Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Power of God: Efficiency of ministers is through

5 ayoyi · 51 fannoni

Ayoyi game da Efficiency of ministers is through

  1. Ni na shuka iri, Afollos kuma ya yi banruwa, amma Allah ne ya sa irin ya yi girma.

  2. Don haka, da wanda ya yi shuki, da wanda ya yi banruwa, ba a bakin kome suke ba, sai dai Allah kaɗai, mai sa abubuwa su yi girma.

  3. Mutumin da ya yi shuki, da mutumin da ya yi banruwa nufinsu ɗaya ne, kuma kowannensu zai sami lada gwargwadon aikinsa.

  4. Gama Allah wanda ya yi aiki a cikin hidimar Bitrus a matsayin manzo ga Yahudawa, haka ma ya yi aiki a cikin hidimata a matsayin manzo ga Al’ummai.

  5. Na zama bawan wannan bishara ta wurin baiwar alherin Allah da aka yi mini ta wurin ikonsa da yake aiki a cikina.