suka yi.

  12. Saboda haka sai ya ce wa mutanen Fenuwel, “Sa’ad da na dawo da nasara zan rushe wannan hasumiya.”

  13. Ya rushe hasumiyar Fenuwel ya kuma karkashe mutanen garin.

  14. Da jin haka, sai ’yan ƙasa a hasumiyar Shekem suka shiga wurin mafaka a hankalin El-Berit.

  15. Saboda haka mutanen suka sassare rassan itatuwa suka bi Abimelek. Suka tattara su a jikin mafakar suka kuma cinna mata wuta a kan mutanen da suke a ciki. Ta haka dukan mutanen da suke cikin hasumiyar Shekem, wajen maza da mata dubu ɗaya suka mutu.

  16. Allahna shi ne dutsena. A gare shi nake samun kāriya shi ne garkuwata da kuma ƙahon cetona. Shi ne mafakata, maɓuyata, da mai cetona. Daga mutane masu fitina, ka cece ni.

  17. “Ya ba wa sarkinsa kyakkyawan nasara; ya nuna madawwamiyar ƙauna ga shafaffensa, ga Dawuda da zuriyarsa har abada.”

  18. Mai tsaro kuwa yana tsaye a kan hasumiya a Yezireyel, sai ya hangi rundunar Yehu sa’ad da yake zuwa. Ya ce, “Na ga wata runduna.” Sai Yoram ya umarta, “Nemi mahayin doki a aike shi yă tarye su, yă kuma tambaye su, ‘Lafiya?’ ”

  19. Daga hasumiya zuwa birni mai katanga, ya ci Filistiyawa da yaƙi, har zuwa Gaza da kewaye.

  20. Ya ce wa Yahuda, “Bari mu gina waɗannan garuruwa mu sa katanga kewaye da su, da hasumiyoyi, ƙofofi da ƙyamare. Ƙasar har yanzu tamu ce domin mun nemi Ubangiji Allahnmu, mun neme shi ya kuwa ba mu hutu a kowane gefe.” Saboda haka suka gina suka kuma yi nasara.

  21. Uzziya ya gina hasumiyoyi a Urushalima a Ƙofar Kusurwa, a Ƙofar Kwari da kuma a kusurwar katanga, ya kuma yi musu katanga.

  22. Ya gina hasumiyoyi a hamada ya kuma haƙa rijiyoyi masu yawa, gama yana da dabbobi masu yawa a gindin duwatsu da kuma a kwari. Yana da mutane masu yin masa aiki a gonakinsa da gonakin inabinsa a tuddai da kuma a ƙasashe masu dausayi, gama yana son noma.

  23. Sai suka yi aiki tuƙuru suna gyaran dukan sassan katangar da suka fāɗi, suna kuma gina hasumiya a kai. Ya gina wata katanga a waje da wannan, ya kuma ƙara ƙarfin madogaran gini na Birnin Dawuda. Ya yi makamai masu yawa da kuma garkuwoyi.

  24. Eliyashib babban firist da ’yan’uwansa firistoci suka tashi suka sāke gina Ƙofar Tumaki. Suka tsarkake ta, suka sa ƙofofinta a wurarensu, suka yi ginin har Hasumiyar Ɗari, wadda suka tsarkake, da kuma Hasumiyar Hananel.

  25. Ƙungiyar mawaƙa ta biyu suka yi jerin gwano a ɗaya gefen. Na bi su a bisan katangar, tare da rabin mutanen, muka wuce Hasumiya Tanderu zuwa Katanga Mai Faɗi,