Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Tower: In the walls of Jerusalem

4 ayoyi · 16 fannoni

Ayoyi game da In the walls of Jerusalem

  1. Uzziya ya gina hasumiyoyi a Urushalima a Ƙofar Kusurwa, a Ƙofar Kwari da kuma a kusurwar katanga, ya kuma yi musu katanga.

  2. Sai suka yi aiki tuƙuru suna gyaran dukan sassan katangar da suka fāɗi, suna kuma gina hasumiya a kai. Ya gina wata katanga a waje da wannan, ya kuma ƙara ƙarfin madogaran gini na Birnin Dawuda. Ya yi makamai masu yawa da kuma garkuwoyi.

  3. Ƙungiyar mawaƙa ta biyu suka yi jerin gwano a ɗaya gefen. Na bi su a bisan katangar, tare da rabin mutanen, muka wuce Hasumiya Tanderu zuwa Katanga Mai Faɗi,

  4. bisa Ƙofar Efraim, Ƙofar Yeshana, Ƙofar Kifi, Hasumiyar Hananel da kuma Hasumiya ɗari, har zuwa Ƙofar Tumaki. A Ƙofar Matsara suka tsaya.